17

27 2 2
                                    

*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
           _{Babban jarabawa agareta..}_

     
            *NA*

   _Hafsat Hafnan_

                *DA*
   
        _Zainab Chubad'o_

*Labarin daya ƙunshi Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fuzgar zuciya❤*

     

        *17*

_____✍️Firgigit Sumaiyya tayi ta farka daga nannauyan baccin daya ɗauketa, wata irin wahalalliyar zufa ce take keto mata tamkar wadda aka watsawa ruwa  manyan fararen idanunta ta ɗaga ƙirjinta na bugawa ta  sauka su saman makeken agogon bangon dake ɗakin, a hankali ta ringa jiyo hayaniyarsu Yaya Basirah dake hira a Falo   yafendu Faridah ce ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da wani madedaicin kofi wanda ke ɗauke da fresh madaran shanu tana kallon Sumaiyya wadda ta kafeta da itanu tana kallonta tun shigowarta  tace "Harkin farka kenan ?"  ta faɗa a lokacin datake ajiye mata kofin daga gefanta  tareda ɓallo Pcm ɗin dake hannunta ta miƙawa Sumaiyyar,  kallonta kawai Sumaiyya keyi amma sam ta kasa motsa bakinta datakejin yay mata wani irin Nauyi, daƙyar ta iya buɗe bakinta tace "Yafendu nan inane pls?"   kafeta da ido Yandu Faridah tayi  kamar meson gano wani abu a tareda Sumaiyyar can kuma setai murmushi tace "Gidan Sumaiyya Muktar Azare ne"  se'a lokacin Sumaiyyah ta fahimci halinda take ciki, Babu shakka mafarki tayi kenan aɗan ƙanƙanin lokacin data samu tana bacci..." ki tashi kiyi wankan ki shirya kozaki ɗanji daɗin jikinki tunkafin iyayen mujin naki su shigo ciki" gaban sumaiyya ne yay wani irin bugawa a zahiri kuma seta kalli Yafendun nata cikeda Tsoro  bakinta na rawa tace "Au dama..uhm da...dama ba....ba...." kinga Sumaiyya miƙe kawai ki shiga wanka ki fito  banson wani shirme tun ɗazu shaik ke kiran waya donyaji ya ciwon kan naki amma nace masa kina bacci" Miƙewa tayi tareda sakko da santala-santalan ƙafafunta waƴanda ke ɗauke da zara-zaran yatsu masu kyau, a hankali take takawa tamkar kazar da ƙwai ya fashe mata a ciki ƙirjinta na tsananta bugu harta shiga toilet ɗin dake ɗakin,  tsayawa tayi cak tanabin ko wani lungu da saƙo da kallo Sosai ta yaba da tsayin toilet ɗin musamman daya kasance komai fari ne,  kayan jikinta ta fara ragewa  sannan ta matsa dabda bahon wankan da aka cika da ruwa se baza ƙanshi yakeyi,  bra ɗin jikinta ta cire har zuwa kan panty ɗinta sannan ta shiga cikin ruwan ta zauna tareda lumshe manyan idanunta sabida yanda zafin ruwan ke ratsa duk wata gaɓa ta jikinta,  watsa ruwan da Yafendun nata ta haɗa mata  ta farayi zuwa kan fuskarta nan da nan wani irin ƙamshi me tsayawa a  rai ya gama gauraye toilet ɗin,  mafarkin datai ne ya fara dwo mata a cikik kwanyar kanta nan take wasu zafafan hawaye suka shiga zubo mata tamkar bazasu tsaya ba, abu daya ne yafi komai tsaya mata a rai shine   kalmar "Karuwar" da tsohuwar data gani a mafarkinta ta kirata da ita, wannan kalmar ita kaɗaice  kawai take mata yawo a tsakiyar ƙwaƙwalwar kanta. Wata nannauyar Ajiyar zuciya ta sauke tareda yin Hamdala ga Ubangijinta a zuciyarta dayasa hakan ta kasance mata a iya mafarki ne kawai.

Ƙwanƙwasa ƙofar toilet ɗin akai hakan yasa ta miƙe da hanzari tareda ɗaukar wani babban Farin towel ta  ɗaura sannan ta fito bayan ta watsa kayan data cire a washing machine, wani irin bugawa ƙirjinta keyi a duk lokacin data tuna mummunan mafarkin datayi ɗazu  a bakin gadon ta samu Yafendu Farida zaune  da alama jiran fitowarta takeyi,  wata haɗaɗɗiyir Lufaya Maroon ta gani daga gefanta yafendun nata se kuma wata milk ɗin  doguwar riga me kamada Alkabba wadda taji ubn ado a jikinta, janyota yafendun tayi cikin mintunan da bazasu gaza biyu ba ta gam shafe Sumaiyya da wata sihirtacciyar humra me bala'in ƙamshi irinta Asalin kanuri ba jabun ba, kafin kace me tuni ɗakin yaɗau ƙamshi tamkar anyi ɓarin turare wata streat gown ta nika mata tasa bayan ta gama sanya bra da panty ɗinta waƴanda sukabi lallausar farar fatarta wadda keta glowing tana walwalin gyara, a lokacin da Sumaiyya ta sanya wannan riga Ita kanta Yafendu Faridah sedatai tasbihi zuwaga ubangijin daya ƙagi  wannan  kyakkyawar surar ta Sumaiyya, abu ɗaya kawai zata iya cewa shine lallai Sulaiman yayi babban dace da samun wannan halittar a matsayin kyauta ga ubangijinsa  sedai lokaci ɗaya zuciyarta taimata rauni a lokacin datake ɗaurawa Sumaiyyah lufayar a saman rigar, hakanan duk yanda taso ta danne hawayen dake shirin zubowa daga idanunta sam seta kasa dole yasa ta barsu suka zubo wanda hakan yay dedai da kammala mata ɗaura lifayar datayi, Yaya Asiya ce ta shigo ɗakin se wani ɗaure fuska take alamar baƙinciki ƙarara ta dubi Yafendu faridah tace "yakamata kibarta haka ta fito indai ba fatar jikinta zaki sauya mata ba, wahalace ma da bata ƙare ɗan Adam idan ba haka ba wani shiri zaki tsaya kinawa yarinyar data gama watsar da mutuncin na ƴa mace a waje?"  gaban Sumaiyya ne ya buga dam amma kuma seta daure a zuciyarta kuwa karanta duk addu'ar datazo mata baki kawai take, roƙonta ga Allah a yanzu be wuce guda ɗaya ba shine ya tsareta daga jin kunyar Surukan nata don gudun karsuji abinda yayyenta mata suke faɗi akanta kodan gudun abinda ze taɓa ƙimar mahaifinta da ita kanta.

MUTUNCIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now