7

36 1 1
                                    

I think you'd like this story: "MUTUNCIN 'YA MACE" by HAFNANCY01 on Wattpad https://www.wattpad.com/story/278469404?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_reading&wp_page=reading_part_end&wp_uname=HAFNANCY01&wp_originator=iz8CPN6PS5iBijnWCnJyZeR3xCDalw%2FS2dLvdKXzlX%2BoD4ooL404KjXP4OYtWm%2FIlDMCC7FZ5XYl3bXt017qr22oAhCdPbtZGRPGRH60DM92lS1VLMyAmRiFnRyGgHlQ

*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
           _{Babban jarabawa agareta..}_

     
            *NA*

   _Hafsat Hafnan_

                *DA*
   
        _Zainab Chubaɗo_

*Labarin dake ɗaukeda Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fuzgar zuciya❤*

       *07*

_______📖✍️"Agaskiya ba karamin rauni ka samu ba, amma menene yayi sanadin wannan rauni naka ?" Likita yayi tambaya cike da alhini, da wutsiyar dayan idon dake da sauran lafiya yake kallon Likitan akarkace yace"ahmm...ahmmm dama dama ni da wannan abokin nawa mun saba wasannin banza irinta abokai, to muna zaune adaki mun gama buga game na wasan k'wallon kafa a TV, sai akayi rashin sa'a nina lashe wasan hakan yasa na mik'e ina zagaye dakin ina masa dariya tare da k'iransa looser, to kasan irin wannan abu babu dad'i sai a k'ara tunzuraka, hakan yasa bai san lokacin da zuciya ta d'ebeshi ya dauki wuk'ar da muka gama yanka lemu ya harbeni da ita, shine ya sameni a idon " Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" shine abunda Likitan ya furta fuskarsa na bayyana tashin hankali, Lukman kuma kusan suman zaune yayi, baki bud'e, Fuska kuma shimfid'e da mamak'i karara, Lallai Muntasir yayi nisa a iya shirya makirci, wato domin ya kare kansa shine shi ya dora masa laifin ? gaskiya bai k'yauta masa ba, yanzu in aka sako hukuma acikin wannan al'amarin fa ? tabbas shi zai kwan ciki "amma meyasa zakayi haka ?, gaskiya ka rage zafin zuciya kar watarana tasa ka aikata abunda za kayi kukan dana sani wanda ya zarce na wannan al'amarin, yanzu gashi ka janyo masa matsala babba domin kuwa wuk'ar ta d'an yage madubin k'wayar idon nasa (cornea black)..."

atsananin firgice Muntasir ya fashe da kuka yana daga murya wanda ya janyo hankulan sauran ma'aikatan dake kan duty, fad'i yake"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un na shiga uku na gama yawo, Sumaiyya kin..." da sauri Lukman yakai hannu ya toshe masa baki ganin yana neman sakin layi yace"kai ka natsu ka dawo hayyacinka..." Da rawar murya ya maida kallonsa ga likitan yace"to to li...li...likita yanzu menene abunyi ? me zaka iya yimun in warke ? dan girman Allah ka taimakamun bana son na samu wani nakasu.."...kuka yaci k'arfinsa, cike da tausayinsa likita yace"zamu doraka akan wasu magunguna da kuma abinciccikan dake dauke da sinadarin rukunin bitamin 'A' har na tsawon sati biyu, muna fatar Allah yasa adace ka samu lafiya, amma in har babu wani improvement to lallai sai an maka dashen wani madubin (eye lense) kuma agaskiya anan asibitin mu bama da kayan aikin nan sai can Abuja.."

Daga shi har Lukman d'in kuka suke sosai tamk'ar ransu zai fita, an samu an masa dressing, aka rufe ido dayan da bandage sannan aka bashi gado tare da masa karin ruwa, Suna nan sai ga uban gidansa Alhaji Namaru ya iso sakamakon kiran daya samu na gaggawa daga garesu, shima tambayar da yayi masa kenan yace" Muntasiru garin yaya haka ta faru ? " sai cewa yayi tsautsayi ce kawai, cike da tashin hankali ya sake cewa"to yanzu babu wanda ya sani ne acan gida ? " a'ah bana da bukatar kowa yasan halin da nake ciki don kar hankalinsu ya daga, mu dai jira zuwa nan da sati biyun mu ga yadda abun zai kasance."

