Khairiyat wannan ma nakine page d'in....kinason Book d'in nan sosai sosai....29.
Salati suka saka gaba d'ayan su kowacce kagani jikin ta rawa yake cikin tashin hankali Amma tace to fa daga yanzu kenan anfara inaga an kai k'arshen wasan.
Isma ce cikin rashin gane maganar Amma tace khadija bangane maganar ki ba?.
Isma ai bazaki gane ba tunda har yau Allah bai waye muku garin sa ba.
Bazaki gane ba tunda kema bakar aniyar uwar ki kika kwaso ta ina zakiga ne cewa Allah ne ya kama Uwar ki akan shirka da ta'addacin da tayi ne. Baba kad'an kika gani bakiga komai ba nidai Allah ya ganar dani komai ni d'in ma ashe ba barni kikai ba nida uwata to gaskiya tayi halin ta anyi walk'iya gari ya haska mugu zai koma makomar sa.
Umma idan zaki tsaya ne to nikam tafiya zanyi dan ubangiji zai iya saukar da ikon sa akan ku gaba d'aya mutanen da basa sallah...zakkah...azumi....sadaka...gaida mara lafiya duk basayi saboda neman duniya to ni Khadija nagane gaskiya kuma insha Allah yara na zasu san wace ke muguwa azzaluma bantab'a ganin shaid'anun mutane sama da ku ba.
Mari Isma ta sakarwa Amma cikin k'ara ji tace ke mitsiyaciya 'yar mistiyata. Matalauciya wato an miki rana shine zaki mana dare.
Mun d'auka ka darajar ki shine zaki zo kimana ta 'yan garin nan koh an fito dake daga cikin talauci da k'angin wahala saboda kin zama mutum shine zaki yiwa mutane iskanci wallahi idan bakiyi wasa ba sai mu b'atar dake ke har wata tsiya ce mayya kawai...badan Baba ba taya ma zaki auri Saif....uwar taki mece ita har wata a bace da zai kiyi tutiya da ita..a k'asan mu take harta mutu bare ke.
Ke kul naji ni 'yar mitsiya tace amma kuma uwata batai bak'in halin ku ba. Kuma nima badan k'addara ba mai zai sani zama cikin ku.
Kune kuka nemi da na zo na auri d'an uwan ku ba wai nina ce ba. Kuma kunyi haka ne saboda kunsan kunshanye uwa ta ba zamuyi muku musu ko gaddama akan komai ma.
Shegu mugwaye asirin ku ya tonu duk sirrin ku ashe a baibai kuka sanar damu ba gaskiyar al'amari ba. Kuka saka nake bawa bawan Allah wahala ashe nima ba a banza kuka barni ba naji duk hiran ku a kwanaki kafin tafiyar mu. Nacewa nafara jiji dakai zakuyi magani na.
Ashe wajen bokan da muke zuwa duk maganin da yaban na ku mallakeni ne bana tsarin jiki na bane....kungama siyan sa da kud'i dangin jaraba.
Umma fa kanta ya juye bata gane komai ba illa kallo da take bin su da shi na rashin sani.
Umma idan zaki taho ki taho dan bazan zauna ba. Hannun Umma ta jawo sukai gaba amma gaba d'aya fa kan Umma ya kwance dan sun saka ta a wata duniyar tunani ta daban..
A mota sai hawaye Amma take sharewa na nadama sosai da dana sani har suka k'araso gidan..
Motoci suka hanga wajen guda goma ga soldiers da police ga kuma Mopal da wasu masu bak'in kaya a tsaye a k'ofar gidan.
Cikin Umma ne ya kad'a tace Amma su waye wad'an nan kardai wani abu yaran nan sukai mun shiga uku. Insha Allah ba komai mu shiga. .
Su da gidan su amma saida akai serching nasu before su shiga gidan.
Idanu suka ware ganin gidan cike da jama'a a hankali suka kutsa cikin parlor d'in kowacce jikin ta na mazari.
Yauwa gasu nan yanzu nake cewa ya gidan shiru Amrah ta fad'a bayan tazo wajen Iyayen nata.
Eh...Amrah lafiya mene nake gani?, Amma kenan abinda kuke boy'emana ne ya bayyana. Sirrin da kuke rufewa ne shekara da shekaru ya tonu duk jama'ar nan dangin Abban mune da kuma dangin Maman Maleek.
Mai farin ciki sai yayi wanda kuma baya yi saiya mutu. Amma naji bakin cikin kasancewar ki uwa ta ace har dake a masu kin jin tsoran Allah da girman ki Amma sai kuka.
Taufeeq ma kuka yasaka yana gayamata magana cikin masifa tace Ya ishe ku mana ya kuke so nayi kunason kashe nine ku barni da abinda nake ji.
Ku barni da fushin da ubangijin yake dani mana duk da ba'a cikin hayyacina nayi ba...ku barni na huta sai kuka.
Jikin sune yai sanyi jin maganar da take fad'a. Mrs President yace Taufeeq wato bakaji magana ta ba koh da nace kai shiru?, a'a Uncle kai hak'uri wallahi naji maganar ka abin ne da ciwo.
Sa Sauri Amma ta juya ganin mai maganar idanu ta bude tace President kaine?, itama Umma haka ta fad'a.
Seema ce tace Umma nasan bakisan komai ba amma inason yau zan ga yamiki abinda ke baki san dashi ba.
Aunty Safeena ma zata gayamiki komai. Wacce Safeena na kuma?, Fulani Maman Maleek tana nan a raye gata kusa dani.
