21

29 0 0
                                    

*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
           _{Babban jarabawa agareta..}_

     
            *NA*

   _Hafsat Hafnan_

                *DA*
   
        _Zainab Chubad'o_

*Labarin daya ƙunshi Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fuzgar zuciya❤*

     

        *21*

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un wallahi Balarabe ka cuceni kuma kaci amanata! ka rasa wacce zaka lalatawa rayuwa sai d'iyata ta cikina ? shiyasa akace dan adam butulu, idan ka masa rana shi kuma sai yayi maka dare, idan har ban manta ba akan titi na dakkoka na kawoka cikin iyalina, na suturtaka, na baka muhalli sannan na baka aikin gadi, baka nemi komai ka rasa ba, kamawa daga ci, sha da kuma kulawa ta musamman inka kwanta ciwo, Balarabe shine saika rasa abunda zaka sakamun dashi sai lalata d'iyata ? 'ya daya kwal da Allah ya azurtani da ita ? har tsawon yaushe ma kuka dauka kuna aikata Wannan barnar bamu da masaniya akai don wannan ya nuna ba shine farau dinku ba, alamu ya nuna Fatima ta dad'e da rasa *MUTUNCINTA* na *'YA MACE* ,wani mara imanin ya amshe budurcinta kuma ina tsammanin kaine ...." ya ida magana gami da barkewa da kuka yakai masa mugun shuri, Balarabe da idanunsa suka gama raina fata, Zufa sai keto masa kota ina yake, yace"Alhaji kayi hakuri wallahi sharrin shaidan ne, lallai na kasance butulu , kamun alheri ni kuma saina saka maka da sharri, kuma kayi gaskiya nine namiji na farko daya soma tarayya da Fatima, ma'ana nina kau da budurcinta sannan kuma mun dauki tsawon lokaci muna aikata wannan abu ba tare da sanin kowa ba.... "Safara'u ku fitar mun dashi kafin in kashe banza anan, bani wayata human right sai ta shiga wannan al'amari " magana yake daqyar hannunsa dafe da kirji, jikinsa sai rawa yake tsabar tashin hankali, ga wasu hawaye masu radad'i dake bulbulo masa saman kunci, Zuciyarsa kuma tafarfasa take sosai, da sauri sukayi kansa ganin halin da yake ciki, daqyar yake iya fadin"Lallai Sumaiyya tayi gaskiya data ce saina girbe abunda na shuka, abunda nake yiwa ya'yan mutane sai an rama akan nawa, wannan gaskiya ne alkawarin Allah kenan, ya Allah na tuba ka yafemun .." Maganarsa ta yanke ayayin da Numfashinsa ya tsaya cak! Wani irin kara Hajiya Safara'u ta Fasa tana girgizashi sosai "Alhaji ! Alhaji !" babu amsa, afusace ta waiga ga Balarabe dake bayanta yana wasu 'yan kame kame ta doka masa tsawa"wallahi ka sani in ya mutu kaima saika mutu ! Allah na tuba ma in ba don kaddara ba har me Fatima ta gani na burgewa atare dakai da har ta sakar maka jiki ka gama mommoreta ? Koda yake ubanki ne ya jawo miki wannan masifar " ta furta idanunta akan Banan dake cizgar kuka tana "Daddy don Allah ka tashi bazan sake bata maka rai ba " wani tsawa uwar ta doka mata wanda yasata ida gigicewa "Shegiya zaki je ki dakko makullin mota mu kaishi asibiti ko kuwa sai mun rasashi sannan hankalinki zai kwanta ? " arud'e ta juya bata masan inda kanta yake ba "Nan ne dakin ?" Haka taji Mum din nata ta fad'a, sai asannan ne hankalinta ya dawo jikinta, ashe madafi ta nufa, da sauri ta canza direction zuwa master bedroom d'insa ta dakko makullin, Hajiya Safara'u koda wasa bata bari Balarabe ya tab'ashi ba, ita da Basira me aiki ne suka ciccibeshi zuwa mota, ita da kanta tayi driving zuwa wani private hospital a inda suka amsheshi cikin gaggawa ganin irin halin da yake ciki wanda baza'a iya tantance akwai rai ko babu rai atare dashi ba sai anji ta bakin likitoci.

