11

32 1 1
                                    

*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
           _{Babban jarabawa agareta..}_

     
            *NA*

   _Hafsat Hafnan_

                *DA*
   
        _Zainab Chubaɗo_

*Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fizgar zuciya❤*

     

        *11*

____✍️"Bayanin Uwar me zan musu bayan cin zarafin ƙanwata da kadaɗe kanayi?"  cikin yanayi na wanda ke dabda kiɗimewa yace " wai me kake ƙoƙarin faɗane Muntasir? Don Allah idanma wasa kakeyi pls ka dena man........   " Dalla malam rufemin baki Azalimi kawai  mayaudari  Wllh kaci amanar abotarmu dakai Lukman, bantaɓaji a raina na tsani wani mahaluki ba a rayuwata sekai kuma wllh bazakaci banza ba seka girbi abinda ka shuka!!!"  duk maganar da Muntasir keyi idon Lukman na kansa, kallonsa kawai yakeyi sabida tsabar kaɗuwa da mamakin abinda Muntasir yayi masa wata irin ƙwallar baƙin ciki ce kwance a saman ƙwayar idanunsa waƴansa sukai ja sabida ɓacin rai, bakinsa na Rawa ya nuna Muntasir a mugun ƙufule yace " Ni kaiwa haka ko muntasir? "nika gaiyato cikin gidanku kuma ka ratawa jakar tsaba ko?, to na rantse da ubangijin daya Halicci Annabi Adamu sekayi danasanin abinnan dakai min billahillaz..... Wani ɗan iskan mari Baba shaik ya sake ɗauke Lukman dashi sannan ya nunashi cikeda ƙunar zuciya yace "wani danasani xakasashi yayi banda wannan wanda ka sanyamu gabaɗayan mu?"  zeyi magana kenan  numgashinsa ya fara sama sabida fishi da ɓacin ran dayake ciki, da Sauri Abban Adil ya tareshi cikin yanayi  na Rarrashi yace " Haba Baba Sam be kamata ka bari ɓacin rai da fushi su dinga sarrafa zuciyarka ba a wannan lokacin, duk abinda zamuyi ko muyiwa Lukman baze taɓa goge tarihin abinda Sumaiyya ta aikata ba koma ince suka aikata ita Lukman  ba, don haka don Allah baba ka saisaita zuciyarka mu samarwa kanmu mafita ba tareda maganar nan ta fita waje ba"

"taya zan iya rarrashin kaina akan wannan abinda Sumaiyya ta aikata min ? Allah ya sani na baki tarbiya gwargwadon iyawata, haka kuma nasoki so mafi tsanani a cikin  ƴaƴan dana haifa a cikina,  na fifitaki samada kowa cikin ƴaƴana, Sumaiyya Meyasa zakiyiwa Ubanki Muktar Azare haka?"  ya ƙarasa mganar yana fashewa da wani irin kuka wanda yasa ba shiri ya zube akan gwiwoyinsa yana mecigaba da kukan daya kasa dannar kansa,  Sumaiyya wadda taci kuka harta godewa Allah kasa cewa komai tayi sabida wani irin zafi da zuciyarta ke mata, wani irin abu takeji a saman maƙoshinta yana taso mata,  idanunta da suka rine da kuka ta ɗago ta kalli Mahifinta wanda ke zubar da hawaye a sanadin sharrinda muntasir ya ƙulla mata tace  " haƙiƙa na karya tarihin wannan Ahalin tunda har na saka Mahaifina kuka da idanunsa!! amma inaso kowa dake wannan falon ya sani kuma ya shaida cewar Allah baya bacci kuma baya zalinci, haka kuma yana gaggauta karɓar Addu'ar wanda aka zalinta ba tareda haƙƙinsa ba,  ina Roƙon Allah da sunayensa Mafiya kyawu yaymin sakaiya akan duk wanda ya zalinceni har yay sanadiyar zubar hawayen Mahaifi......... Mari yaya Basira ta ɗauketa ɗashi wanda yasa ba shiri ta haɗiye maganar dake ƙoƙarin fitowa daga ƙasan  maƙogaronta, cikeda ɓacin rai tace "don uwarki har kinada bakinda zakiyi wata magana bayan duk hujjoji sun tabbatar da cewar ke ɗin Fasiƙace?, wllh ni kaina kin cutar dani Sumayya!  Nasoki so na gaskiya sabida har raina nakejinki amma kika cutar da irin yardar danai miki meyasa kikai haka Sumaiyya why?"   " hmmmm ai kibarta kawai yaya Basirah ni kaina sumaiyya ta mugun bani mamaki a lokacin dana ganta rashe-rashe a kwance kan gadon Lukman,  wllh yarinyar nan ta wuce duk yanda kuke zato, muguwar makira ce ga ɗan banzan taurinkai kamar jinjirar Jaka" Muntasir ya faɗi hakan yayinda yake jifanta da wani ɗan iskan kallo wanda yasa taji ƙirjinta ya buga da ƙarfi, kaf falon babu wanda ke firta alkhairi akan Sumaiyya sakamakon makircin Muntasir dayay tasiri a kunnuwansu da zukatansu, ɗagowa Baba shaik yay da jajayen idanunsa yana kallon Sumaiyya batareda ya iya furta koda kalma ɗaya ba, ajiyar zuciya ya sauke tarda ƙara share ƙwallar dake sakko masa yace  " duk wani wanda zeji ciwon abinda Sumaiyya ta aikata to wllh a bayana yake, don haka zan zartar mata da hukuncin danake ganin shine daidai akanta."  Muryar Emran dake tsaye jikin ƙofar falon tun lokacin da aka fara meeting ɗin ce ta katsewa kowa hanzari ciki kuwa harda  da baba shaik  dake ƙoƙarin yankewa Sumaiyya hukunci bisa laifinta yace " yanke hukunci cikin fishi sam ba aikin masu ilimi bane Baba duba da yanda ilimi kan zama hasken fitilar dake yaye jahilci,idan har zan iya tunawa dedai kaine ka karantar dani cewar Akwai ayar datai magana a  cikin alƙur'ani wadda take horar damu cewar  yanada kyau idan aka kama mutum mai lefi abashi dama ya kare kansa, haka kuma shari'a bazata yanke masa hukunci ba harse  idan me laifin ya gaza kare kansa da gamsasshiyar hujja  sannan ne ya halatta a zartar masa da duk hukuncin daya dace dashi don gujewa ɗaukar hakki da kuma  zalinci""

MUTUNCIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now