11 NEENA MALEEK

1.7K 128 13
                                    

   Sarki Family. .....❤
 
           11.

Zagaye suke a kan dining table suna lunch kaf yaran gidan da surukan gidan suna ci suna dan hira k'asa k'asa.
  K'aran tawowa sukaji hakan yasa su kallon step d'in da ake sakkowa. .... wow wata cute baby ce cikin English wears top d'in fara ce sai red d'in skinny wanda ya fiddo da ainihin suran jikin ta hips kamar sa fashe.
  Baka ce gaskiya dan farin dake jikin ta bana komai bane face na tsabar hutu da kuma AC batada tsaho sosai amma duk inda mace take wannan yarinyar takai.
A shekaru bazata wuce shekara 22 ba. Kanta babu dankwali kalaba ce manya wanda akaiwa ado da wasu duwatsu masu kyau.
  Sakkowa take ciki da yanga harta k'araso kan dining d'in....kusa da wani dattijo taje wanda shima tsabar hutu bazaka tantance shekarun sa ba.
  Uncle shine kuka fara cin abincin ku kuka kyale ni koh?, kanta ya shafo yace NEENA badai rigima ba thought da kaina naje na tashe ki amma baki fito ba sai yanzu.
Cikin shagwaba tace wallahi Uncle baku sona u see babu wanda yazo mun welcome natashi lafiya ba, ayya NEENA wallahi duk munje baki tashi ba wayace bamu son ki?, we can do anything for u ....kece fa sanyin idaniyar mu muna son ki kece ma baki son mu.
  Aunty Mimi ina son ku mana....tafad'a a shagwabe....to amma ai ni a gidan mu ina zuwa kowa yake tashi har saina zauna.. 
  Uncle ne yai dariya yace hooo NEENA gaskiya wanann halin daga ke sai Dadan ki da Maman ki...mu dai muna son ki amma wannan mulkin....wayyo Dada zo kaji saida nace ban zuwa kace nazo gashi nan sunata zagina sai kuka na gaske kuma.
  Yaya Farhan ne ya mike yace to fa jangwam zo NEENA wasa muke miki wa zaice baison k'anin sa a duniya?, kalla kiga babu wanda yaci komai ke muke jira...NEENA muna son ki sosai kece hasken mu muna qaunar ki kodan kamar da kikai da Maman mu dole mu so ki.
Baki NEENA ta tabe "Hmm nidai nasan Dada na da Momy na sunfi sona, haba lelen Dada wayace bake ba yar shagwaba mu kowa ya takaki sai inda k'arfin mu ya k'are.
Dariya takama kafin tace ai nazata baku sona...amma meyasaka matan ku basu zo ba?.
To qanwar mu taxo gida bamu sani ba tanason taga matan mu kusa da ita ko bata so shiyasa basu zo ba.? Dariya tai sosai kafin ta furta tab kuma dai ai matan ku familyn mune kuma suma yayu nane tunda suna auren jinana taya za'a ce bazan so su ba?.
Sunada yara tare daku yanzu ace yaran ku su girma suji banason iyayen su nata da wanne ido zasu Kallen please ku kirasu ai suma mune...amma fa banson raini I will respect them all as my sisters amma idan naga wani abu gaskiya bazan d'auka ba.
Haba NEENA dole ne su biki indai suna son kansu a gidan nan...shidai Uncle murmushi kawai yake yana kallon NEENA yanason ta sosai komai nata irin na Zainab ne matar sa fatan sa Allah yaiwa Matar sa rahma.
Tare da matan sukai breakfast sunayi suna dan hira dake sunsan juna sosai idan sukaje London mace guda ce kawai jinin su bai had'u ba amma sannu zata koya mata hankali dan koda sukazo ta gaida ita bata wani sake ta amsa ba.
  NEENA yar gidan Dada gashi zaman 9ja yakama ku ya zakiyi?, Aunty Mimi  yazanyi kuwa ai mahaifata ce nan banda kowa a London idan ba Dada da Mama ba to suma zaman yakama su dole na zauna.
Ban mance wa Mijin ki kuwa ya kirani lokacin ina London yai tamun nasiha akan rayuwa da yanda rayuwa ke juyawa da kuma samu da rashi....ya gayan cewa kowa d'aya ne da talaka da mai kud'i nayi halin yayu na saboda kunada kirki naso kowa kodan watarana yace mun idan har zaman tare yakama mu duka zanga canji dole nai hak'uri gashi kuwa yakama inason mijin ki sosai yanada kirki.
Ayya hakan da yace miki is good kuma nasan kinji nasiha koh?, Aunty naji mana kuma duk wanda yasamu ilimi na addini ai bashi ba d'agawa dan wanda akai duniyar domin sa ma bai d'agawa kowa kai ba bare mu wanda ba kowa ba agun Allah saidai idan munyi aiki nagari.
