8

30 0 0
                                    

I think you'd like this story: "MUTUNCIN 'YA MACE" by HAFNANCY01 on Wattpad https://www.wattpad.com/story/278469404?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_reading&wp_page=reading_part_end&wp_uname=HAFNANCY01&wp_originator=iz8CPN6PS5iBijnWCnJyZeR3xCDalw%2FS2dLvdKXzlX%2BoD4ooL404KjXP4OYtWm%2FIlDMCC7FZ5XYl3bXt017qr22oAhCdPbtZGRPGRH60DM92lS1VLMyAmRiFnRyGgHlQ

*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
           _{Babban jarabawa agareta..}_

     
            *NA*

   _Hafsat Hafnan_

                *DA*
   
        _Zainab Chubaɗo_

*Labarin dake ɗaukeda Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fuzgar zuciya❤*

       *08*

"Abban Adil......." ta k'irayi sunansa Cike da mamak'in ganinsa amakarantar tasu, bata gama tsinkewa da lamarin ba sai data had'a kwayar idanunta da nashi sanda ya waigo gareta, idanun nasa sun dan kad'a sunyi jaa, da rawar murya tace"Un....uncle...Ham..Hamza meke Faruwa ne ?, ko wani ne ya mutu ?, ba...baba..Sheikh ina fatar lafiyarsa lau ko ?" tayi tambayar arud'e kasancewar shine mutum mafi kusanci ga zuciyarta " kowa lafiya lau yake babu wanda ya mutu, baba Sheikh d'in nema ya umarceni da inbar abunda nake yi inzo gareki sannan in baki waya kuyi magana, yauwa gashi nan ma ya sake kira..."

"Assalamu alaikum, eh eh Baba gata nan ma muna tare ayanzu " Baba yace"Bata wayar..." mika mata yayi yana fadin"yace abaki wayar..." hannu na rawa ta karba ta kara akunne"Assalamu....." Addana amincinki don bazan karba ba, Sumaiyya ki saurareni dakyau, kina shirin fara zana jarabawarki ta karshe, ko kuma kina kan rubutawar ne, ko kuwa ma dai har kin gama kin fito, wannan ba matsalata bace, abunda kawai na sani shine ina da bukatar ganinki anan Azare cikin gaggawa, kome kike yi ina mai umartarki daki ture ki amsa kirayana, in kuwa kika ce ke sai kin kammala abunda kike kafin kizo to wallahi ban yafe miki ba, in har kina son kanki da lafiya to ki hanzarta zuwa don na had'a taron gaggawa ne domin ki...." kit ya kashe wayar "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" kawai kake ji yana fitowa daga bakinta, hannunta dayan dafe da kirjinta, dayan kuma rike da wayar data kasa saukewa daga kunnenta, hawaye sai zirara kawai suke saman kuncinta tamkar an bud'e famfo, Abban Adil ne yayi k'ok'arin sa hannu ya karbe wayar jikinsa asanyaye yace"me yace miki ? "Cewa yayi in bar abunda nakeyi in taho Azare yanzun nan " hular kansa ya cire yana furta kalmar Innalillahi ya rasa ko menene yake Faruwa dan yana wurin aiki shi baba sheik d'in ya kira yace masa dan Allah yabar abunda yakeyi yaje ga Sumaiyya ya bata waya yana son magana da ita amma dai bai d'iga masa komai ba sai abakinta yake ji, amma yasan duk yadda akai babu lafiya domin daga jin muryarsa kadai kasan atsananin fusace yake "jeki kammala jarabawarki zan jiraki" runtse idanu tayi wasu hawaye masu radad'i suka gangaro mata tace"cewa fa yayi in har na tsallake umarninsa nace saina kammala abunda nakeyi kafin in amsa kiransa to bai yafemun ba, ni ko bama wannan ba, Uncle Hamza bazan iya cigaba da zana jarabawar ba don hankalina atashe yake, bari inyi submitting in taho mu tafi gashi ko sign out bazan samu inyi ba tare da abokan karatuna ba, ranar da na dad'e ina jiran zuwansa gashi yazo mun ahagunce" kuka yaci mugun karfinta, shi kansa duk jarumtarsa sai da hawaye yadan zubo masa, hankici yasa ya share hawaye sannan yakai hannu yana k'ok'arin share mata nata, da sauri ta rik'e hannun nasa zuciyarta na tsuma tace"a'a Abban Adil kabarsu su zuba don baka sani ba hawayen nan zai taimaka wajen rage radad'i da sama mun sassauci azuciya"

sakin hannun nasa tayi ta juya da sauri tana kuka ta koma cikin dakin jarabawar, idanun kowa akanta amma babu halin ritsata da tambayar abunda ke faruwa sai kallo, Zuwa tayi ta dakko booklet d'inta tazo inda ake submitting, ita ce ta farko kuma ba wai ta kammala bane da dan saura, Supervisors na tambayarta abunda ke Faruwa ma kasa tankasu tayi sai k'ok'arin Signing out take akan signing book, dagowar da zatayi sai sukayi ido biyu da Dr. G.G (Garba Gana) sai da gabanta yayi mugun dokawa, wannan shine karon farko da suka jame tun bayan abunda ya afku tsakaninsu, don daga baya tazo ta daina zuwa ajinsa, ayanzu ma shigowa yayi don ya duba in akwai mai korafi tunda cos dinsa ne ake zanawa, da idanun nan nasa ciki ciki kamar an soya gyad'a yake kallonta, har zata rab'a ta gefensa ta wuce sai taji yace"S.M.A menene damuwarki ?, ko ku kun san damuwarta ?," yayi tambayar yana duban sauran supervisors d'in, Mr.Umar ne yace"well, bata mana bayani ba amma na tambayi wanda yazo wajenta ya nunamun cewa shi d'in uncle d'inta ne kuma gida ba lafiya shine ake nemanta da gaggawa " eiyah Allah ya kyauta amma ta samu ta kammala kuwa ?" Yayi tambayar yana kallon cikin k'wayar idanunta wannan karon, bata bashi amsa ba ta rab'a ta gefensa ta wuce amma tana jin sanda Mr.Umar ke bashi amsa har take jin yana umartansa daya miko masa booklet d'inta, da sauri ta waiga amma sai Khadija ta dauke mata hankali datake tunkarota da wani maker ahannu tana fad'i da karfi"Guys let's sign her out before she go " ai kamar jira suke da sauri rabin aji suka mimmik'e kowa da makersa aka nufeta, ita abun ma sai ya bata mamak'i, haka sukayita signing kuma balaifi ta dan tsinci kanta cikin farin ciki, rungumar Khadija tayi tana kuka tace"Thanks much Khadijah Saleh" rad'a Khadijar takai mata akunne"Be prayerful! Nima zan cigaba da tayaki da du'a'i don nasan kiran da ake miki bana lafiya bane amma ki sani Allah na tare da mai gaskiya, kije sai munyi magana " haka suka rabu suna kuka...

MUTUNCIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now