*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
_{Babban jarabawa agareta..}_
*NA*_Hafsat Hafnan_
*DA*
_Zainab Chubad'o_*Labarin daya ƙunshi Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fuzgar zuciya❤*
*24*
_____✍️Yanayin yanda yake kiran sunanta kaɗai ya isa ya baiyana maka irin zallar tashin hankalin daya samu kansa a ciki, miƙewa yayi cikin wani irin hanzarin dashi kansa be taɓa sanin yanada irinsa ba ya kinkimeta se mota, Zainab ce ta ɗakko mayafin rigarta daya zame daga kanta ta bisu dashi a baya se'a lokacin Muktar ya iya cewa " Gamawa don Allah ka nutsu mana insha Allah she will be alright ba abinda ze sameta" kallon Zainab yayi wadda fuskarta ke ɗauke fal da tausayin Sumaiyya sannan yace "Madam pls ga motan Company nan dayazo ɗaukansu Gamawa ku hau ya kaiku gida keda Asma'u bari mukaita Asbiti" ɗaga masa kai tayi tareda cewa " its ok dear Allah ya bata lfy" se'a lokacin Asma'u tayi magana itama cikeda makirci tace "Allah ya bata lfy" jan motar Muktar yayi Suka ɗauki hanyar Baban Asibitin Kuɗin da Compaynsu ya ɗauki nauyin duk wani babban ma'aikacinsu dake aiki taredasu, sedai sukai tafiya me nisan gaske sannan suka iso katafaren Asbitin dake Wuse 2 abuja basu ɓata lokaci ba Muktar yay paking, cikin mintuna kaɗan sega Nurses sanye da fararen kaya riƙeda kujerar faukar marasa lfy.
Ƙoƙarin ɗaukart Suka farayi amma sam sun kasa se jagwalgwala masa mata sukeyi dakatar dasu yayi tareda naɗe hannun rigar dake jikinsa ya ɗauketa kaman baby, a hankali ya fara takawa cikin nutsuwa zuwa cikin Asbitin amma har lokacin idanunsa nakan kyakkyawar fuskarta, kokaɗan be damuda irin kallon da mutane Asbitin kebinsa dashi ba harya kaita ɗakin da aka tanadar mata ya kwantar da ita a saman gadon, wani irin tausayinta ne ya fara tsirga masa tun daga tsakiyar kansa har saman zuciyarsa, idanunsa ne suka sauka a a gefan fuskarta inda ya mareta jiya gabaɗaya seyaji a ransa cewar bekyauta mata ba daya ɗaga hannu ya mari guri me daraja a jikinta, Ajiyar zuciya ya sauke me nauyin gaske sannan ya kai hannunsa dedai gefan bakinta dayay ja ya fara shafawa da fararen yatsun hannunsa, ɗan yatsina Fuskarta tayi kaɗan alamar gurin na mata zafi da sauri ya ɗauke hannunsa a lokacin da likitan ya shigo.
Bp ɗinta ya fara aunawa sannan yasa wata nurse ta ɗauki jininta zuwa lap ba jimawa sosai ta dawo da result ɗin tareda miƙawa Dr. Ɗin, allura ya ɗauka tared haɗawa ze mata da sauri Sulaiman ya riƙe hannunsa tareda tsareshi da manyan idanunsa yace "taya ina zaune zan bari kana namiji ka taɓamin mata?" murmushi Dr. Farouq yayi bece komaiba ya miƙawa Samirah nurse ɗin dake gefansa yace "gashi ki mata idan kin gama seki sameni a office dake dashi" karɓan alluran tayi tana murmushi tace " sir seka ɗan naɗe mata rigan jikinta sabida a bayanta zan mata ba'a hannu ba" da sauri Sulaiman yace "ok" ɗagata yay daga kwancen datake jikinta zafi rau har lokacin, a nitse ya janye haɗaɗɗen baƙin rigan har zuwa saman faffaɗan hips ɗinta daya fito sosai a cikin farin sket ɗin dake jikinta wanda yabi fatar jikinta ya kwanta lub dashi, hannu Nurse Samirah tasa taɗan janye farin panty ɗin dake jikinta tai mata Alluran wanda tasa Sumaiyya ta ƙanƙamwshi sosai a jikinta sabida zafin dataji, zare alluran tayi sannan tace "kaɗan murza mata gurin sabida karya mata ciwon don naga ta ƙanƙame jikinta sosai" be kulata ba yasa hannu a dedai gurin ya fara murzawa kaɗan har yana lumshe idanu. Zaunar da ita yay a gefan gadon yace "barinje naga Dr. Kinji?" ɗaga masa kai tayi tareda share ƙwallar data zubo mata da bayan hannunta, hannayenta ya kama cikin nasa a hankali ya fara mirzawa a hankali tareda kafe fuskarta da manyan dara-daran idanunsa yace " pls Maya don Allah kibar kuka kinji?" ai kamar yace ta ƙara yawan gudun hawayen nata ne se kawai ta fashe da wani irin kuka "oh my God!!" sulaiman ya faɗa yayinda ya janyota zuwa jikinsa da zummar ya rungumeta, janye jikinta tayi da sauri sannan ta zauna a ƙasan tiles ɗin ta fara rizgar kuka kamar bazata dena ba daƙyar ta iya buɗe baki cikin kuka tace "wllh zazzaɓin dake jikina rahama ne akan ciwon dake cina a cikin zuciyata Man!" kamar yanda ka faɗa a baya hakane nayi kuskure sosai da harna bari zuciyata ta fara son mutumin da banida da gurbi a cikin tasa zuciyar, a nawa haukan ban taɓa zaton kusanci kan iya haifar da soyayyar me tsanani ba seda na Rabeka, Ashe abinda ban sani ba shine duk abinda zuciya da baki suka gaza furtawa to taɓawa takan iya isarda saƙon ba tareda gangar jiki ta ankare da hakan ba!" hawayen idanunta ta fara sharewa da sauri kamar wata zararriya, lokaci guda kuma ta saki murmushin dayafi kuka ciwo tace "bazan tilasta maka wajibi seka soni ba amma ina roƙon wata alfarma a gareka don girman Allah ka sanar dani laifin dana aikata maka yasa ka canza min,ni kuma nayi maka alƙawarin cewar idan har inada masaniya akan laifin wllh zan sanar dakai duk wata gaskiyata ba tareda na maka ƙarya b......" kuka ne ya kuma suɓuce mata wanda hakan ya haifarwa da Sulaiman tsananin Tausayinta, kasa ce mata komai yayi illa ɗagota ya haɗa jikinsa da nata ta hanyar rungumeta
YOU ARE READING
MUTUNCIN 'YA MACE
Action"Sumaiyya ki sani wallahi sai an buga sabon kafce! Koda ni Muntasir zanyi yawo tsirara acikin duniyan nan ne saina tabbata na lalata miki rayuwa ta yadda nan gaba bazaki moru ba ko agidan aurenki!." Muntasir na tsaneka!na tsani duk wanda ya sanka! n...