Aunty kullum idan na kwanta na kan yi tunanin wa zan aura wa zai auren da wa zan zauna nan gaba?, bansani ba kinga kuwa dole kayi k'ok'arin gyara halin ka kodan gaba.
  Daga bayan ta taji an rungume ta ana cewa weldon yarinya ta....yarinya tazama babba kullum sainayi tunanin ya zakiyi rayuwa anan ashe babyn tamu tanada hankali wow am so speach less NEENA...zamu so ki sosai kinji....dariya tai kana ta juyo wadda take gaban ta kusan sa'ar Aunty Mimi ce kuma duk kamar su d'aya da ita ba kowa bace face matar Uncle  su qanwa kuma ga Matar sa wadda ta rasu.
Ummi ko baku sona nidai jiran dawowar Dada na nake na koma gunsa....dariya sukai duka kafin matar Ya Abdul tace ki jiki da wata magana Dadan naki da yafi shekara a 9ja kece dai baki jima ba shine zakice ya dawo ki gudu gunsa to mu rike ki...tab Mrs Abdul babu wanda zai kwace ni gun Dada. Sai mijin ki inji Aunty Miki.
Nan suka zauna akaita hira ana dariya kafin masu aikin gidan sukazo suka kwashe kayan...suma canja parlour sukai akaci gaba da hira.
Can wajen 1 Uncle ya fito cikin shirin sa na Office da sauri NEENA ta mike uncle zani nima?, NEENA office ne kuma zanyi meeting da senates shiysa kibari wani lokacin kinji?.
  Matar Yaya Jameel ce ta fakaici idon kowa ta saki wani murmushi na mugunta daidai nan suka had'a ido da ita...itama NEENA murmushin ta saki.
Ba komai Uncle kaje wataran ma tafi tare. ..yauwa saina dawo koh?, kowa tashi yai akai masa adawo lafiya kafin security d'in ya bude masa k'ofa suka fice.
  Aunty Mimi zaki koma gida yaune?, eh sis kamar kinsani ango na zai dawo kuma ma kwana bakwai nayi dashi amma sai gobe dai zan tafi dan ba yau zai dawo ba ...ayya zan koma gidan ki kafin Dada ya dawo....sis gida na kuma kai naji dad'i nayi murna oyoyo bara nai waya sai mu sami jirgi koh?, banson nuna isa ace sai lokacin da zaka fita sannan zaka nemi jirgi kingama shirin koh?. Think so...Bata dubi kowa a gun ba ta haye sama dake Ummi ma na sama d'akin ta tayi.
Kan gado ta ganta a zaune jikin ta tafad'a tace Ummi nagayamiki Uncle baisona kince wai yana sona agaban matan broths fa nace zan bishi yace a'a ita kuma waccen harda mun dariya zanyi maganin ta yau d'in nan zan bar gidan.
  Daughter bangane taya zakice zai kibar gida ina zaki idan kin tafi? , Ummi gun Aunty Mimi zan zauna idan Dada ya dawo saina zo. Ayya Daughter uncle d'in ki baida lafiya da qyar ya shirya fa yanxu ma ki masa uzuri kuma inaga duk duniya baison kowa kamar ki yanason ki kara yakewa Dadan ki ganin yadda yake kula da ke ki gane mana yarinya mai iyaye da yawa.
  Dariya ta fara kyalkyalawa harda rike ciki kafin tace Ummi waike amma kece last born a gidan su Mama?, me kika gani?.
To ganin ki nayi fa ba wata babba ba kamar mate d'in Aunty Mimi ma, eh kusan haka amma nabawa Sakina two years.
  Ok...yauwa Ummi gaki kyakyawa amma ya akai kika auri tsoho dan Allah?.
Dariya Ummi ta sanya sosai kafin tace amma ke d'in nan su Aunty sun lalataki wallahi kinfiya calikanci yo duk tsufan sa haka nake son kayana ehe ta fad'a tana murguda baki.
Bude k'ofa sukaji NEENA ce ta juya..matar Yaya Jameel ce da sauri ta daure fuska tace excuse ina magana da uwata idan nagama kya shigo out tafad'a da k'arfi zatai magana Ummi tace NEENA mene haka matar yayan ki ce fa.
  Eh nasani itace saime Ummi duk wanda ke sona nake so banson wanda bai sona, NEENA bani ke miki magana ba?, tsam ta mike ta fice daga d'akin tace Ummi nabar ku.

Auta ce
     
    Am sorry fans....I can't update this book again....cuz of many reasons...u guys are my reasons. ..
Thank you so much #Anataresosai sosai ❤👌

NEENA MALEEK     {COMPLETED}Where stories live. Discover now