18

53 2 5
                                    

*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
           _{Babban jarabawa agareta..}_

     
            *NA*

   _Hafsat Hafnan_

                *DA*
   
        _Zainab Chubad'o_

*Labarin daya ƙunshi Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fuzgar zuciya❤*

     

        *18*

_______✍️Yau kimanin watanni biyu kenan da tarewar Sumaiyya kuma har iyau Sulaiman bai samu lokacin matar tasa ba kasancewar awannan lokacin data tare acikin satin nan aka turasu wani aikin contract awani babban kamfani a legas, acan Allah ya hadasu da Muntasir da suma d'in aiki ne ya kawosu wannan kamfanin, haka suka share kusan watanni biyu acan kafin su dawo, amma su Muntasir nasu aikin zai daukesu kusan watanni uku kafin su kammalah...ana gobe Sulaiman zai dawo ya turawa Asmy kudin mota yace su had'e a Bauchi, ba don ranta yaso ba ta hau shiri don yace zasuyi kusan sati daya acan d'in, tun bayan wucewarsa ta tare agdn Alhaji Madugu sunata sha'aninsu, aranar da zata tafi Bauchin ma shida kansa ya sauketa agarage, saida yaga tashiwarsu sannan ya kama gabansa bayan ya cika mata makuden kudade ta account!   ,abangaren Sumaiyya an samu ta kare karatun nata lafiya lau, duk sanda zata makarantar direba ake sawa yakaita kuma yakoma ya daukota inta gama, sosai su Gwaggo ke tattalinta basa son ko gud'a ne ya tabata, hakan yasa tayi wani irin fresh dake nuni da hutu ya samu, ga shapes dinta har kara Fitowa sukayi, Muddin tana gida tofa awajen Gwaggo take yini susha hirarsu, su kuma yi komai tare kai kace kawaye don shakuwarsu ta wuce misali!  ,Khadeeja da yaya Basira sukan kawo mata ziyara lokaci zuwa lokaci kuma itama d'in takan kai musu, kowa yazo mata hatta da Mamansu Muntasir tazo tare da Beebah, nan hankalinta ya dad'a tashiwa ganin irin gdn daular da Sumaiyyar ta samu, Mamanta ce dai har yau bata zo ba.

Misalin biyar din yamma Sulaiman ya iso, Kai tsaye bangaren Gwaggo ya soma shiga kamar yadda ya saba akodayaushe muddin yazo tofa wurinta yake fara zuwa, zub'ewa yayi asaman gadonta yana wassshh Allahna wallahi na gaji Gwaggota" Gwaggo dake saman sallaya tana lazimi tace"Kai Manu ban san iya shege karka karasar mun da katifar dana dad'e ina cin moriyarta tun zamanin toshonka yana tsumma na siyeshi " da sauri yace yana dariya"Allah me iko yanzu Gwaggo tun Abba na jinjiri kike tare da wannan katifar shine kika ki bari acanza miki ita ? " tace"tabbas wannan katifar akansa ubanka Madu yayi fitsari da kashi, kuma bana jin zan bari arabani da wannan katifar dan har gobe babu kamarsa awajena, ko kai baka ji tudunsa na daban bane ba irin naku na yanzu ba ?, kai maza sauka ina magana sai kara daddane mun shi kake gaka ba kadan ba, tashi kaje ka hau na matarka " ta mik'e da casbi ahannunta ta nufeshi tana kokarin shaud'a masa ita, da gudu ya mike yana kyakyatar dariya yayi kofa, adaidai Lokacin Sumaiyya ta shigo wanda kadan ya rage su ci karo da juna!  ,sanye take cikin doguwar riga ta less kalar sararin samaniya da sirkin ruwan madara madara, dinkin bubu akai masa sai ya zauna cas ajikinta, ta kafa daurin Aisha Buhari, sai tashin wani irin ni'imtaccen kamshi kawai takeyi, Lumshe idanu yayi yana jin gabansa na bugawa da sauri da sauri, ita karan kanta kirjin nata bugawa yakeyi don tunda akai auren yau ne karonsu na Farko na haduwa gaba da gabanta, suna dai waya dashi lokaci zuwa lokaci amma babu wani shakuwa irinta ma'aurata atsakaninsu, gaisuwa kawai sukeyi ya kuma tambayeta ya makaranta ? Ita kuma takan tambayeshi aikinsa da kuma Antynta Asmy Ma'u, sai dai kuma acikin 'yan kwanakin da suka shud'e wato gabannin dawowarsa sai kiran da yake mata awaya ta yanke, kwata kwata yabar kiranta, ita kuma koda rana daya bata taba tunanin kiransa taji ko lfy ba, amma dai takan samu labarinsa awurinsu Gwaggo hakan ya bata tabbacin lafiyarsa qalau watakila aiki ne yayi masa yawa shiyasa bai sake nemanta ba..