Inalillahiwa Inna ilaihir raji'un dama ana mutuwa a dawo?. Ba'a mutuwa a dawo indai har an mutu. To ya akai ta dawo?, wannan magana sai anje a asibitin da Momy ta haihu sai aji yaya akai da Doctor d'in da aka saka ta kashe ta.
Ke Seema mene haka Amma ta juya min da kai kema kinason juyar min mene gaskiyar al'amari?.
Hmm ki zauna yanzu zakiji koma mene.
Labarin komai da ya wakana tundaga farkon auren Baba da Kakan su da kashe kakar su da tayi da kuma gudowar da tai har kawo yanzu da suke bada labarin saida suka gayamata har na Momy Safeena.
Ihun kuka Umma tasaka tace kaji la'ananniya wato ita din ba komai bace a wajen mu. Ashe shiyasa take son kashe Maleek tunda dole shine zai iyayin jagora ta ganin family nasa....amma Baba kin cuce mu ko dayake cuta ta k'are tunda gashi munga a halin yaran mu cikin aminci.
Ke kuma cutar da kikai Allah ne zai kama ki muguwa wallahi kotu ce zata rabamu kai amma dai wannan mata akwai makirci.
Amma itama cikin kuka tace wallahi yara na ku yarda dani bansan ba Baba bace kakar ku ba....wallahi ni kaina nida uwata tsaface mu tayi sai abinda tace.
Nima sai a kwanan nan nasan cewa bamuda alak'a da ita ta komai. Kuma ko da asirin ta ya tonu nice sanadi saboda labarin da naji nata da kuma inda duk ta binne komai da inda take watsa wannan gayen tunfafiyar duk nina lalata su.
A can bayan tsohon gidan mu ansaka abubuwa na al'ajabi wanda suke da rai sama da shekara Ashirin saidana fiddo su tare da Dan Asabe mukaje shine yakama su har bak'in zakara mai gemu da kuma Aku wadda aka rufe bakin ta ruf sai mujiya kaya dai wallahi ni naje d'akin da aka zuba su na saka aka yanka.
Na biyu akwai layu a jikin ta wanda su suke fitomata da gashin jikin ta koda ba lokacin fitowar su ba...ni naje na cire.
Duk wani kulli saidana karya shi da wanda tasani nayi da wanda mukaje tare wallahi saidana karya nayi kuka sosai jin abinda matar nan tayi.. nayi kukan kasancewar uwata k'anwa ga wannan azzaluma sai kuka.
Amma kinaso kice kema bakisan komai ba...to amma ai Maman ki tasani tunda tace su kad'ai suka sani.?
Seema tabbas uwata tasan wani abu amma ba komai tasani ba. Kuma koda tasan komai batada ikon komai akai tunda sun tsaface kowa.
Uwata k'anwa ce ga Baba amma uban su d'aya uwa kowa da tasa. Kaka ta taci wuyar Babar Baba bata jima ba ma suka rabu. Umma ta taso wajen Uwani duk da dai tana nuna banbanci amma ba sosai ba tunda tasami duniya miji kuma a hannun ta yake ba ruwan ta da Umma ta....amma fa aikin gida itace yawo kuwa ko k'ofar gida bata zuwa itace aiken duk Mama ta Ghana kenan tunda tare suka taso.
Har akai auren ta. Nikaina bansan ba uwani ce kaka ta ba saida mukaje dangin Kakata sannan na sani. Amma fa komai Umma na zatayi saida shawaran su dan suna gama da ita.
Kwatsam rana nan naga Baba gidan mu. Bataji ta baki na ba kota bakin uwata tace tamun miji d'an ta Saif. Gaskiya bana sonsa amma sanin waye shi yanada kyau yasaka na amince amma fa saidana sha sharad'i na cewa ba ruwa na da komai kada nasaka idanu akan komai.
Ita uwar sace komai tace yayi zaiyi....Kuma. kishiya ta za'a san yadda za'a juya ta amma dai na kama idanuna da bak'i na akan komai.
Wallahi Seema bansan ba Baba bace Uwar Alhaji saida Umma na zata rasu shekara 3 kenan nakeji abakin ta.
Nashiga tashin hankali sosai nace kenan batada gadon Alhaji amma taci....dama ba 'yar uwa Alhaji bace lallai muguwa ce.
Sosai Umma na tace nayi hak'uri akwai ranar kin Dillan ci da sannu zata ga k'arshen ta.
Tundaga lokacin nake taka tsantsan da ita nake istigfaar nake kaiwa Allah kuka akan ya bayyana gaskiya.
Amma ni uwata uba d'aya suke da Baba ba uwa d'aya ba. Kuma muma ba wai dad'in ta mukaji ba wuyar ta uwa ta taci.
Dan Mama na ta sakaye ne amma yanda naji taci wuya a gun Uwani da a hannun kakar ta take ganin anyi wa Baba aure yasaka ta dage sai an karb'o Umma na.
Aikin komai Umma nace aure ma da kyar aka mata. ...amma ita bata gayan taci wuyar su ba saima nuna wa da tayi dad'in su taji wanda duk aikin rufe baki ne.
Ku yarda dani Umma kema ki yarda dani kinga ai na dena komai sai kuka.
Tab aiki babba wato wanann matar ita duniya tasaka a gaba ba Allah ba.
Mr president dai shiru yai yama k'asa cewa komai. Tab idan baka mutu ba baka k'are kallo ba.Auta ce
More comments.....kowa ta fad'i raayin ta#Anatare sosai sosai ❤❤

ВЫ ЧИТАЕТЕ
NEENA MALEEK {COMPLETED}
Исторические романыHere are some little part of NEENA MALEEK Book...the story of an orphan Boy called Maleek....and his father's Family....get inside the story .