*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
_{Babban jarabawa agareta..}_
*NA*_Hafsat Hafnan_
*DA*
_Zainab Chubad'o_*Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fuzgar zuciya❤*
*02*
Haka Sumaiyya ta koma gida tunani da damuwa fal ranta, sai take ji kamar ta kashe kanta, da sauri ta k'wabi kanta da wannan banzar tunanin data tuna makomar duk wanda ya kashe kansa to fa kai tsaye wuta zashi, addu'a ta dunga yi da kuma karatun alqur'ani kan Allah ya kawo mata mafita kafin takwas d'in daren da suka ajje.idar da sallar magrib d'inta kenan, ta dan sake tab'a karatun Qur'ani sama sama sannan tayi add'ua ta shafa, kana ta mik'e tana ninke sallaya ayayin da take tunanin irin karyar da zata shararawa su Yaya Basira har asamu su batta ta Fita adaren nan.Bayan ta gama yanke shawara da zuciyar ta, Kai tsaye ta nufi dakinta, ta sameta tana sallah, danta Adil kuma ya bingire da bacci agefenta, Zama tayi har sai data jira ta sallame sannan ta juyo gareta tace"ya akayi ne k'anwata na ganki wata sum sum dake ? Ko akwai wani damuwar ne ?"
Shiru babu amsa da alamun tayi nisa cikin tunani, hannu Yaya Basira tasa ta tab'o ta"ke! Sumaiyya." Firgigit! Ta dawo hayyacinta hadda sa hannu tana dafe k'irji, sai sauke numfarfashi take tace"Kai Yaya har kin ban tsoro wallahi."Tace"wai ni meke damunki ne ? acikin 'yan kwanakin nan nasa miki ido sosai na lura kwata kwata baki da walwala, kamar akwai abunda ke damunki amma zurfin cikin tsiya ya hana ki bud'e mun cikinki, ey Sumaiyya ? baki son ki gayamun damuwarki sabida ba ciki d'aya muka fito bako ?" Da sauri Sumaiyya ta matso kusa da ita tana girgiza kai alokaci daya kuma wasu hawaye masu radad'i na shirin kwaranyo mata, ta kamo yatsun Yaya Basira tace cikin raunin murya"haba yayata meyasa kike fadin irin wannan maganar da ko kadan batta da dad'in ji ? Ni ko kadan bana mana kallon 'yan uba, ji nake tamk'ar uwa daya ce ta haifemu, dan haka na hadaki da girman Allah karki sake irin wannan tunanin, kuma zancen damuwa babu abunda ke damuna kawai kewar su Baba nake tunda na dad'e ban je gida ba."
Ajiyar Zuciya Yaya ta sauke tace"Kai Sumaiyya 'yar Baba, gashi Baba ya nace sai kinyi karatu tunda mu mun ki maida hankali muyi, to don Allah Sumaiyya yadda tsohon nan yake fad'i tashi akanki dan ganin kin cimma burinki arayuwa, ki dubi girman Allah da soyayyar dake tsakaninsa da fiyayyen halitta karki bashi kunya, ki bari ki gama makarantar nan lafiya ba tare da an samu wata matsala ba, sannan duk inda zaki shiga kuma ki fita ki cigaba da tsare mana _*MUTUNCIN KANKI*_ ,Sosai mutuncinki yake da matuk'ar daraja agareki damu kanmu danginki, Sumaiyya ko baki san da cewa bayan mahaifinmu kece haske ga danginmu ba ? dalili kuwa shine kasancewar acikinmu duka kece kika dakko halayen Baba Sheikh saf! Komai baki baro ba hatta da kamanninsa da komai ma, shiyasa idan kika lura yafi kaunarki akanmu, hakan ne ya jawo sauran ke tsananin kishi dake, ki sani zub'ewar mutuncinki yana nufin zub'ewar mutuncin gidanmu ne, dan haka ki rikeshi dak'yau kar kiyi sakaci, ki bari mu aurar dakai cikin mutunci kamar yadda aka aurar da sauran matan Zuri'a.." kuka yaci mugun karfin yaya Basira, ita kanta Sumaiyyar kukan take sosai tamk'ar zata had'iyi zuciya ta mutu, musamman ma da taga Yayar tata na mata tuni ne tamk'ar wacce tasan abunda take shirin aikatawa adaren yau...."Sumaiyya kina da tarin masoya da mak'iya masu nufinki da sharri sosai, akwai masu son shiga tsakaninki da mahaifinki domin wargaza kyakkyawar alakar dake tsakaninku amma fa ki sani sai in kece kika bada damar faruwar hakan, Shiyasa nake sake zaburar dake da ki dunga k'ok'arin gayamun damuwar ki ,ni kuma na miki alk'awarin baki shawarwari na gari.."
Cikin sarkewar murya tace"inshaa Allahu Yaya bazaku tab'a kuka dani ba, kuma ina mai rokonki alfarma da ki cigaba da tayani da addua domin ina jin zuciyata na neman gazawa akaron farko arayuwata wajen biyewa sharrin shaidan, yaya ki taimakeni da du'a'i Allah yasa in cinye jarabawar da Allah ya safko mun domin kuwa hak'ik'a na fara fuskantar jarabobin da Allah ya rubuto mun na rayuwa..." Cike da tsoro Yaya Basira tace"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! ina fatar wannan jarabawar bai tab'o mutuncinki ba dai ko ?" Cikin tsoro da fargaba, da kuma dauriya tace"ko kadan!..." Yaya ta saukar da ajiyar zuciya tace"Alhamdulillah! domin mutuncinki shine babban damuwa, to Allah ya yaye miki duk wani abunda ke damunki, kuma Allah yasa ki cinye duka jarabobinki duniya da lahira."
YOU ARE READING
MUTUNCIN 'YA MACE
Action"Sumaiyya ki sani wallahi sai an buga sabon kafce! Koda ni Muntasir zanyi yawo tsirara acikin duniyan nan ne saina tabbata na lalata miki rayuwa ta yadda nan gaba bazaki moru ba ko agidan aurenki!." Muntasir na tsaneka!na tsani duk wanda ya sanka! n...