*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
_{Babban jarabawa agareta..}_
*NA*_Hafsat Hafnan_
*DA*
_Zainab Chubad'o_*Labarin daya ƙunshi Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fuzgar zuciya❤*
*27*
_____✍️Bata wani jima a tsaye ba sega Driver ɗin hajiya Safarah yazo ɗaukanta a wata jakar motar wadda ta amsa sunanta mota, fitowa yay ya buɗe mata tareda faɗin "varka da zuwa rankishidaɗe" yatsina fuska kawai Asma'u tayi alamar ta ƙosa da shegen surutunsa, ƙaramar akwatin ta ya karɓa yasa a bayan motar sannan ya dawo yaja motar sukabar harabar filin jirgin, nan ma tafiya sukai me nisan gaske hartaji ta ƙosa da nisan tafiyar ta zari wayarta wadda tun saukarta taji ƙarar shigowan message
Ganin daga bakin datake amfani dashi ne yasa tai saurin buɗewa 5million tagani an mata transfer, wani irin ƙwalalo idanu tayi a lokacin dataga sunan wanda ya turo mata da kuɗin don haka da sauri ta fita a gurin message ɗin ta fara ƙoƙarin kiransa, Alhaji madugu wanda ke zaune a office yay murmushi irinna ƴan iskan masu kuɗinnan sannan ya ɗaga yace "Baby yadai ina fatan kinga saƙona" wani irin fari da idanu Asma'u tayi tace "yes nagani my boo sedai ƙwaƙwalwara ta kasa yardar min da abinda idanuna suka gani" Madugu yay dariya irin wadda ke cikeda izza yace "gimanki da kimarki ya zarta haka babyna, nan gaba ma kyautar dazan miki wllh setasa numfashinki tsayawa a lokacin da idanunki suka ganemiki ita." dariya Asma'u tai cikin wani irin sauti wanda tasan yana haukata kwarton nata tace "shiyasa kake Maliya na tabbata ba banza yasa kake amsa wannan sunan ba" ƙwarai kuwa baby ai dama idan kikaji ance wane to wllh babanza ba" Madugu ya faɗi hakan yayinda yake kai hannunsa saman wandonsa yana shafawa, numfashin dayake ja ne yasa Asma'u faɗin "My boo badai Alawa me tsinkena bace take neman tashi?" Madugu ya lumshe idanunsa kaɗan tareda mirza kan abar tasa yace "wllh baby itace da alama tanaso tajita a cikin kogin zumarki wadda ke mantar dani kaina da duk wani abu dana tara" karka damu my boo nanda gobe zakaji ka a faɗata kuma na maka alƙawarin cewar zan maka cinda har ka mutu you will never forget it, kaidai kawai ka ƙara haƙuri." Asma'u ta faɗi hakan yayinda ta katse wayar cikin zumuɗin ganin sun iso gidan Hajiya Safara'u wadda takewa laƙabi da Hajiya Safa. Buɗe mata ƙofar Driver ɗin yayi ta sakko a ƙasaice wanda hakan ya ƙara fito da ƙasaitarta irinta manyan mata ƴan barikin gaske, gaba yay da akwatinta tana take masa baya har suka shiga haɗaɗɗen falon gidan wanda keta zuba ƙamshi me bala'in daɗi
Lumshe idanunta Asmy tayi tareda shiga tsakiyar falon ta zauna akan ɗaya daga cikin royal chairs ɗin da sukama falon ƙawanya, yana ajiye akwatin ya juya ya fice batareda ya sake waiwayonta ba donya cika umarni, batafi mintuna2 da zama ba Hajiya Safara'u ta fito cikin takunta na isa da ƙasaita sanye take cikin wata baƙar riga wadda ta baiyana kyakkyawar surar da Allah yay nata, gabaɗaya ilahirin manyan nononta duk a waje suke tamkar bata sanya tufafi ba cikin kwainane irin nasu na ƴan bariki kokuma ince waƴanda Allah ya kwashewa albarka ta ƙarasa falo se baza wani uban ƙamshi takeyi tace "maraba da..." kasa ƙarasawa tayi sabida sarƙewar da idaninsu yay cikin na juna, gabaɗayansu Kallon juna suke a matiƙar kiɗime asma'u kuwa zuface ta fara keto mata tindaga saman goshinta har zuwa dokin wuyanta.
****
Abuja Nigeria.
