I think you'd like this story: "MUTUNCIN 'YA MACE" by HAFNANCY01 on Wattpad https://www.wattpad.com/story/278469404?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_reading&wp_page=reading_part_end&wp_uname=HAFNANCY01&wp_originator=iz8CPN6PS5iBijnWCnJyZeR3xCDalw%2FS2dLvdKXzlX%2BoD4ooL404KjXP4OYtWm%2FIlDMCC7FZ5XYl3bXt017qr22oAhCdPbtZGRPGRH60DM92lS1VLMyAmRiFnRyGgHlQ
*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
_{Babban jarabawa agareta..}_
*NA*_Hafsat Hafnan_
*DA*
_Zainab Chubaɗo_*Labarin dake ɗaukeda Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fuzgar zuciya❤*
*09*
Miƙa mata farar takaddar dake hannunsa yayi Ba tareda ya iya ce da ita ƙala ba ya juya ya koma falon, gabanta ne yay wani irin dokawa nan da nan cikinta ya fara juyawa wata irinnzuface ta fara karyo mata hannunta kuwa seka rantse lantarki aka jona mata sabida tsabar Rawan dayakeyi, da sauri ta miƙe da zimmar tabishi falon sukai karoda juna yayinda yake ƙoƙarin shigowa ita kuma zata fita, tsareshi tayi da ido jikinta na rawa ba shiri ta fashe masa da wani irin kuka tana faɗin"wani irin laifi na aikata maka dana cancanci irin wannan hukuncin da tsakar Ranar nan? Wllh Sulaiman ba laifina bane idan har inada lefi to be wuce dabaibayinda zuciyata tayi min ba, nasan ba lallai ka iya kai zuciyarka nesa akan laifin danayi maka ba amma tabbas Alƙawarin Allah gaskiya ne kuma yanason bayinsa masu yafiya da kuma Haƙuri,banaso ka zama mutumin daze zama silar datse farin cikin rayuwata ta hanyar yakice ni Idan har kayimin hakan to ka sani ka cutar da zuciyar da ta daɗe tana dakon sonka!" ta ƙare maganar tana ƙara sautin kukanta, tunda ta fara magana yake kallonta cikeda Rashin Fahimtar inda maganganunta suka dosa cikeda ƙosawa da shirmen surutun ta ya raɓa ta gefanta ya shige bedroom ɗin ya barta nan zube tana gurzar kuka. haka kawai yakejin wani irin haushinta wanda idan aka tirkeshi baze iya cewa ga dalili ba, a haka Asma'u ta kwana cikin zullumi da rashin nutsuwar zuciya.
****
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un..." shine kawai kake ji na fita daga bakin Sumaiyya hawaye masu radad'i na zuba bisa kumatunta, izuwa yanzu kuma bugun zuciyarta ya tsananta fiye da misali, mayar da tabarau d'in yayi ya rufe idanun ganin su Yaya Basira sun sawo kai cikin gidan, da hanzari ya fada dakin taron Zuciyarsa fari kal ganin Sumaiyyar acikin kunci wanda dama hakan ne burinsa akodayaushe ya kuntata mata! ,Ya Asiya babbar yayarsu ce ta daga labule ta lek'o dakai waje tana fad'in"amma kin san ke ake jira da kika wani tsaya anan ko ?" Mamansu ce ta kada baki tace"ke kuma keda wa uwar masifa "wa kike zaton zan fadiwa hakan in ba Sumaiyyar ba ?, ta iso amma ta tsaya awaje ko kulle kullen me takeyi ne ohon mata " Maman ta tab'e baki tace"abinki da mara gaskiya ai ko acikin ruwa gumi yake " ta ida maganarta tana satar kallon Maman shalele dake cikin wani irin hali mara misaltuwa, tun dazu Haj.Maryam da zaratan ya'yanta mata biyar keta sossoka mata! ,Baba Sheik kuwa tunda ya hango Shigowarta kasancewar zaune yake adaidai saitin windo sai kawai ya saukar dakai kasa kirjinsa na bugawa, yana jin sanda Muntasir ya zauna agefensa amma bai dago ya dubeshi ba.Maganar da yaya Asiya ta mata ne yasa ta tsinci kafarta da motsawa, tuni yaya Basira har ta shige ciki abunta, Abban Adil ne keta bata magana suna tafe har sukayi sallama, darajar Abban Adil d'in ne ma kawai yasa aka amsa sallamar, Numfashinta ne ya tsaya cak ganin irin kallo kallon da kowa ke binta dashi kamar anga kashi ajikinta, Baba Sheik kuwa kallo daya tayi masa ta karanto damuwar dake tattare dashi duk kuwa da cewa bai dago ya dubeta ba amma tasan akwai tashin hankali ayau! ,dakin acike yake don ya'yan Haj Maryam duka su takwas din suna ciki, mata bakwai namiji daya kuma shine Muntasir, shidda sunyi aure auta Beebah ce kawai ta rage da batayi ba wacce tsakaninta da Sumaiyya 'yan watanni ne kawai, ita kuma Sumaiyyar ita ce d'iya ta farko awajen Haj Badi'atou, sai kannenta maza biyu! ,bayan kowa ya nutsu Sheik ya dubeta da jajayen idanunsa yace"Babu shiri Sai kika samu kiran gaggawa daga gareni hakane ? " Eh eh Baba meyake Faruwa ne ? naga kowa sai bina yake da kallon banza wallahi ni ban aikata komai ba ku yarda dani " hannu tasa ta toshe bakinta jin kuka ya kufce mata " dama waya ce kin aikata wani abun ?, kunga irinta ko ai dama na fada muku mara gaskiya ko aruwa gumi yake " Mamansu Muntasir ta furta akufule...da sauri Baba ya daga mata hannu"kin ga Maryam banason in sake jin muryarki har atashi wannan taron inba nine da kaina na bukaci jin ta bakinki ba "
YOU ARE READING
MUTUNCIN 'YA MACE
Action"Sumaiyya ki sani wallahi sai an buga sabon kafce! Koda ni Muntasir zanyi yawo tsirara acikin duniyan nan ne saina tabbata na lalata miki rayuwa ta yadda nan gaba bazaki moru ba ko agidan aurenki!." Muntasir na tsaneka!na tsani duk wanda ya sanka! n...