19

36 1 1
                                    

*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
           _{Babban jarabawa agareta..}_

     
            *NA*

   _Hafsat Hafnan_

                *DA*
   
        _Zainab Chubad'o_

*Labarin daya ƙunshi Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fuzgar zuciya❤*

     

        *19*
Banyi Editing ba🙅‍♀️

_____✍️A nitse take kallonsa da mamaki kwance a saman fuskarta kamar yanda shima Dr.Gana ɗin ke kallonta, zuciyarsa ce ta shiga bugawa da mugun ƙarfi lokaci Guda kuma ya fara addu'a a ransa cewar "ya Allah kasa mafarki nake bada gaske bane abinda idanuna suke ganemin ba" murmushi Sulaiman yayi tareda katse mishi zancen zucin  dayakeyi a ransa yace "uncle kodai kunsan junane da Surukar taka?" 

da fari soyay ya daburce amma dayake mutum neshi me basira seyay murmushi tareda ɗauke kansa daga barin kallon Sumaiyya yace "Ae nasanta tana Ɗaya daga cikin jerin ɗaliban da muka yaye na wanan shekarar."  ɗan jim yayi  sakeyi Kaɗan  a ransa yanajin wani irin ƙunci  da takaicin rasa sumaiyya na cika Duk wani gurɓi Dake zuciyarsa, lumshe idanunsa yayi kaɗan tareda buɗesu akan Sulaiman yace "ina tayaka murna Son, Amma babu shakka kayi dacen mata irin wadda kowa ke fatan samu babban abun burgewar ma shine daga gidan Mutunci ta fito"  duk wannan uban zancen da Dr. Gana yake zubawa daurewa kawai yakeyi amma a zahiri ji yake tamkar ya fasa ihu idan ya tuna cewar ya rasa Sumaiyyah har Abadah, miƙewa tayi idanunta akan Sulaiman tace "barin shiga ciki seka shigo" daga haka tai waje abinta duk takaicin ganin Dr. Gana ya cika mata zuciya, tana  shiga taga Falo babu kowa a ciki dama batai tsammanin ganinta ba ta nufi ɗakinta Ranta a ɗan ɓace, dogon  hijab ɗin dake jikinta ta cire sannan ta shiga toilet ta sake ɗauro Alwala tazo ta haye gado abinta, addu'ar bacci tayi ta shafe jikinta Dashi tareda jan lallausan bargon dake kan gadon ta rufa har kanta, a hankali abubuwan da suka faru ɗazu suka fara ɗawo mata a rai musamman kissing ɗin Sulaiman datayi,  miƙewa tayi zaune da sauri kamar wadda aka tsikara tareda rufe fuskarta da zara-zaran hannayenta tana wani rintse idanu sabida kunyar data cika ta, sosai abin ya mugun tsaya mata rai harta kai ɗuk lokacin data rintse idanunta ji take tamkar lips ɗin Sulaiman ɗin suna cikin nata

Lumshe idanunta tayi kamar wadda ke bacci amma kuma a zahiri sam ba hakan bane, alamar tafiya Ta faraji daga siririn coridor ɗin daya raba ɗakinta da falon hakan yasa taƙarayin lamo a cikin lallausan bargon zuciyarta na bugawa kaɗan-kaɗan, murɗa handle ɗin ƙofar yayi ya shigo bakinsa ɗauke da Sallama, harɗe hannayensa yayi a ƙirjinsa yana me ƙarewa yanayin fasalin ɗakin kallo Daga inda yake a tsaye a hankali ya fara takawa har zuwa jikin haɗaɗiyan drowern bangon dake ɗakin ya buɗe, da fari  tsayawa yayi yana bin kayan cikin Drower ɗin da kallo Komai tsaf-tsaf a jere gwanin shi'awa har idanunsa suka sauka akan wasu tausasan milk ɗin pjmas na bacci Masu shegen kyau, zarowa yayi tareda ajiyesu daga gefan gadon datake kwance sannan ya shiga toilet in less than 5minutes ya fito ƙugunsa ɗaure da wani ƙaramin towel wanda ko idan sawun ƙafarsa be kai ba sabida tsahonsa, ƙaramin towel ɗin dake hannunsa yasa ya fara goge lallausar sumar dake kansa wadda keta faman ɗigar da ruwa,  a hankali ruwan dake ɗigowa daga cikin sumar kansa ke sakkowa ta dokin wuyansa har zuwa faffaɗan ƙirjinsa wanda ke ɗauke da wani kwantaccen gashi lub-lub dashi, duk abinda yake Sumaiyya na kallonsa ta wutsiyar idanunta dake lumshe banda bugawa babu abinda zuciyarta keyi, amma kuma a zahiri sam takasa hana kanta kallonsa sabida tsarin halita da cikar zatin da ubangiji yayi masa, a iya rayuwarta Zata iya cewa bata taɓa ganin mutum irin Sulaiman ba indai a fagen kyawun fuska dana Ƙirar jiki ne itakam  tafi danganta hakan a mafarki kokuma cikin duniyar hasashenta,amma kuma abin mamaki se gashi yau taci karoda da irin wannan  mutumin ma'abocin kyau da kuma kwarjini  a hakan kuma wai mijinta ne,  wata nannauyar Ajiyar zuciya ta saki wadda sam batai tsammanin zuwanta ba  hakanne yaja hankalin Sulaiman dake ƙoƙarin saka riga zuwaga fuskarta, ƙirjinta ne ya wani irin buga Dum  ba shiri ta juya fuskarta zuwaga ɗaya gefan tana miƙa kamar me baccin gaske, murmushinsa mekyau yayi wanda hakan yay dedai da  kammala sanya kayan nasa a jikinsa, gaban dreesing  mirror ɗinta yaje ya tsaya tareda ɗaukan wani sassanyan turare Me sanyin ƙamshi ya fesa a jikinsa ya nufi gadon sabida wata irin gajiya dataiwa gaɓɓansa yawa, gabaɗaya Sumaiyya tayi tsammanin gefanta zeje ya kwanta amma kuma me setaji mutum dabda gadon bayanta ma'ana jikinsa na gugar nata, zaro idanu tayi sabida tsabar kaɗuwa inda Allah ya temaketa ma ba ɓangarensa take kallo ba wata ƙila daya fahimci ba baccin  take ba, kamar daga sama taji ya jawota jikinsa ya rungumeta tamkar wanda ya samu fillo a haka wani daddaɗan bacci yay awon gabadashi, a hankali takejin saukar numfashinsa a gadon bayanta wanda hakan ya samu nasarar saukar mata da wata irin kasalla da mutuwar jiki, a hankali cikin dabara ta zame jikinta daga nashi ta matsa can nesa dashi tana aikin sauke numfashi ba zato balle tsammani taji ya kuma jawota zuwa jikinsa fuskarta na facing nashi fuskan,  zaro idanu tayi tana kallon fuskarsa jin yaƙi sakinta ne yasa tai lamo a jikinsa har itama baccin ya samu nasarar ɗaukarta.

MUTUNCIN 'YA MACEOnde histórias criam vida. Descubra agora