30

76 2 1
                                    

*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
           _{Babban jarabawa agareta..}_

     
            *NA*

   _Hafsat Hafnan_

                *DA*
   
        _Zainab Chubad'o_

*Labarin daya ƙunshi Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fuzgar zuciya❤*

      The final chapter

        *30*
🔚🔚🔚🔚🔚🔚

_____✍️"Malam kada kaimin haka Don girman Allah katuna da irin girman alƙawarin dake tsakaninmu nidakai!!"  girgiza mata kai kawai Shaik keyi idanunsa sunyi wani irin ja sabida damuwa sannan yay wani gajeran murmushi yace "Haƙiƙa ubangijn mu sarkin Rahama ne da kuma jinƙai Maryamu, shiyasa yaywa annabin mu umarnin akan ya horar damu akan Rufawa junan mu Asiri babu shakka faɗin ma'aikin Allah ne cewar duk wanda ya rufa Asirin wani to ubangiji ze rufa nasa Asirin Duniya da lahira, Allah shine mafi sani akan niyata bawai zan faɗa bane danna keta alfarmaki ba a'a  zan faɗa ne kawai donna tsaftace iyalina tinkafin Ajali ya riskeni don gudun Ruɗani a tsakanin ƴaƴana.!!"  Baba shaik ya faɗi hakan yana kallon tsakiyar idanun Umman Beebah wadda ke wani irin kuka sabida tashin hankali"

Gabaɗaya falon kallon shaik suke ciki kuwa harda Muntasir wanda gabansa ke wani irin bugawa sabida fargabar abinda Baban zece, Yaya Asiya kuwa gabaɗaya tama kasa yin kukan sabida tsabar baƙin cikin datake ciki hakama Yaya Basirah wadda ta gama sandarewa a zaune.

Wani gajeran Murmushin Baba shaik yayi ya kalli mutanan dake falon yace, " A wata ranar Alhamis wadda tai dedai da Shekarar 1987 ciki dare nida Maryamu  muna zaune muna ɗan taɓa hira, a ƙa'idata idan na dawo daga aiki na nakanje masallaci nayi wa'azi a lokacin ina kan ganiyata ta samun kuɗi, tun farkona ban laru da cewar se wani ya ɗauki nerarsa ya bani ba sannan zanci abinci a'a ni mutumne me zafin nema duk da cewar ina aikin gwamnati kuma a lokacin ni Babba ne a jerin gwanon waƴanda ake mugunji dasu a cikin jihar bauchi, a wannan ranar na dawo gida a matiƙar gajiye ne amma dukda hakan bayan nayi wanka sena zauna muka ɗan taɓa hira da Maryamu lokacin bata daɗe da yaye Basirah ba, to'a wannan ranar ne ƴan fashi sukai mana dirar mikiya bayan sun ƙwace kuɗaɗen dana dawo dasu shine shugabansu yayiwa Maryamu Fyaɗe!! A wannan daren munyi kukan baƙinciki nida ita kamar bazamu dena ba, sedai kokaɗan hakan besa na gujeta ba haka kuma nayi mata alƙawarin cewar zan ɓoye mata sirrinta fatana kawai shine tayi haƙuri Mukarɓi Ƙaddarar da Allah ya jefo na.

Bayan gajeran lokaci da faruwar hakan ne Maryamu ta fahimci ciki ya shigeta a dalilin mu'amalar da shugaban ƴan fashin yayida ita, a wannan ranar tayi kuka kamar ranta ze fita  babu yanda batayi dani ba akan muje a cire mata cikin dake jikinta amma sam naƙi yarda nace baza'a aikata laifin kisan kai dani ba, kuma wllh muddin ta cire wannan cikin tota ƙaddara tayi hakan ne a bakin Auranta  wannan kalmar  danai mata barazana da ita itace ta shiga tsakanin niyarta da zubar da cikin harta haifeshi, inda Allah ya ƙara rumata Asiri se Muntasir yazo duniya yana bala'in kamada ita kamar an tsaga kara, duk wata hidima da uba keyi da ɗansa na cikinsa nayi masa ita ban taɓa gazawa ba balle harna kalleshi da wani matsayi na daban ba, amma dayake ɗan Adam Butulu ne kai duk irin Halaccin danai maka da irin wannan sakamakon zaka bani tukwici!!!!"  se'a lokacin wani irin kuka ya ƙwacewa baba shaik.

