15

56 2 4
                                    


*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
           _{Babban jarabawa agareta..}_

     
            *NA*

   _Hafsat Hafnan_

                *DA*
   
        _Zainab Chubad'o_

*Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fuzgar zuciya❤*

     

        *15*

________✍️Wayar ce ta ɗauke duk yanda yaso ya kunnata amma sam se abin yaci tura, kallonsa shaik yayi da dara-daran idanunsa zeyi magana kiran waya daga Abou Mumtaz ya shigo masa dole tasa shaik ya miƙe don wayar na buƙatar sirri, shaik na fita Muntasir daya maƙale ɗaga jikin ƙofar ya fito yana bin baban ikilima da wani ɗan iskan kallo wanda yasashi shan jinin jikinsa,  tun shigowar Baban Ikilima cikin gidan Muntasir daya hangeshi ta window yaji yana zarginsa ai kuwa bisa ga mamakinsa se gashi tunanisa yay dedai da zarginsa, don haka ya zaro wani farin hankici daga aljihun gaban rigarsa ya nufeshi gadan-gadan ya shaƙa masa in less then 2 minute ya ɓingire a gurin da bacci,   ja da baya yay da sauri dayaji tafiyar shaik don haka ya maze kamar bashi ba yace "Baba meya kawo wannan mahaukacin nan gurin ?, gaskiya dai ya kamata a fita dashi tun kafin ya farka  a nan mu shiga uku" cike da mamaki Baba Sheik yace"ikon Allah yanzu fa na barshi lafiyarsa qalau ashe mahaukaci ne ban sani ba ?, to amma abun da matukar daure kai ko menene yake k'ok'arin nunamin awayarsa shine ban sani ba, ya kunnata kenan sai ga kiran Abou Muntaz ta shigo, anya wannan din mahaukaci ne kuwa don kokarin diga mun magana yake akan Sumaiyya kuma ni ban ga alamun rashin hankali atattare dashi ba illa tsoro..." Zuciyar Muntasir na bugawa yace"Baba wallahi ka yarda dani mahaukaci ne, haka zaka gansa tamk'ar mai hankali amma anan d'in Allah ya ragewa aya zakinta, ni na sanshi tunda dadewa kai ne dai baka tab'a ganinsa ba sai yau, yanzu in aka bibiya shirmensa ne yazo yayi maka shine ya bingire da bacci..." Baba sheik ya girgiza kai yana mai jimanta al'amarin yace"To Allah ya kyauta, yanzu dai kayi maza ka fitar dashi waje sannan kace da matan gidan daku kanku 'ya'yan ina son ganinku duka, yauwa ga ma Emran nan bari ya tayaka isar da sakon " Muntasir ya ciccibi Baban Iklima dake sharar baccinsa hankali kwance hadda munsharinsa, Baba kuma ya bawa Emran sak'onsa zuwa cikin gida..

Muntasir ya kwashe kusan mintuna ashirin kafin ya dawo, kuma Allah ne kadai yasan inda yakai Baban Ikliman, yadai fad'o gidan ne ahargitse ya tarar tuni kowa ya hallara shi kawai ake jira, kowa sai tambayarsa yake"yana ganka ahargitse ?" Inda inda ya fara yana sosa k'eya alamun rashin gaskiya yace"wallahi wani mahaukaci ne ya shigo gidan shine ya bani wahala haka, daukansa nayi har can babban titi don wurin na saba ganinsa.." sai ikon Allah ake ta fadi, Baba sheik yayi gyaran murya yace"yauwa dama kai kadai ka rage da ake jira don ya zama lallai yakasance babban yaya yana kusa ya shaida auren yar'uwarsa, kodayake wannan tsohon zance ne nake maka, kamata yayi in damk'a maka sadakinta ahannunka..." washe haqora yayi yana fadin"Kai masha Allah yaushe Habiban tayi miji har ana maganar sadakinta bamu sani ba ? " a'a bafa Habiba nake nufi ba.." Baba Sheik ya furta yana kallonsa, Wani irin bugawa Zuciyarsa tayi yace yana inda inda"to..to..wa...wa kake nufi kenan baba ? " Baba yace"Habiba ce kadai kanwarka ?, to ni Sumaiyya nake nufi, awannan ranar da Allah ya kaddari cewar Fu'ad ba mijin aurenta bane, Cikin k'ankanin lokaci yayi mata sauyi da mafi alheri, ya zab'i nagartaccen namiji acikin wannan taron ya musanya mata dashi, abin nufi anan shine, bayan shi Mahaifin Fu'ad mai girma Gwamna yayi kokarin kunyatar dani sai Allah yace bazai bari inji wannan kunyar ba, Mahaifin yaron nan dalibina dake kawomun ziyara lokaci zuwa lokaci wato Suleiman Gamawa, Mahaifinsa Alhaji Muhammad Gamawa ya nemawa dansa auren Sumaiyya Mukhtar Azare, ayayin da babban aminina Abou Muntaz shi kuma ya karbawa d'iyar tasa auren! Ban sanar da kowa ba domin ina gudun kar abunda ya faru ya sake Faruwa, wato wani ya sake zagawa yaje ya zuga saurayin har yace ya fasa, abunda ya faru da sumaiyya inaso kowa ya sani mukaddari ne daga Allah wanda babu wanda ya isa ya gujewa kaddararsa walau me kyau ko mara kyau, nasan ni kaina naso in dan kauce hanya ta hanyar tsananta mata amma daga baya sai nayi wa kaina karatun ta nutsu sanda na tuna cewa fa Manzon Allah saw yace,  Idan Allah yanason mutane sai ya Jarraba su, wanda ya yarda sai ya sami yarda, wanda yayi fushi sai ya gamu da fushi, Manzon Allah saw yace, Manya manyan sakamako yana tare da manya manyan bala’o’i,Manzon Allah saw yace, Idan Allah yana nufin bawansa da alkhairi sai ya gaggauto masa da Tsanani a duniya, Manzon Allah saw yace, Babu wata musifa da zata shafi  mumini ko mumina,  tun daga taka kaya, ko fiye da haka face sai Allah, ya Daukaka musu daraja, ko ya kankare musu zunubi, Allah yana jarabtar wasu
Domin Ya yafe musu zunubi, Domin ya Daukaka musu daraja
Domin ya yi musu Jan kunne kan wani abu da sukayi da kuskure
Domin ya Jarraba imaninsu da kaddara, kunga kenan anan muna iya cewa kowa da tasa jarabawar da kuma kaddarar, don haka daga rana irinta yau bana son kowa ya sake ciwa Sumaiyya Fuska, kowa yaje yaji da nashi aduwawunsa, har gobe Sumaiyya yarinya ce me wannan hankali da kuma kokarin kiyaye wasu dokokin mahaliccinta, don kawai akaron farko na rayuwarta ta aikata ba daidai ba be kamata ace duk mun juya mata baya ba, Sumaiyya Allah yayi wa rayuwarki albarka, Allah kuma ya baku zaman lafiya, sai dai na manta ban tambayeki ba ko kina ra'ayin wannan auren da muka daura miki ba tare da mun nemi jin ta bakinki ba ? "

MUTUNCIN 'YA MACEDove le storie prendono vita. Scoprilo ora