I think you'd like this story: "MUTUNCIN 'YA MACE" by HAFNANCY01 on Wattpad https://www.wattpad.com/story/278469404?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_reading&wp_page=reading_part_end&wp_uname=HAFNANCY01&wp_originator=iz8CPN6PS5iBijnWCnJyZeR3xCDalw%2FS2dLvdKXzlX%2BoD4ooL404KjXP4OYtWm%2FIlDMCC7FZ5XYl3bXt017qr22oAhCdPbtZGRPGRH60DM92lS1VLMyAmRiFnRyGgHlQ
*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
_{Babban jarabawa agareta..}_
*NA*_Hafsat Hafnan_
*DA*
_Zainab Chubaɗo_*Labarin dake ɗaukeda Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fuzgar zuciya❤*
*10*
"Mama me kike ci ne na baka na zuba ?, ki kwantar da hankalinki yanzu duk zan fiddaku cikin rud'ani kuma zan gaya muku ta yadda akayi kayan Sumaiyya suka shigo hannuna " ya furta yana sakin murmushin mugunta, Furzar da wani iska mai zafi yayi sannan ya dire kallonsa akan fuskar Sumaiyya da tashin hankali ma ya hanata motsa koda 'yar yatsarta ne, yace"Aranar ashirin da bakwai ga watan Yuli sanda na raka uban gidana kwaso kayayyaki acikin garin Bauchi sai dare yayi mana, hakan yasa muka tafi Villa hotel da misalin taran dare domin kwana, Wani abun mamaki sai nayi kicibus da kanwata Sumaiyya tana fitowa daga wani daki ayayin da wani gardin yabiyo bayanta daga shi sai gajeren wando da singlet ya jawota ta dawo da baya " dauke kallonsa yayi daga gareta ya koma duban sauran mutanen dake katafaren falon da kallo daya bayan daya yana fadin"yanzu wannan labarin dana bayar wani irin fassara ne mai sauraro zaiyi mata ? " yo! karuwanci taje yi mana in ba haka ba menene zai kai yarinya budurwa otel ita ba aure ba in banda karuwancin ? " Mamansu Muntasir ta furta Zuciyarta cike da farin ciki da wannan al'amarin.
"Tabbas ni kaina da kuma mijina shaida ne don awannan ranar shashantar damu tayi akan cewa ta manta da littafinta awurin kawarta kuma suna da test awashegari don haka zata je ta karbo, Ni kuma kuskurena daya dana bata izinin fita ba tare da sanin Abban Adil ba, koda ya dawo fada ya dungayi yace don me zan bari ta fita acikin wannan daren bada izininsa ba ?, wallahi yayi fada sosai don ko kanwarsa ce ta uwa daya uba daya karshen gatan da zaiyi akanta kenan na nuna damuwa karara, ashe dai ba nan taje ba.." nan ta kwashe labarin yadda akai da Fu'ad da shima karetan da yayi, Muntasir shine hadda nuna musu Video clip d'in daya samo awurin wani ma'aikacin hotel d'in, amma saida ya biyashi kudi tukunna kafin ya samu wannan leakage d'in wanda cctv camera na hotel din ya kwasa, nan suka ga Shigar Sumaiyya cikin hotel din tana ta waige waige kamar mara gaskiya, amma anki nuna yadda tattaunawarsu ta kasance da Dr.Gana, Muntasir ya saka an yanke wurin, sai fitowarta kawai suka gani da kuma lokacin da shi Dr.Gana din ya biyo bayanta ya jawo hijabinta, sai Fuskar Muntasir din da ubangidansa Alh.Namaru da aka hasko, Shikenan! ,kowa sai sallalami yake yi yana tofa albarkacin bakinsa, yaya Asiya tace"wayyyyo Abun dariya wai kunkuru ya yi wa bushiya ƙafa, Baba me nake gani ne haka kaida Shalelenka yau sai gaku arana tsaka tana toyaku ?, d'iyar daka fifita akan sauran ya'yanka, d'iyar da kafi alfahari da samun irinta, d'iyar da aka tsaya kan tsayin daka na ganin ta samu gurbin karatu, kai magana ma in zaayi maka ita in ba zancen Sumaiyya bane tofa bazaka baiwa wannan zancen muhimmanci ba, yau gashi ta kwab'e muku, mun ganku arana yana toya tsakiyar kanku, ayau Sumaiyya ta kwaso maka degree d'in karuwanci, Allah ma yasa dai babu rabon juna biyu..." haka sauran ya'yan ma sukayita yi dashi, Maman shalele kuwa kasa magana tayi, Maman muntasir ta dubeta tace"hehehe Badi'atou yau ba bakin magana ne ?, duk da cewa nasan ke d'in ba mai fiya magana bace amma yana dakyau kidan tofa albarkacin bakinki aciki..." kai tsaye Mama tace"tambayata ga Muntasir shine acikin wannan bidiyon daya nuna mana meyasa ba'a nuna abunda ya gudana tsakanin Sumaiyyar dashi abokin ma'ashar nata ba ?, ai ya kamata mu gani " Anty Asiya tace"an gaya miki 'yan hotel sukan nuna sirrin mutum ne ?, iyakacinsu wannan dai da kika gani, in kuwa har kika ga an nuna miki cikin dakin tofa sai in ya kasance ana zargin wanda ya kama hayar wannan dakin da aikata wani mugun abun ne..."da sauri Muntasir yace"Yauwa gaya mata dai..."
YOU ARE READING
MUTUNCIN 'YA MACE
Action"Sumaiyya ki sani wallahi sai an buga sabon kafce! Koda ni Muntasir zanyi yawo tsirara acikin duniyan nan ne saina tabbata na lalata miki rayuwa ta yadda nan gaba bazaki moru ba ko agidan aurenki!." Muntasir na tsaneka!na tsani duk wanda ya sanka! n...