 

    ***

Gama cin abincinta kenan ta shiga daki don kwantawa ta dan huta sabida wani irin ciwon kan daya saukar mata, daga jiya zuwa yau tana cikin damuwa don kwata kwata ta rasa gane kan Man d'inta, gabaki daya yabar shiga harkanta, ko magana take masa da fada fada yake amsata, haka ma in taje kusa dashi tashiwa yake yabarta mata wurin, ta rasa laifin me ta masa yake gasata ta ruwan sanyi haka amma ta shirya tisashi agaba aduk sanda kwanakin girkinta ya zagayo, yanzu akwancen take amma baccin ya gagara zuwa, hawaye sai diga yake saman zanin gadon amma ko kadan bata damu ta tsaida zubar nasu ba, bata san da shigowarsa ba sai jin saukar amon maganarsa tayi atsakiyar dodon kunnuwanta "ki tashi ki shirya kayanki gobe idan Allah ya kaimu da sassafe zamu wuce Abuja " da sauri ta tashi zaune idanunta akansa, tsaye yake abakin gadon Fuskarsa amurtuke tamkar bai tab'a sanin dariya ba, kuma ba ita d'in yake kallo ba, hannunta dake rike da wani hotonsa wanda ya jike da ruwan hawayenta shi ya kurawa ido, ji yayi tace"Tafiya da sauri haka ? Ni ku tafi abunku ku banni zan zauna anan dasu Gwaggo ." Wani wawan kallo ya wulla mata wanda yasa gabanta fadiwa yace"uban wa kike son ki dunga bawa aikin dogon tafiya duk bayan kwana bibbiyu ? in kuma ke zaki juri zuwa ai shikenan sai in bar miki wannan aikin " kai ta shiga girgiza masa sabbin hawaye na ziraro mata tace"haba Man kai ba kaya ba to menene kuma na hawan farashi ? in laifi na maka dan girman Allah ka gayamun in roki gafararka sannan awuce nan, mu koma zaman lafiya kaji pls Man i miss the way we use to be " ta fad'i hakan tare da rungumar kafarsa daya, sosai yaji tausayinta na kokarin tsirguwa aransa amma idan ya tuna da wani abu sai yaji kawai ya tsaneta, kuka ta sake fashe masa dashi tace"Wallahi Man Maya tana kewar murmushinka, tana kewar dariyarka, tana kuma kewar dumin jikinka, infact Maya na kewar komai na Man d'inta " sosai yacika da mmakin ta yadda har akai yayi sakaci ta fad'a tarkon sonsa alokacin da bai shirya sama mata gurbi azuciyarsa ba..."Kaji Man d'ina..." ta sake furtawa cikin jan hankali, hannu yasa ya dago habarta, kwayar idanunsu ya gauraye dana juna, dukkaninsu sai da suka ji wani abu na yawo aransu, tsawon lokaci suka dauka ahakan kafin daga bisani yayi kokarin kau da shirun yace"Sumaiyya Allah dai yasa ba sona kika fara yi ba, in kuwa hasashena gaskiya ne to ina me shawartarki da ki gaggauta yakiceshi daga ranka domin ban shirya sama maki gurbi azucina ba, adon haka kibar wahalar da kanki abanza, sannan ni baki mun laifin komai ba nine dai kawai naga dacewar in dauke miki kafa don banason ki cutu da yawa da sona alhalin ni ban shirya miki ba, yanzu dai ki tashi ki cika umarnina ki had'a kayanki, banason tarkace akwatina biyu kacal sun isheki, sai wasu daga cikin muhimman abubuwanki da zaki tafi dasu, sannan in kin gama ki shirya kanki bayan Zuhur zamu shiga Azare kiyi musu sallama " yana gama fad'in hakan yasa kai yabar dakin, yabarta nan durqushe tana rera kuka amma abangare daya tana me farin ciki da ganin ayau zata je ganin gida zata ga Babanta da Mamanta da kaninta Emran wanda rabonta dasu tun randa aka kawota Zaman aure !

MUTUNCIN 'YA MACEDonde viven las historias. Descúbrelo ahora