*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
_{Babban jarabawa agareta..}_
*NA*_Hafsat Hafnan_
*DA*
_Zainab Chubad'o_*Labarin daya ƙunshi Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fuzgar zuciya❤*
*22*
"Wa yace ki Fito ?" ya tsareta da idanunsa wa'enda ke neman sata ta zauce, cikin in ina tace"Na aza ko dubiya muka zo yi kuma kana da bukatar rakiyata " haka nace miki dubiya muka zo ? Sannan kuma inda ina da bukatar kimin rakiya zan baki izinin Fitowa ..." hawaye ne sharr ya zoma zuba mata, Allah ya gani bata jin dadin sabbin halayen da Man ke gwada mata, gashi ta lura shima d'in yana da zurfin cikin tsiya kamarta, ya kasa sanar da ita laifin data masa balle ta bashi hakuri sannan awuce nan..."Maza koma ciki ki zauna ki jirani bazan dad'e ba, kuma karki sake in dawo in sameki kina kuka in ba haka ba ranki zai fi nan baci " amsawa tayi da "To " sai kuma yaji ta dan bashi tausayi amma ko kadan be bari hakan yayi tasiri aransa ba, asanyaye ya koma ciki ta zauna Zuciyarta na zafi...ba'a fi 10mins ba sai ganinsa tayi ya dawo ya mika mata wani bakar leda ta windo, turus tayi tana kallonsa yace"karbi man kin tsaya kina kallona " hannunta na rawa ta karba tana fadin"Na menene ? " yace"in kin bude kya ga abunda ke ciki, sannan zaki san abunda yakamata kiyi dashi " yana gama fadin hakan yabar wajen tabi bayansa da kallo har ya bacewa ganinta kasancewar duhu ya fara kawo kai, bude ledar tayi kamshi ya daki hancinta, nan taci karo da ruwan Faro, lemon kwali sai kuma wani leda aciki wanda shike tashin kamshin, ciroshi tayi ta warware wani kunshin takarda dake cikinsa, hasken motar ya taimaka mata wajen ganin abunda ke ciki, gurasa ce aka yayyanka kanana kanana tare da gasasshiyar kaza, shima din kanana kananan aka yayyanka sai aka gaurayesu, cabeji, tumatir da kuma albasa akai kwalliya dasu asama, sosai take hadiyar yawu don ba karamin yunwa take ji ba, amma bazata iya ci ba tare da Man dinta ba hakan yasa da sauri ta mayar ta ajje, samun kanta tayi da sauke ajiyar zuciya ta furta afili" Allah kadai yasani watakila babu alheri ne awuraren da muke ta zuwa shiyasa Man bayason in bishi, to Allah yasa hakan shine mafi alheri "
Sulaiman na shiga ciki kai tsaye wajen reception ya nufa ya gaya musu sunan wanda yake nima, su kuma suka duba record book din sannan suka gaya masa ward da kuma room number, yana zuwa ya sami Likita aciki yana duddubashi amma babu kowa dake jinyarsa, shi kadai ne sai Likitan, yana ganin Sulaiman d'in ya kakalo dariyar dole Zuciyarsa cike da fargaban kar dai ace sun samu labarin halin da d'iyar tasa take ciki ne har yayi sanadin kwanciyarsa agadon asibiti, shi kuma gogan tunda ya samu kujera ya zauna ya kafe Dr.Ganan da ido da har yasa ya kasa samun sukuni, bayan Fitar likitan Sulaiman yace"Sannu ashe baka da lafiya bamu sani ba, daga gidanka nake ake gayamun shine nace bari in biyo in duba jikin naka " washe haqora yayi yace"ehya Allah sarki ai ka kyauta kuma jikin da sauki sosai nagode "Nayi zaton zan samu me dakinka anan kodai ita din tana gida ne ?" Dr.Gana yace"yanzun nan suka tafi ita da Banan, Allah ne dai be kaddara zaku hadu awaje ba, Nikam yaushe zaka koma bakin aikinka ne naga kadan jima agarin ? " iska yaja ya fesar tukun kan yace"gobe insha Allah zamu tafi ..... " Tare da Sumaiyya ??" Sosai abun ya shayar da Sulaiman mamaki da wannan tambaya ta uncle din nasa amma ta wani bangaren bai kamata yayi mamakin ba, ganin irin kallon tuhumar da yake watsa masa ne yasa jikinsa sanyi sosai, Allah ya sani wallahi subutar baki ne yayi...."meyasa kake tambaya ko da Sumaiyya za'a ? kaima kasan wannan dole ne don yana da kyau ta zauna kusa dani domin insa ido sosai akanta " kai Dr.Gana ya shiga girgizawa yana fadin"eh eh kam hakane kayi tinani me zurfi anan " tashiwa yayi daga inda yake zaune rike da wayarsa ahannu yana danne danne har ya isa gabansa, mika masa wayar yayi yana fadin"uncle please watch this..." hannunsa na rawa ya karba ya fara kallon vidiyon, Zufa ne kawai ya fara keto masa kota ina...."Uncle akunna maka fan ne naga sai Zufa kake ? " daqyar ya dago kai suka hada kwayar ido yace cikin karyewar murya "a'a ka barshi kawai " ya fadi hakan yafi akirga ba tare dayasan yayi ba, har karshe ya kalli vidiyon yana salati, Sulaiman ya warce wayar ahannu yana binsa da wani irin kallon tsana kan yace"kana son mu tattauna akan abunda ka kalla ayanzu kuma anan ne ko kuwa in bari sai ka murmure dakyau ?"...."muyi maganar yanzu " ya furta zuciyarsa na bugawa sosai sai mamakin ta yadda akai Sulaiman ya samu leakage din vidiyon kawai yakeyi.....

YOU ARE READING
MUTUNCIN 'YA MACE
Action"Sumaiyya ki sani wallahi sai an buga sabon kafce! Koda ni Muntasir zanyi yawo tsirara acikin duniyan nan ne saina tabbata na lalata miki rayuwa ta yadda nan gaba bazaki moru ba ko agidan aurenki!." Muntasir na tsaneka!na tsani duk wanda ya sanka! n...