37 NEENE MALEEK

1.2K 67 4
                                    

Da sauri Mama ta dago kanta tana duban Neena kallon juna suke sosai a hankali Neena tace Mama kiyi hakuri bansan ranki zai baci ba da ban fada ba.
Dan Allah mama kada kiyi fushi bangayawa kowa ba sai ke tunda baki yarda ba wallahi shikenan. Dan murmushi Maman tayi tace Neena kenan kina zaton zaki bukaci namiki abu nakasa ne wallahi ko abinda yafi wannan wuya ne zanmiki indai ba addini yasabawa ba.
Safeena tanada kirki zanso nikaina tasan dadin rayuwar aure, Allah ya sanya alkhairi Allah kuma yasa wata falala ce daga Allah.
Ihu Neena tasaka ta rungume Mama tana wow Mama u are special fa tnq tnq remain Dada na.

Wayar dake dakin tayi amfani da ita wajen kiran Dada da uncle da Ummi lokaci daya suka zo.
Bukatar data zowa da Mama ita shima ita tagayamasa. Kafin yace komai Mama ta dora da Dada kagan Safeena tanada kirki fatana Allah ya sanya alkhairi a abin Neena tayi tunani mai kyau.
 
   Banzan kallo ya watsa musu kafin yai tsaki yace da ke kune iyaye na sainayi abunda kuke so ke kuma dake bakisan ciwon kanki ba harke ake rokon amiki kishiya ko kuwa Alamu kika gani na kin gaza ne?, ko kuwa ji kikai ina zancen kara aure?, to bazanyi ba bazan kara aure ba idan kingaji da nine saikigayan amma ban miki alkawarin kara aure ba ke daya kin isheni duniya da lahira Banda fatan auren wata mace bayan ke.

  Fita yake kokarin yi da sauri Neena Tasha gaban sa tace Dada kai duba da rayuwar da Momy tayi na wahala da kunci, wallahi duk duniya kaine kadai wanda zaka iya bata farincikin data rasa, kuma Dada yar uwar kace Momy batada aibu. Mama kuma ai ba ta hana ka ba kuma itama duba tai da Momy mace ce tagari yasaka ta amince, wallahi badan Momy bace banga macen da zance tashigo rayuwar mu ba.

  Badan Momy bace banga macen da zata zamo abokiyar zama ga Mama naba. Zumunci da taimako zakayi ka duba halin data shiga dan Allah Dada dan soyayar ka da Annabin Rahma da ni kuma ka auri Momy kuka take.

Uncle kace ya aure mana dan Allah?, mr president baice komai ba illa kallon Qanin sa da yai kana ya kai kallon sa ga Mama.

Kafin yace wani abu Dada ya janyo Neena jikin sa yace Neena kukan na mene kuma?, indai auren ta zaisaka kiyi murna wallahi na yadda Allah yaban ikon adalci tsakani yana magana yana kallon Mama wadda sai murmushi take....shi kam hararen ta yai.

Ihu Neena tasaka na murna sosai taita tsalle tana godewa Dadan ta da Mama.
Masha Allah yanzu kuma sai a kirawo Mommy Da kanta ta sauka kasa wajen Momy, a zaune taganta itada Maleek suna ta hira hannayen su na sarke da juna kansa yana kafadar ta sai dariya yake
Wajen su tai da murmushi tace Momy meyake cemiki kuke dariya haka?, bakin sa ya murguda yace oh shi mutum da son jin gulma ko Ina ruwan sa.
Lah nice mai gulma koh?, kafar sa ta take, osh zaki ciremin danyatsa fa, ai gara na cire tafada da murmushi shima dariya yai.
Yauwa Momy kizo Uncle yana kira har kaima, mikewa sukai nan Momy tai gaba, shikam ganin Momy taigaba da sauri ya janyo ta....wana kama? Haba babyn Neena ai kasan wasa nake fa, kafada ya make yace banyarda ba nifa saina Rama, fuska ta shagwabe Tace to nifa da wasa nake, dariya yaimata yace nima da wasa nake inani Ina taba lafiyar jikin mata na. Daidai nan suka karasa dakin.
A zaune suka tarar dasu Neena ce ta kalli Dada tace Dada na Kaimata bayani kaji?, aa Neena kece zakiyi fa domin kuwa kece komai.
Tom Dada na. Wajen Momy taje inda ta tsuguna ya kamo hannayenta duka kafin tafara da Momy nasan abunda zan gayamiki zai zama sabo ranki domin baki taba kawo hakan ko a mafarki ba.

