1

68 2 0
                                    

*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
           _{Babban jarabawa agareta..}_

     
            *NA*

   _Hafsat Hafnan_

                *DA*
   
        _Zainab Chubaɗo_

*_Da sunan Allah mai Rahama maijin ƙai, salati da ɗaukaka su tabbata ga manzon tsira Annabi Muhammad(s.a.w)  Ya ubangiji yanda muka fara Wannan rubutu lfy  Allah kasa mu saukeshi lfy_*
     
*_GARGAƊI bamu yarda wani ko wata su sarrafa mana wannan littafi ta kowace fuska ba tareda amincewar mu ba, wannan kasheɗin kan me uwa dawabi ne musamman ɓarayin Youtub_*

Not edited

        *01*

_____✍️A zaune take ta Rabka uban tagumi idanunta duk sun caɓe da Hawaye wanda ke zubowa bisa saman ƙunduguginta, tunanin halinda take ciki yake ƙara mata yawan zubar hawayen nata ba tareda ta iya dakatar dasu ba cikin yanayi na Rashin sanin madafa Asma'u ta miƙe cikin hanzari tana gyara zaman hijjabin dake jikinta, fita tayi zuwa farfajiyar madedaicin gidanta wanda ke ɗauke da tarin shuke-shuke na alfarma  bata tsaya a ko inaba se'a gaban ƙaramar Motar ta ƙirar Camry, a hankali ta buɗe motar ta shiga ta zauna sannan tayi mata key ta nufi Ƙofar fita daga Babbar Ƙofar Gidan.

Cikeda girmamawa mai-Gadin Ƙofar ya buɗewa Asma'u Ƙofar ta Fice daga Gidan cikin Hanzari  kamar zata tashi Sama, duk tsawon lokacin da Asma'u ta ɗauka a Motar tana tafiya har Lokacin bata dena kukan datake ba harta iso ƙofar Gidansu ta tsaida Motar , Sam bata damu da Hawayen dake zubowa daga saman ƙunduguginta ba a haka ta fito daga motar ta shiga wani Ƙaramin Gida dako ƙofar kirki babu sai Labulan Buhu,   Babu kowa a Tsakar Gidan se  Wata dattijuwar Mata wadda bazata wuce shekaru Sittin a duniya ba  daga ɗan nesa da Dattijuwar kuma wata matace itama wadda bazata Wuce Shekaru Arba'in ba,  Dattijuwar dake Zaune bisa Tabarmar Kaba tana shafa magani a saman ƙafarta wadda ta kumbura Alamar ciwo ta ɗago kai tana kallon Asma'u baki a sake tace " Yau naga tsigalalliyar yarinya babu sallama zaki shigowa mutame gida ki tsaya kinai mana kuka sabida janyowa kai Masifa Asma'u?  To wllhi Aniyarki saidai ta biki, mudai bazamuga kuka ba duniya da lahira kinji na gaya miki. can kuma saita fashe da kuka tana maida kallonta ga wannam matar dake can nesa da ita tana gyara itacen dake cikin Murhu tace "yanzu Talatu kullum Haka Asma'u zata dinga shigo mana gida babu sallama sedai kuka? Dama irin tarbiyar da kukai mata kenan keda Haruna Talatu?

Talatu wadda ke shirin Fara tankaɗan Garin tuwon dake gabanta ta tsaya tana Kallon Gwaggo wadda keta faman matsar ido baki buɗe tace "Wace Asma'un kike nufi Gwaggo?.  Ta faɗi hakan tana fitowa da hanzari daga ɗakin girkin hannunta ɗauke da Rariyar tankaɗen Garin

Asma'u na ganin Innarta ta nufota da gudu ta Rugumeta tana mai Ƙara sautin kukanta tace "Inna Don girman Allah ki taimaka min karna faɗa ga halaka Inna, wallahi idan har ba'a Raba Aurena da Sulaiman ba zaisa nakai kaina wutar jahannama da ƙafata Inna!!  Don girman Allah kusa ya aikomin da takardar Saki na Roƙeku.   Gabakiɗayansu salati suka saka daga Inna har Gwaggo wadda tai mitsi-mitsi da ido tana shirin fara bala'i cikeda masifa Inna ta hankaɗe Asma'u daga jikinta tace "Asma'u Ashe bakida hankali ban saniba?  Auren naki kikeso ki kashe sabida wani banzan dalilinki marar amfani?  To wllh ki sani muddin kika kaso wannan Auren  wallahi bada yawuna b...."Nima kaina bada yawuna ba kuma wallahi a sanadin hakan saina tsine miki!!  Malam Madu Mahaifin Asma'u dake ƙoƙarin shigowa tsakar gidan ya katse Talatu ta hanyar faɗar hakan cikin ɓacin rai da kumfar baki,  duk yanda Asma'u taso ta fahimtar da iyayenta akan matsalarta da mijinta sulaiman sam sukaƙi bata damar hakan dan dole ta haƙura,  haka iyayen nata da kakarta Gwaggo suka dinga surfa mata masifa duk dan abinda Sulaiman ɗin yake aiko musu dashi na yau da gobe.

Jikin Asma'u a mace ta fito daga gidan tana ƙara sautin kukanta a haka ta shiga motarta ta koma gida cikeda Rashin sanin makama akan matsalar tata,  idan har zata iya tunawa dai-dai yau watan Sulaiman  Goma cif da tafiya kwatano batareda ya dawo gida ya duba lafiyarta ba, ko babu komai ai yasan akwai haƙƙinta da addini ya ɗora masa a wuyanta taya yake tunanin zata iya rayuwa a hakan bayan itama lafiyayyiya ce kamar ko wacce mace, tabbas ya zama wajibi a gareta ta samawa kanta mafita don bazata iya zama a cikin wannan masifar datake ciki ba a gidan Sulaiman.

MUTUNCIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now