14

31 0 0
                                    

*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
           _{Babban jarabawa agareta..}_

     
            *NA*

   _Hafsat Hafnan_

                *DA*
   
        _Zainab Chubad'o_

*Labarin daya ƙunshi Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fuzgar zuciya❤*

     

        *14*

_____✍️Innanillahiwa'inna ilaihirraji'un faɗar irin halinda shaik ya samu kansa a ciki abu ne mawuyaci gareni bare kuma ga shaik wanda hakan ta faru akan ɗiyarsa, ze iya cewa wannan ranar itace mafi munin rana daya taɓa gani a Rayuwarsa a haka taron jama'ar ya watse kowa da abinda yake tufkawa a ransa, lokacin da labari Fasa Auren Sumaiyya  ya shigo cikin gidaba ƙaramin kaɗuwa Maman shaleletayi ba wani irin jirine ya kwasheta kafin kace me tuni ta yanke jiki ta faɗi, babban abinda ze bawa mai karatu mamaki shine ko ƙwayar hawaye bata zubo daga idanun  Sumaiyya ba dan tasan hakaɓ zata iya faruwa a ranta Su yaya Basirah ma sosai taji abin a ranta dukda hashin sumaiyyar datakeji, Umma kuwa bazaka iya fahimtar komai daga yanayin Fuskarta ba   Beebah ma daga kallon farko bazaka taɓa iya karantar abinda ke ranta ba kamar uwarta Hajiya maryam, a wannan ranar haka zukata suka wuni cikin baƙin ciki marar misaltuwa shin meyafi wannaɓ abin tozarci ace ranar ɗaurin Aurenka miji yace ya fasa?  Meyasa tun a lokacin dayaji labarin bece ya fasa Aurenta ba seda suka bari  aka tara jama'a?, wani hawayene me zafin gaske ya dinga zubowa daga idanun maman shalele hakan yasa zuciyarta ta ƙara raunana, ɗaga hannayenta tayi sama tace "ya ubangiji kayi min komai a rayuwata, haka kuma ka wadatani da mijin mafi nagarta a cikin al'uma  Allah ka bani ƴaƴa guda biyu sannan ka wadatamin su da ilimin alƙur'ani, ya ubangijina meyasa kake min jarrabawa irin wannan me wahalar jurewa?"  da Sauri Yafendu Faridah ta rufewa mama baki tace "kul Badi'atou sam karki sake bari bakinki yay irin wannan furucin me cikeda jahilci a cikinsa, kada ki mantafa ko wani mumini yanada mujarrabin da Allah kan gwada imaninsa akansa Maza ki gaggauta yin istig fari akan Furucin da kikayi"  zubar hawayen idanunta ce ta yawaita fiyeda farko bakinta Na rawa tace "Astagfirulla Allah! Ya Allah na tuba ka gafarta min, ya ubangiji idan har wani laifin nayi maka yasa kake jarrabani akai ina roƙonka ka gafarta min!!!!"  kuka ne yaci ƙarfinta a haka dai mutanan falon suka dinga bata baki.

Ɓangaren shaik ma Hakance ta kasance Sedai dayake Shi namiji ne yasa bekaiga faɗuwa ƙasa ba, amma baiyana irin halinda daya samu kamsa a ciki abune me matiƙar wahala  yanaji yana gani haka jama'ar daya tara suka watse batareda sun shaida auran ɗiyar tasa ba,  zaune yake cikin babban falonsa gaɓaɗaya abin duniya ya gamai masa kanta a rai gefansa kuma Alhaji Muhammad gamawa ne se kuma wani shaƙiƙin Aminin Baba Shaik mai Suna Mumtaz dayazo tun daga ƙasar Sudan, Abou Mumtaz ya dubi Aminin nasa yace "haƙiƙa komai na Rayuwa yanada muƙaddarinsa kuma duk  abinda Allah ya Rubuta shine tabbatacce a rayuwar ɗan Adam,  don haka ka ƙaddara haka ubangiji ya hukunta  "  ajiyar zuciya Muhammad Gamawa ya sauke tareda kallon Baba shaik duk a lokaci guda sannan yace "Babu shakka yadda da ƙaddara yana cikin jerin shika-shikan imani  base na tuna maka hakan ba, fatana a nan shine kada ka bari ƙuncin ɗake cikin zuciyarka ya rinjayi imanin ka kamar yanda waƴanda suka gafala daka Rahamar Allah keyi insha Allah komai zeyi daidai" ya ƙare maganar yana me ƙara masa ƙarfin gwiwa, Abou Mumtaz be sake cewa komai ba hakama Alhaji Muhammad Gamawa a haka duk suka watse suka barshi yana me fashewa da wani irin kuka wanda betaɓayin kamarsa ba, hakanan yakeji a zuciyarsa babu abinda ya kamata yayi face yay kukan koze samu zuciyarsa tai sanyi  a wannan Ranar Baba shaik yayi kukan dabe taɓayin kamarsa ba tunda yazo duniya, babban abinda ke ƙara ɗaga masa hankali Shine Sumaiyya wadda ya raina a matsayin shalelansa tsawon adadin shekarun haihuwarta!  Yasota a Rayuwa so  mafi tsanani, haka kuma ya kyautata mata mafi girman kyautatawa   yay mata tarbiya mafi inganci a Rayuwarta amma meyasa gabaɗayansu da ita da mutanan datai mu'amala dasu suka gaza Fahimtar hakan?  Wani sabon kukan ya fashe dashi a wannan ranar ko masallacin besamu kagarar zuwa jan salla ba sabida wani wahalallan zazzaɓi dayay masa rumfa.

MUTUNCIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now