   Momy duba da kedin uwace kuma da rayuwar da kikai nagan yakamata ace kema kinyi aure kina dakin ki kodan cikar kamalar ki da kuma dorewar farincikin ki dana iyayen mu baki daya.
Aure shiyafi cancanta dake, kuma babu wanda ya cancanta ya zama mijin ki face Dada na.
Fatan zaki amshi tayin mu ki auri Dada kinga Dan uwan kine kuma zai rikeki da daraja.
Kwalalo idanu Momy tayi tace ke Neena kina cikin hankalin ki kuwa?, taya zan auri mijin Fatee qawata? Bazan iya ba wallahi, ni banson aure wanda nai a baya ma Alhamdulillah.
Momy kada kice haka da yardar Mama da Dada nazomiki da wannan Maganar saidai idan ba irin Dada kike so ki aura ba, ko kuma bazaki iya zama da Mama ba matsayin abokiyar zama.
Haba Neena ya zakice haka amma haka kawai sainazo na aurewa mata mijin ta?, da yardata fa Safeena kuma Dada ya amince babu komai yardar ki kawai muke nema saidai idan bamu cancanta kimana alfarma ba.
Haba Fatee taya zakice baku cancanta ba amma gaskiya....aa kada kice komai kisawa abin albarka kawai ko ba haka ba Maleek?, kwarai kam Mama.
Naji dadin haka Allah yabiyaku da alkhairin sa hakika samun irin ku sai an tona kudin na daban ne ko cikin alumma.
Momy kada kice aa rahma ce auren ki cikin dangin ki, kuma kinga ke bakiwani jima acikin rayuwar aure ba kaddara ya fada inaganin wannan sakamakone Allah yaimiki.
Maleek kaima kenan ka yarda? Kwarai Momy domin inda zakiji dadi ne ba inda zaki wulakanta ba.
Kan Momy a kasa tace na yarda Allah yasa alkhairi. Ameen kowa yace agun.
Ummi ce tace gaskiya naji dadin haka wallahi. Abdul dake shigowa yace ai sauran ke Ummi kema sai asamowa Baba koh?.
Cikin fusata tace wa?, ai wallahi babu wajen wata a gida na. Kai Baban kuma baison mata biyu ko can, mai mugun baki.
Dariya Dada yai yace ai wato Ummi kishin ku daya da marigayya kinsan tana labour fa tagan wata nurse tana kallon Yaya wallahi cikin karaji taringa cewa ke fita I don't need ur help out I said, dariya akai sosai kafin Mr President yace ai Allah yaimata rahma amma akwai kishi katuna lokacin da nake saka mask?, na tuna ai Yaya kasha gashi wajen big Aunty.... Eh yasha nima kuma ba kishiya in our policy ko ba haka ba Babyn zuciyar Ummi? Dariya Mr President yasaka sosai yace kunji koh taji maganar kishiya ta manta da kunya tafara Baby to dai ga yaran ki nan.
Sai me suma wayasan sunan da suke gayawa junan su. To naji kanta ya shafa dake ta kwanto jikin sa....ba kunya domin Ummi Baby take komawa a gaban Mr President yaran sa harsun saba da ganin haka.

   Murmushi sukai nan akai addua aka sanyawa auren albarka.
Dada nifa inada magana nima. Munajin ka Abdul.
Yauwa gani nai maizai hana Baba na Sokoto shima a bashi guda tunda kunya har yanzu bai aure ba tun rasuwar Matar sa.

Ah shawara mai kyau kasan kuma wallahi ko zuwan nan saida mukai magana (Governor of sokoto), ka kawo shawara inaga wacce tafi dama kai Maleek cikin iyayen naka?.
Dariya Maleek yai cikin kunya yace ai Abba inaga Umma ce saboda nagan Uncle dan gayu ne itama kuma itace kawai ai maganar Umma.
Saboda babar kace koh?, ba haka bane Momy kawai dai yafada yana sosa keya.
Eh hakan ma yayi dayar sai aiwa Uncle din Adamawa maganar ta, wa kenan?, Madakin gini mana ai naji kwanaki yana neman aure, ko ba haka bama dole yai tunda matar sa tazama fanko yanzu.
Kaci uwaka ai cuta ce Abdul zakace fanko, murmushi sukai nan dai aka tsara komai a gun Mr President yaiwa kowa waya ya gayamusu sunyi naam kuwa da maganar.
Momy kam kunya ce kawai a cikin ta saboda takasa sakewa har a gun cin abinci takasa motsi ma. Saida Mama da kanta tace oh su Safeena kunya kuma?, dama ance indai a kwai kunya akwai so. Cikin sauri ya dago tace wallahi aa babu fa. Dariya su kai mata nan dai taita janta da hira harta sake.
Suma suna gama cin abincin Suka fara shirin tafiya gidan su.

Auta
Ce ❤️❤️❤️

NEENA MALEEK     {COMPLETED}Donde viven las historias. Descúbrelo ahora