*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
_{Babban jarabawa agareta..}_
*NA*_Hafsat Hafnan_
*DA*
_Zainab Chubad'o_*Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fuzgar zuciya❤*
wannan littafin Free ne bana kuɗi ba 🙅♀️
Advert 👇
*Yar uwa jarraba amfani Mg's herbal whitening black soap Kiga ikon Allah, domin jin tasirinsa ga fata ki duba ƙasan wannan page ɗin na tabbata zakiyi alfahari da hakn😊*
*13*
Not edited 🤷♀️
____✍️Wani irin zaro idanu Sumaiyya tayi lokaci guda kuma ta fashe da wani irin kuka tace "meyasa zaki kawo mutumin daya zama silar rushewar rayuwata gidan mu khadeeja? Shin kin manta da cewar shine mutumin daya jefani a cikin wannan halinda na samu kaina a ciki?" durƙushewa tayi a gurin ta saki wani irin kuka me karya zuciyar duk wani me sauraronta, sosai jikin khadeeja yay wani irin sanyi durƙusawa tayi tareda ɗagota tace " don Allah Sumaiyya kiyi haƙuri amma meyasa bazaki saurareshi ba? Zuwa yanzu fa wllh Dr. Gana yayi nadamar abinda ya aikata miki kuma wllh inada yaƙinin cewar yana gabda ya nemi yafiyarki" "yafiyar me kuma ze Roƙeni bayan shine mutumin daya fara farautar Mutuncina? Wllh Khadeejah a halin yanzu na gama tsanarsa kuma banajin cewar zan iya yafe masa sabida duk wani bala'i dana shiga har zuwa kan ƙazantar data gifta tsakanina da ɗan uwana wanda muke Uba ɗaya duk shine silah, don haka idan ma kece kikai masa rakiya a radin kanki to ki gaggauta zuwa ki gaya masa cewar Sumaiyya Muktar Azare sam bata buƙatar Nadamarsa kokaɗan!!" "Amma sumaiyya ya kamata kibashi dama wata ƙila alkhairi hkan ze zame miki a sanadin zuwan nasa" ɗagowa tayi tana kallonta still hawaye na zuba a saman kyakkyawar Fuskarta datai wani irin rama tace "Alƙhairi dai? Ai sam babu Wani alkhairi a tattare da wannan mutumin, don haka kije ki gaya masa ya gaggauta barin ƙofar gidan mu idan har yanason ganina a doran ƙasa baso yake ya kasheni b....." wani irin kuka ne ya sake taso mata amma kuma ta danne tareda kallon khadeeja tace "a halin yanzu da kinsan irin haɗarin da zuwansa ke shirin haifarwa a rayuwata wllh khadeeja da baki kawoshi ba, a yanzu haka fa Babana nemansa yake Ruwa a jallo danya Aura min shi, idan har hakan ta faru inada yaƙinin rayuwata tazo ƙarshe khadeeja" zaro idanu khady tayi tana kallonta cikeda kaɗuwa tace "inanillahiwa'inna'ilaihirraji'un, wannan wace irin masifa ce? Kinga ki kwantar da hankalinki sumaiyya indai Dr. Gana zuwansa matsala ne a gareki to ki ƙaddara babu abinda ze faru se alkhairi, dama nida Kazim ne muka Ƙaraso nan amma shi Dr.G yana can bakin babban masallaci acan yay faking motarsa barinje insa Kazim yasashi yay gaba tun kafin komai ya kwaɓe mana" da sauri Khadeejah ta koma jikin motar, tunda ta nufo motar yake kallonta kamar ze cinyeta sabida so lumshe manyan idanunsa yay yace "babe ya akai naga ƙawar tamu se kuka take hope dai lfy" jan fasali khadeeja tayi tace "inafa lfy Babe wllh matsala ce ke dabda tasowa akan zuwan Dr.Gana" "matsala kuma babe ? To matsalar me? " Kazim ya jera mata tambayoyin duk alokaci guda, langaɓarda kai Khadeejah tayi tace "yanzu dai ka fara zuwa ka sallami wancan mutumin tukunna ni kuma zan maka bayani idan zamu koma gida" ɗaga girarsa yay tareda faɗin "ok" key yaywa motar tareda janta baya ya juya sannan yabar gurin ya ɗauki hanyar babban Masallacin juma'a.Juyawa khadeeja tayi zuwa inda Sumaiyya ke durƙushe tana sharar ƙwalla zatayi magana keman Emran ya ƙaraso gurin yace " Yaya Sumaiyya Mama tace wai ku shigo ciki" Kama hannunta khadeejah tayi suka nufi cikin Gidan, babu kowa a tsakar gidan hakan yasa Direct suka nufi part ɗinsu sumaiyyar still hannunta na cikin na Khadeejah muryar Beebah sukaji ta window ɗakinsu tana faɗin "lallai Sumaiyya Rayuwa bata zamar miki aya abin kuma harda kwaso ƙwaye jami'ar har gida?" batako kalleta ba taja hannun khadeeja sukai cikin falon mama da sauri, a khitchine taji mama dan haka ta isa gurin ta sameta dakatawa Mama tayi da dama furar datakeyi ta kalƙi Sumayya cikin yanayi na damuwa tace "kuka kika kumayi ko Sumaiyya? Har so nawa zan gaya miki cewar yawan zubar da hawaye baya taɓa canza abinda ƙaddara tazowa mutum dashi?" Sunkuyar da kanta Tayi ƙasa cikin sanyinta tace "kiyi haƙuri Mama bazan sakeyin kukan ba insha Allah" murmushi mama tayi sannan tace "Allah yay miki Albarka maza ki ɗauki furar nan kikai babban Falon Baba shaik yayi baƙi" da sauri ta ɗago fararen idanunta waƴanda suka sauya launi sabida kukan datayi tana kallon mama, ɗaga mata kai nama tayi tace "ki hanzarta kikai inyaso idan kin dawo sekisha Magani ki kwanta" ɗaga mata kai kawai tayi tareda ɗakko jug me tsafta ta juye furar ta ɗora a babban trey da cups masu ɗan girma kaɗan ta fito falon, murmushi tayiwa khadeejah tace "ina zuwa pls" sannan ta fita ba tareda ta damu da yanayin da fuskarta ke ciki ba, a hankali take takawa cikin dogon hijjabita me launin kalar blue black wanda ya fito da hasken fuskarta sosai, a bakin ƙofar babban falon ta tsaya taredayin sallama kanta a ƙasa ta shiga ba tareda ta ɗago ba don harga Allah bazata iya jurar kallon idon mahaifinta dake cikeda tsanarta ba.
YOU ARE READING
MUTUNCIN 'YA MACE
Action"Sumaiyya ki sani wallahi sai an buga sabon kafce! Koda ni Muntasir zanyi yawo tsirara acikin duniyan nan ne saina tabbata na lalata miki rayuwa ta yadda nan gaba bazaki moru ba ko agidan aurenki!." Muntasir na tsaneka!na tsani duk wanda ya sanka! n...