23

21 1 0
                                    

*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
           _{Babban jarabawa agareta..}_

     
            *NA*

   _Hafsat Hafnan_

                *DA*
   
        _Zainab Chubad'o_

*Labarin daya ƙunshi Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fuzgar zuciya❤*

     

        *23*

_____✍️"Tambayarki nake me kikajeyi a ɗakina?" Sumaiyya ta faɗi hakan yayinda take kallonta cikin ido kamar yanda Asma'un itama ke kallonta, Cikin yanayi na ko'in kula Asma'u tai mata wani irin  kallo irinna rainin hankalin nan sannan tace "me kike tsammanin zan shiga ɗakinki nayi?" wani ƙaya ltaccen Murmushi ta kasheta dashi sannan ta basar da ita tareda raɓawa ta gefanta zata wuce Sumaiyya ta wani irin figota a Mugun Hasale tace  "wllh sekin gayamin uban me kikaje yi a ɗakina?"  tafiyar da Asma'u tajiyo daga bayanta ne yasa ta ƙwalla wata uwar Ƙara cikeda makirci, kafin kace me tuni hawaye ya wanke mata fuska

Sulaiman dake dabda ƙofar falon jin ihun Asma'u yasashi  shigowa da gudu sabida yanda ihunta ya karaɗe falon, Sandarewa Sumaiyya tai a tsayesabida tsabar mamaki ta kasa magana.     Balle tai motsin kirki sakin hannunta tai da sauri taja da baya ita kuma Asma'u ta zube a gurin hannunta dafe da kumatunta, da sauri Sulaiman ya isa gareta tareda ɗagota A mugun ruɗe  yace "Asmy meya faru ?" ya faɗa yana riƙe fuskarta da dika hannayensa biyu, fashewa tayi da wani irin kuka bakinta har rawa yake sabida kukan datakeyi daƙyar ta iya buɗe baki tace " Sulaiman marina fa tayi har so biyu bayan ta gama zakin iyayena!. Koda yake bazan taɓa ganin laifin Sumaiyya ba dan taci zarafina nasan kaine kabata dama, da ace ka nuna mata mahimmancina wllh bazata taɓa iya ɗaga ido harta iya zagin iyayena b.........!!!! Kuka ta fashe dashi tareda miƙewa ta shige ɗakinta harda bunko ƙofa.

Wani irin mugun kallo ya shiga aikawa Sumaiyya tun kafin ta ankara ya ɗaga hannu ya zabga mata wani ɗan iskan mari wanda yasa gefan bakinta fashewa,  sannan ya nunata da yatsa cikin ɓacin rai yace "Sumaiyya idan ma wani abu ne ya shiga tunaninki akan salonda kika ɗauka na wulaƙanta min mata toki gaggauta dawowa cikin haiyyacinki don wllh bazan ɗauka ba!!!!"

Wani irin baƙin ciki ne ya cika zuciyarta amma sabida takaici duk yanda Taso ta hana kanta kuka kasawatayi tanaji tana gani hawaye ya fara zirarowa a saman kyakkyawar fuskarta,  bata sake kallonsa ba ta  shige ɗakinta ta haɗe kanta da gwiwanta ta fara gurzan kuka  Duk yanda taso ta dakatr da zubar hawayenkasawa tayi haka ta dinga rera kuka har 11:30 na dare, shima sabida azabar ciwon da kanta keyi ne yasa Dole ta rarrashi kanta tai shiru

Washe hari daƙyar ta iya miƙewa tai sallar Asuba sabida zazzaɓin daya rufeta, ko miƙewa bata iyayi a haka ta kwanta saman daddumar tai lamo da ita tna sauke numfashi akai-akai. Se wurin ƙarfe takwas ta iya buɗe idanunta shima sabida buɗe ƙofar ɗakin da akayi ne yasa ta buɗe ɗin, baƙon ƙamshin turaren dataji ne yasa ta ɗaga fararen idanunta da suka janye sabida zazzaɓin dake jikinta, maida idanunta tai ta lumshesu batareda  ta sake kallon bakin ƙofar ba. Murmushi Asma'u tayi tareda  ƙarasa shigowa ɗakin cikin shigar riga da zani na atamfa holand ruwan ganyen da yarfan ja a jiki ta kashe uban ɗauri, kallo ɗaya zakai mata kasan tana cikin farin ciki mara misali  tsugunawa tayi dedai inda Sumaiyya zataji abinda take faɗa tace "Eyyah gaskiya ina jajanta miki  bisa gangancin Auren mijina da kikayi Sumaiyyah Muktar Azare."  wani ƙayataccen murmushi ta sake daki wanda yaƙara ƙawata fuskarta sannan tacigaba da cewa "ko'a cikin jerin tsintsaye ni mikiyace, shiyasa ko wani tsintsu dayaji na fito ina shawagi yake shiga tashin hankali, wllh kinji nai miki rantsuwa sena koya miki darasin da ubanki ma besanshi ba balle har ya koya miki ki haddace, wannan ma kaɗan kika gani kijira mu koma abuja kiga abinda nai miki tanadi!."  tana kaiwa nan ta miƙe tabar mata ɗakin tana murmushi, a daining ta samu Sulaiman tana shan kunun data dama as breakfast  ɗago manyan idanunsa yay yana kallonta yace "where is she? " taɓe baki tayi tareda goge ƙwallar dake neman zubo mata tace "tana ɗaki" ta faɗa a taƙaice kamar zata fashe masa da kuka.  Kallon tsaf yayi mata sannan yace "what's wrong? " share hawayen dake zubo mata tayi sannan tace " nayi kuskure sosai a rayuwata da har nakewa Matarka Sumaiyya kallon ƙanwa a gareni shiyasa take min kallon mara daraja, da ace tun farko baka bata damar hakan ba na tabbata bazata zagi iyayena don kawai na bita ɗakinta nace tazo tai breakfast ba!!!!"  tashi yay tareda ajiye cup ɗin hannunsa ya zagayo inda take zaune ya rungumeta ta baya, kansa ya kwantar a saman kafaɗunta a hankali ya buɗe bakinsa daya masa wani irin  nauyi sabida tausayinta yace "I'm so sorry babe but yanda kike tunanin na bawa Sumaiyya dama sam abin ba haka yake ba,idan har zan bawa wata mace dama a Rayuwata to kece  Asma'u lokaci kawai nake jira in tabbatar miki da hakan."  wani ƙayataccen murmushi ta saki cikeda da makirci, tareda ƙuɗurtawa kanta cewar wllh seta dasawa Sulaiman tsanar Sumaiyya a ransa musamman data lura kamar akwai wani ƙaramin saɓani a tsakaninsu.

MUTUNCIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now