   ******

A ƴan kwanakin nan wata irin ɗasawa ce a tsakanin Sulaiman da kuma Asmy  sosai take wani irin tattalinsa kamar ƙwai, don haka gabaɗayansu suka zage damtse wajen  nunawa junansu kulawa ta ɓangarori da dama tun bayan dawowarsu daga Bauchi basu wani sake samun isashshen lokaci tareda Muktar ba, sabida aikin dayasha kansu a ƴan kwanakin zaune yake a cikin haɗaɗɗen office ɗinshi me madaidaicin girma, Salman ne ya shigo hannunsa ɗauke da wasu takardu bayansa kuma wani babban mutum ne ma'abocin firfura a saman fatar kansa, miƙewa Sulaiman yay alamar nuna girmamawarsa a gareshi yace "Barka da zuwa Sir"  murmushi mutumin yayi wanda ya baiyana haƙoransa yace "Barka dai Sulaiman ya aiki da kuma hidima da jama'a?" cikeda girmamawa yace "Alhamdulillah sir"  Salman ne ya kalli dattijon yace "wannan shine Alhaji Abubakar Zarewa wanda ke wakiltar Alhaji Maliya a fanin kasuwanci kuma an turoshi wajenka ne daga babbar headquarter ɗinmu dake Abuja" faɗaɗa murmushinsa Sulaiman yayi yace "masha Allah" Alhaji Abubakar zarewa ya dubi Sulaiman yace "haƙiƙa mun yaba maka bida aiki tuƙurin dakayi bisa gaskiya da kuma Amana, wannan dalilin yasa mamallakin Companyn Maliya Enterprises ya buƙaci da inkawo maka wannan dakaina ba saƙo ba"  ya faɗi hakan tareda miƙa masa wata farar takarda dake ninke yace "congratulations ina tayaka murna samun ƙarin girma zuwa babban matakin dayafi wanda kake kai a yanzu"  karɓar takardan Sulaiman yayi cikin yanayi na rashin gaskata abinda kunnansa sukajiye masa  ya warware takardan ya fara karamtawa hamdala yayi ga Allah , amma sedai wani ɓangare na zuciyarsa sam  be masa daɗi ba dazebar garin kaduna kodan sabida Asm'u, yasan abune mawuyaci ta yarda tabishi cikin sauƙi wancan karon ma ba ƙaramar daga sukasha da itaba a ƙarshe tace ita bazata iyayin doguwar tafiya tabar iyayenta ba, Ajiyar zuciya ya sauke tareda sakin murmushi yace "masha Allah najin daɗin wannan kyakkyawan labarin   ubangiji kuma ya ƙara tabbatar mana da alkhairinsa" da amin suka amsa masa sannan Alhaji Abubakar Zarewa yay masa sallama tareda jaddada masa cewar lallai-lallai ya kimtse iyalansa dashi kansa suzo abuja akan lokacin don on monday insha Allahu zafara zuwa bakin aiki.  Cikeda girmamawa ya amsa da "insha Allah sir"  Suna fita ya miƙe da sauri zeje office ɗin muktar sukai karoda juna nan muktar yake nuna masa shima tasa takaddar ƙarin girman, murna sukayiwa juna sannan suka zauna suka fara tsara planing ɗin tafiyar tasu se yamma liƙis ya koma gida amma kuma bisaga mamakinsa Asma'u bata nan bedroom ɗinsu ya wuce tareda sassautama kansa neck tie ɗin dake wuyansa ya zaro wayarshi ƙirar Samsung yay dailing number Asma'u.  Tsaki yaja  tareda jefar da wayar bisa makeken gadon dake ɗakin sakamakon jin wayarta dayay a kashe.

MUTUNCIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now