*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
_{Babban jarabawa agareta..}_
*NA*_Hafsat Hafnan_
*DA*
_Zainab Chubad'o_*Labarin daya ƙunshi Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fuzgar zuciya❤*
Banyi Editing ba wllh 🙅♀️*20*
_____✍️A haka Rayuwa ta dinga tafiya hankulan gidanjen biyu duk a kwance ba tareda kunnowar wani tseko ba. Kwance tashi akace asarar me rai duk wannan kwanakin da aka kwashe tsakanin Man da Maya wata mu'amala ta auratayya bata shiga tsakaninsu ba, a haka kwanaki bakwan da Sulaiman yayi mata Suka ƙare tareda mayansa wadda yakewa wani kallo na daban kuma me wahalar fassarawa, yau ta kama Juma'a ne wadda tai dedai da 7 ga watan daya gabata Sulaiman ya ɗaga manyan idanunsa tareda saukesu A saman kyakkyawar fuskarta, cikin yanayi na tausasa murya yace "Maya!" gajiyayyun idanunta ta ɗago tareda sauke masa su a kansa batareda ta iya cewa komai ba sabida kasalar daya saukar mata a sanadin kiran dayay mata. Wata gajeriyar Ajiyar zuciya ya sauke tareda sakin mata murmushi yace "muje Falo muyi kallo" ba musu ta miƙe tareda jan maɗaiɗaici ɗangwalinta ta yafa a saman tilin sumar kanta wanda ya sauka har dokin wuyanta sannan ta miƙe batareda ta kuma kallonsa ba, haka kawai seta samu idanunta da kawo hawaye wanda ita kanta batasan dalilin wanzuwarsu ba, abu ɗaya kawai ta sani Shine Zuciyarta sam bata sauraronta indai akan abinda ya danganci Sulaiman ne, ada tana tunanin cewar bazata taɓa kusanta kanta ga zuciyar wani ba kamar yanda tayi akan Fu'ad amma yanzu kam ta fahimci wani babban al'amari a soyayyarta ta baya cewar, ina sonka ko kana sona bashi bane so so yana farawa ne daka lokacin da idanunka suka sauka akan abokin gamaiyyarka wanda ita sam bata taɓajin hakan akan Fu'ad ba, zuwa yanzu ta gama lamucewa kanta cewa Sulaiman sam ba Mutum bane kamar kowa, zefi kyau a kirashi da Sadaukin maza kokuma Mutum na Musamman!!!! Hawayen dake maƙale a cikin fararen ƙwayar idonta ne suka zuraro a lokacin da batai tsammani ba, ɗaga haɓarta yay da sauri yana kallon yanda ruwan hawayen ke sakko mata tamkar an kunna fanfo, jinginar da ita yay a jikin bangon dake dabda jikin ƙofar fita daga ɗakin still yana kallon ƙwayar idonta dake tsiyayar hawaye, hannunsa yasa a hankali ya share mata ƙwallar tareda matso da fuskarsa dabda nata, nan da nan numfashinsu ya sarƙe guri guda lumshe idanunta tayi da sauri sabida baƙon yanayin dake bibiyar duk wata gaɓa ta jini dake jikinta, batareda zato ko tsammani ba taji saukar soft pink lips ɗinshi akan nata. Ƙara rintse idanunta tayi tamkar wadda ake janyewa jinin jikinta a hankali Ya shiga kissing nata gently tamkar wanda ya samu daddaɗar Alewa.
Kissing ɗin dayake gudanarwa a gareta zazzafa ne wanda yasa tunaninta da duk wani yunƙurinta suka tsaya cak, a wannan halin Sumaiyya Muktar Azare ta ƙara tabbatawa dakanta cewar lallai Aure rahama ne sannan kuma nutsuwa ne, iya kissing kaɗai gashi yana barazanar tarwatsa duk wata nutsuwa tata in less than five minutes. A hankali ya zare lips ɗinsa daga nata yana sauke numfashi akai-akai kallonsa ya mayar ga laɓɓanta waƴanda suka ƙara pink sosai sabida tsotsan daya musu, wani irin kyau yaga ta masa musamman yanda lips ɗinta ke fitar da wani irin danshin soliver ɗinshi kamar wanta aka yayyafa musu ruwa, ƙasa tai da idanunta tareda lumshesu kamar ze sakin mata kuka ya kai bakinsa satin fuskanta yace "Mayaaaa" ƙanƙameshi tai sosai sabida yanda tsigan jikinta ke wani irin tashi, lips ɗinsa ya ƙara goga mata a jikin kunnanta a wahalce taɗan saki ƙara hakan yasashi sakin wani gajeran murmushi yace "lemme kiss you again babe matana tana can tana jirana!" sakinsa tayi a hankali batareda ta sake kallonshi ba tace "Goodnight" juyawa tai da sauri ta shige toilet zuciyarta na mata wani irin zafi. Ko sallamar bata bari sun gama ba, Fita yay daga ɗakin taredaja mata ƙofar yana murmushi a ransa yace "mata sarakan kishi" tanajin ƙarar rufe ƙofar ta ɗurƙusa bisa farin tiles ɗin dake toilet ɗin ta fara rera kuka kaman zata shiɗe.
YOU ARE READING
MUTUNCIN 'YA MACE
Action"Sumaiyya ki sani wallahi sai an buga sabon kafce! Koda ni Muntasir zanyi yawo tsirara acikin duniyan nan ne saina tabbata na lalata miki rayuwa ta yadda nan gaba bazaki moru ba ko agidan aurenki!." Muntasir na tsaneka!na tsani duk wanda ya sanka! n...