16

36 1 1
                                    

*MUTUNCIN 'YA MACE....!*
           _{Babban jarabawa agareta..}_

     
            *NA*

   _Hafsat Hafnan_

                *DA*
   
        _Zainab Chubad'o_

*Cin zarafi, cin amana, k'eta, illar k'awa da kuma zazzafar soyayya mai fuzgar zuciya❤*

     

        *16*

______✍️Bakwai saura na dare su amare suka isa gdn Alhaji Muhammad Gamawa, 'yan'uwansu Sulaiman wa'enda ke nan kusa yawancinsu sun samu zuwa tarban amarya duk kuwa da cewa akurarren lokaci ne aka sanar dasu, amma sai sukayi kokarin goyawa dan'uwan nasu baya!  ,babu abunda kake ji na tashi sai sautittinka gud'a daya karade gidan, abangaren Gwaggo akai wa baki masauki, kuma Khadeejah ta cika alk'awarin zuwa, Sumaiyya hadda rungumeta tana kukan murna tare da zuba mata godiya na taimkonta da tayi tasa baki har Baba Sheikh ya amince ta karashe makarantarta!  ,Zaune take abakin kafcecen gadon dakin da aka saukesu, kanta lullube cikin katoton mayafi sai sharban kuka take ganin su yayyunta da yafendunta Farida duk sunyi haramar tafiya dan sun kafe akan bazasu kwana anan ba sai agdn yaya Basira!  ,hannu takai ta damko hannun Khadeeja dake zaune kusa da ita tace cikin yin kasa da murya"Khadeeja dan girman Allah karki tafi, keda Yafendu ku kwana tunda su sun k'iya "wa ? aikam baza'ayi hakan dani ba, kafata! kafarsu ! " ....."Ni zan kwanan miki in kinaso, kai inma kinason in miki 'yar zaman daki ne zanyi kin ga ko ba komai duk safiya dai inna tashi zan dunga had'a ido da madarar zuciyata inji sanyi, kin min kwacensa amma babu yadda na iya dake, wannan gatan ne kawai nakeson kimin wato ki bari in zauna agidanki ...." babu wanda be dara ba da wannan shirme na Beebah ba, ita da hankali sunyi hannun riga ne kawai, irin shigar da tayi kadai ma zaisa kasan hankalin bai wani wadace ba, sai ta wani togalo dankwali gaba ga sharb'a sharb'an lebunan nan nata da suka sha jan fenti sai walkiya suke kamar tsuliyar biri, dariyar da suke mata ne ya kufular da ita don hatta Sumayyar ita kanta sai da wani munafikin murmushi ya kufce mata,  "meye abun dariya donna fadi iya gaskiyata ? " aharzuk'e Khadeeja tace"ban tabbatar da cewa ke din baki da hankali ba sai yau, kai maganganun da ma kike yi ya nuna kwata kwata baki da saiti, just imagine the moron having a crush on her sister's hus......" Wani irin wawan mari ne ya hanata ida abunda tayi niyyar fad'a..

Yaya Asiya ce da wannna danyen aikin wacce tun farko ranta bai so ta biyosu ba don dai kawai babu yadda ta iya ne kasancewar Baba Sheik jan ido yayi mata shiyasa, karin takaicinta ma ya dad'u ne sanda ta tabbatar da cewa gdn maiko ne suka kawo Sumaiyyar!  ,yar yatsa ta shiga karkadawa Khadeejar da tayi Sumar zaune tana fadin"yarinya ahir dinki! Karki kuskura kiyi gangancin tura kanki cikin ramin da bazaki iya fitowa ba in har ba kinsan abunda kika taka bane, Habibar ta miki kalar shashasha ne da har zaki dubeta ki zageta ?, ai gaskiya ta fada shigar sauri aka mata, Sulaiman Habiba yakeso shine Badi'atou tayi shige shige har ta dauke hankalinsa zuwa ga 'yarta wacce ta gama rarrabar da mutuncin kanta akan hanya, jakar titi abin hutawar garadai gata nan ku kalleta dakyau... " ai basai kin tsaya batar da lokacinki wajen zayyane ko ita d'in wacece ba, da hankalina da kuma sauran numfashina bazan tab'a yin gangancin had'a Zuri'a da Fasik'a ba, Allah na gode maka daka bayyana gaskiya tun kafin nayi kukan dana sani akurarren lokaci don wallahi bazan jira ma har sai an wayi gari ba, kafarku kafarta in har na isa da mijin nata! in kuma ya nuna mun cewa ban isa dashi ba to ai na isa da mahaifinsa kuma ya zama dole ayi abunda nakeso" ...da sauri suka waiga suka sauke kallonsu akan Gwaggo wacce ke tsaye abakin kofa da shigowarta kenan, Sumaiyya bata san sanda ta yaye mayafin kanta ta mik'e da gudu tayi wajenta gami da fashewa da kuka ba, adaidai lokacin Yafendu Farida ta fito daga toilet don dama can sauri take ta fito taci mutuncin Asiya sai ga wata sabuwa kuma, hakan yasa ta yanke bahayarta babu shiri ta fito!   ,Sumaiyya ta zube agabanta gami da rirriko kafafunta tace"dan girman Allah hajiya karki dauki abunda ta fad'a da mahimmanci Wallahi ba gaskiya bane sharri akemin, ni ba fasika bace, ban tab'a aikatawa ba amma kuskurena daya na tab'a kusantar inda yake..." da azama Yafendu Farida ta karaso wurinta tasa hannu tana dan jijjigata tace"ke Sumaiyya ki dawo hayyacinki, baki tab'a kusantarsa ba kuma insha Allahu Allah bazai sa mu ga wannan ranar da zaki koma amshin wannan sunar ba, hajiya abinda kika ji ki yadda dani ba gaskiya bane....." Gwaggo ce tayi saurin taran numfashinta"Na shiga ban dauka ba baya fidda barawo, yarinyar ma da kanta kinji abunda ta fad'a, ta tab'a kusantarsa, kenan ba wai ta zama shahararriya bane aharkan kawai sau daya tak! Arayuwarta ta tab'a aikatawa ! kuma sannan ni ba zancen dana ji wannan tana fad'i bane ya daga hankalina ba " ta furta tana nuna Asiya da 'yar yatsa gami da girgiza kai kan tacigaba"a'a ina zaune na ne na sami labari da zafi zafinsa, abunda ma yafi dauremun kai da wannan al'amarin shine.....shine...." kasa karasa maganarta tayi sakamakon kukan daya ci karfinta, Cike da kunar Zuciya tace"wallahi Muhammadu ka cucemu daka aurawa danka Shahararriyar karuwa, kuma ayanzun nan zan nuna maka cewa Nima na isa da gidana! " juyawa tayi ta fita daga bayanta tana kwalawa Zainab kanwar Sulaiman k'ira, Su Yafendu kuma suka mara mata baya suna rok'o.... "Ke Zainab kiramin Ubanki awaya kice dashi maza maza ina son ganinsa yanzun nan ".......amsawa tayi da"Tou" amma tasan babu lafiya...

MUTUNCIN 'YA MACEWhere stories live. Discover now