"komai muƙaddari ne daga Allah haka kuma duk abinda Allah ya tsara mana bamu isa mu kauce masa ba Baban shalele, don haka mu tattara maganar nan duk mu ajiyeta gefe dukda cewar ɗacin abinda ya faru baze taɓa gogewa a zukatan mu ba."  maman shalele ta faɗi hakan yayinda take share hawayen fuskarta da gefan hijabin dake jikinta. Se'a lokacin sumaiyya da itama ke kuka ta kalli Muntasir wanda ke rizgar kuka tace "zubarda hawaye bana irinka bane Muntasir, haƙiƙa ka cutar da rayuwata mafi munin cutarwa sannan kasa almakashi ka datse   kyakkyawar alaƙar dake tsakanina da Mahaifina, dukda hakan be ishekaba har seda ka lalata Aurena da Fu'ada amma dukda hakan se Allah ya nuna maka cewar shi baya zalinci kuma baya bari a cutar da lamarin wanda ya dogara gareshi" kukane yaci ƙarfinta daƙyar ta iya dakatar da kanta sannan tacigaba da cewa "duk irin wannan manakisar da kaimin wllh muntasir ni Sumaiyya Mukhtar Ahmad Azare na yafe maka duk abinda kaimun harga Allah kuma har zuciyata"  gabaɗaya Falon idanu suka zuba mata don basu taɓa zaton zatayi hakan ba a irin baƙin cikin daya daɗe yana ƙunsa mata. Idanunsa na tsiyayar da hawayen ya buɗe bakinsa daƙyar yace "Wllh Sumaiyya ban can-canci ki yafemun ba idan har akai duba da abinda na aikata miki A rayuwa ba !!  Sumaiyya meyasa zaki yafemun cikin sauƙi haka?"  murmushi tayi still hawaye na zubo mata ta kalleshi tace "sabida a sanadinga na samu gwarzon mijin Irin Sulaiman Muhammad Gamawa, da ace baka lalata alaƙar Aurena da Fu'ad ba da yanzu ƙaddara bata haɗani da wancan jarumin ba!!!" ta faɗa tana nuna Man wanda ke zaune agefan Baba shaik sannan tai murmushi tace "wannan dalilin yasa na yafe maka cikin sauƙi tareda da tuna cewar duk wanda yay yafiya sabida Allah to ubangiji shina ze gafarta masa laifukan daya aikata masa"  da rarrafe Beebah ta matsa inda Sumaiyya ke zaune tana kuka tace "na cutar dake ta hanyar muzantaki a cikin jama'ar da kikeda mutunci a gurinsu, don girman Allah ki yafemin ƴar Uwata!!" rugumeta ta Sumaiyya tayi zuciyarta a cikeda farin ciki don babu abinda yafiye mata dedaitawarta da ahalinta daɗi a rayuwarta, nan dai aka dunga yafewa juna sannan Ahalin sukaci abincin rana cikin wani ƙaton faranti gabaɗayansu idan kuka cire muntasir wanda aka ɗaukeshi ak maidashi ɗakinsa, kallon baba shaik kawai sumaiyya keyi rabonda ta ganshi a irin wannan yanayin tun kafin muntasir ya gurɓata mana farin ciki, dariya Emran yay ya kalli Shaik yace "Baba kalli yanda Yaya Asiya kecinye mana abinci karfa su baro gidan mazajensu su karya maka tattalin Arziƙi" dariya dukansu sukayi sannan yaya basirah tace "aikuwa dai don wllh yaya Asiya akwai ci  nan gaba se ƙaramar hukuma tasawa Abban Nihal hannu wajen cida ita" gabaɗayan su dariya sukayi har aka gama cin abincin ko wacce ta kama gabanta, Kyautar ban mamaki Baba shaik yaywa Baban ikilima ta wani danƙareren gida a cikin garin bauchi, Man kuma da kansa ya bashi jari 1milion sannan ya bashi katinsa yace duk sanda ya shiga wata matsala ya kirashi kawai. Nandai yayta godiya harda ɗan hawayensa

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 24, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MUTUNCIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now