Gwaggo ce ta katse musu kallo kallon da suke yiwa juna"ni Salame yau ga sabon iskanci, yaran zamani babu ta ido wai agabana suke shirin had'iye juna ? ai kwa b'oye maitarku ku bari in kun fi haka yawa sai ku cinye junan naku " sosai maganar tata ta basu dariya da kunya, Sumaiyyar ce tayi saurin dukar dakai kasa tare da russunawa tana gaisheshi"barka da zuwa ya hanya ? " dauke kansa yayi yana mai kokarin rabawa ta gefenta don ya fice, har ta cire rai da zai bata amsa sai kuma taji yace"Alhamdulillah, mun sameku lfy ?" Gwaggo ta bishi da"yo haka zakuyi gaisuwan kana wucewa ?, kinga maza maza dauki jakarsa kibi bayansa mutumin naki ne sai kinyi hakurin zama dashi dan wani irin murdadde ne wallahi " cike da kunya ta mik'e ta dauki jakarsa sannan tabi bayan nasa, koda ta shiga part din nasu bata tarar dashi ba, ashe yana wajen Mama ya shiga gaida ita, acan ya tarar Abba ya dawo, sai fira ta barke atsakani har ya cika tunbinsa da abincin Mama duk da dai ta hanashi tace yaje yaci na matarsa amma yaki!  ,bashi ya shigo bangarensu ba sai kusan shidda da rabbi, tarar da ita yayi tana Kallon wani movie amma azahirin gaskiya hankalinta baya ga kallon, tunanin Mijinta kawai take, tana tunanin yadda zasu zauna tare da Asma'u awurina daya harna tsawon kwanaki bakwai...."hajiya Maaya tunanin me kikeyi haka ?" Shiru babu amsa sai hawaye kawai take, hakan yasa hankalinsa dagawa yasa hannu ya tabota yana fadin"Ke Sumaiyya wai meke damunki ne? " firgigit! ta dawo hayyacinta tace"barka da shigowa muje in zuba maka abincinka " akaikaice yake kallonta yace"da abinci ya kamata ki soma tarbata ko kuwa wanka ? baki ma tambayi yar'uwar taki ba ko baki da labarin tana hanya ne ? " 'yan yatsunta ta shiga wasa dasu kanta akasa tace"sorry ina da labarin zuwan nata kuma dama ina da kudirin tambayarka kawai saurin baki kamun " uhm! to naji, bai fi 5mins da muka gama waya ba take sanar dani isowarta, yanzu haka an tura direba ya dakkota daga garage " gabanta ne ya bada rass! daqyar ta dago ta dubeshi ta kakalo murmushi tace"to Allah ya kawota lafiya " ta ida magana hawaye na gangaro mata wanda ita kanta bataso hakan ba "Maaya wai menene damuwarki kike kuka ? Kar dai ace har kin soma kishina ? ashe dama ana kishin mutum a inda ba soyayya atsakani ? Ko kuwa dai har Gamawa ya riga ya samu gurbi ne azuciyarki tun bai kai ga kafa gwamnatinsa ba ? eyy 'yan mata Maaya gayamin ina jinki "

MUTUNCIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now