"Muktar nakan rasa meye matsalata a duk lokacin danakeson kusantar iyalina Sumaiyyah kuma abinda yake qara ɗauremin kai shine sam bana samun wannan matsalar idan ina tareda Asma'u kokaɗan!" Man ya faɗi hakan damuwa kwance a saman kyakkyawan fuskarsa, Ajiyar zuciyar muktar ya saki meɗan nauyi sannan ya dafa kafaɗunsa yace "Gamawa dukna fahimceka kuma insha Allah ka ƙaddara matsalarka tazo ƙarshe a yau ɗinnan base anjima ba" kallon galala Man kebinsa dashi harya miƙe ya shiga hanyar dazata kaishi bedroom ɗinsu kasancewar fasalin ginin duk iri ɗaya ne danasu Man ɗin, be wani jima a ciki ba ya fito hannunsa ɗauke da wata ƙaramar roba me murfi wadda ke ɗauke da ruwa me haske a ciki kamar zam-zam, miƙa masa yayi yace "kasha ka bani robar yanzu base anjima ba" kallon tuhuma Man kebinsa dashi inda wani ɓangare na zuciyarsa ke cike tabda tarin tambayoyi akansa, dariya Muktar yayi sannan yace "tun lokacin danaga sauyi a tareda kai naji A jikina cewar kanada matsala ama kuma shegen zurfin cikinka ya hanaka ka gaya min, to shine nayi amfani da wannan damar na Sanarda Baffah Umaru ya haɗa maka wannan maganin" tunda ya fara magana Man ke kallonsa harya kai ƙarshe, haka kuma sosai yaji kimar Muktar ta ƙara nunkuwa a cikin zuciyarsa murmushi ya saki wanda ke baiyana zallar godiyarsa ga aminin nasa yace "haƙiƙa na yaba da wannan karamcin naka gareni Muktar, haka kuma har abada bazan manta wannan alkhairin ba" dariya muktar yayi sannan ya ɗaga girarsa ɗaya yace "ikon Allah kace ko yanzu na mutu nabar maka abinda zaka dinga tunawa" murmushi Man tayi yace "tabbas" dan jim sukai kaɗan sannan muktar yace "indai har akwai sammu ko Asiri a taredakai Sulaiman to wllh dazaran kasha ze karye da izinin Allah, sannan kuma kaida kanka zakaji canji a tareda kai." kwance murfin rObar man yayi tareda cewa "ai banga ta zama ba tun yanzu barinsha ya faramin aiki" dariya sukai gabaɗayansu suka tafa muktar yace "to kashada bisimillah" se'a lokacin Man yace "kagaida Ma'am zee idan ka koma gida dukda ranar ka gama haɗamu da ita" dariya kawai Muktar yayi yace " insha Allah zan gaya mata." sun jima sosai suna hura sannan man ya miƙe yay masa sallama, harya isa jikin motarsa da sauri Muktar ya dakatar dashi yace "Yauwa kaga na ɗan sha'afa bamuyi magana akan mamallakun wannan number da kace ai maka binkice akai ba" ɗan zaro ido gamawa yayi kaɗan sannan yace "Wldone Bakori to yanzu ya ake ciki an samo location ɗin mutumin ne?" "Ae an gama binkice akan number ɗin harma an gano cikakken bayanai akansa kai harma da gidan ubanninsa" Fuskar Sulaiman ce ta canza lokaci guda yace " Muktar don Allah kayi magana dasu duk inda yake ina buƙatar ya shiga hannun hukuma a daran yau pls." kallon tsaf muktar kebinsa dashi sannan ya harɗe hannunsa bisa ƙirjinsa yace "Gamawa wai me mutumin nan yamaka haka da kake ɓarnatar da kuɗinka akansa don kawai ya shiga hannun hukuma?" a ɗan zafafe Man yace "abinda yaymin kakeso kaji?" idanunsa ne suka rine sabida takaicin video ɗin da aka tura masa, mota ya shiga kawai yay mata key ba tareda ya kuma cewa Aminin nasa ƙala ba yabar harabar gidan gabaɗaya ransa na masa zafi.
YOU ARE READING
MUTUNCIN 'YA MACE
Action"Sumaiyya ki sani wallahi sai an buga sabon kafce! Koda ni Muntasir zanyi yawo tsirara acikin duniyan nan ne saina tabbata na lalata miki rayuwa ta yadda nan gaba bazaki moru ba ko agidan aurenki!." Muntasir na tsaneka!na tsani duk wanda ya sanka! n...