8 NEENA MALEEK

1.6K 127 5
                                    

Baba wai me kike had'awa ne?, Isma barni gidan can zan koma da zama nagaji da wasu abubuwan da suke b'ullowa gara na koma part d'in bayan gidan idan yaso ayi komai a gaba na wannan ko haya ne sai a saka ko ki zauna.
Baba to ba sai a saka marasa k'arfi ba?, babu taimako a tsari na nama tura aje a share mun gidan gobe zuwa jibi zamu tare....Allah ya kaimu to.
****
 
Aslam wai me za'ayi ne naga anata gyara a part d'in BAYA?, kakar kace zata dawo da zama. Inalillahi kace kawai masifa ce zata dawo....dariya Aslam  ya kwashe da ita yace aini inaganin ta dawo idan zata takuran barin gidan zanyi wallahi mata sai jaraba gashi yaran ta kaf sun biyo halin ta Abban mu ne kawai bayada masifa....dangin ta kaf suma masifaffu ne ai jaraba batayi ba.
Addu'a itace maganin komai...haka ne D'an small. Yauwa nace wacce school ka cike ma?, BUK. Ok nima haka me ka cike?, da medicine na cike...ohh gaskiya ka canja nifa ban wani son aikin likitoci kawai ka canja....ido ya d'an zubamasa kafin yace duk abinda kike so inaso kai mai zakayi?, ah ni ai business admin zanyi dan shine daidai dani.
Ok bara Aunty Seema tazo sai nace shi nake so...ok.
  A haf kai nashiga uku ni Umma....wannan yaro kagama da ni....da sauri Maleek ya d'ago ganin Umma a tsaye a kansa tana hararar sa....sannu Umma da aikin da zan miki ne?, kai babu abunda zaka mun kawai dai nace ne nashiga uku da kai ka kwashen yara da suna zuwa guna amma yanxu saina kwana biyu ma bangan su ba.
Ido ya bud'e dariya ce ta kwace masa yace Umma kenan kiyi hak'uri to...hmm shege sai aikin bada hak'uri wucewa tayi....shikam ko babu komai yasan Umma ta rage tsanar sa.
Rayuwa akace tana tafiya ne ba tare da kasan tana tafiyar ba saidai idan lokaci yai kagan shi kwatsam.
Aikin Baba yaci dan kuwa gaba d'aya babu wanda yak'ara tada maganar dangin mahaifiyar Maleek....abu guda ne dai ba tasa mu ba tusa k'in sa wajen Aslam da Seema.
Anyi baikon Seema inda aka saka biki wata uku kacal karkuso kuga murna wajen yaran gidan.
Afrah da Amrah kuwa tunda suka dawo basuda lokacin komai saina kai Maleek uguwan ni da wurare da yimasa hira....sosai Seema abin yake faran ta mata....wani bari guda kuma tana auna rayuwa babu Maleek idan tayi aure tunanin nan kad'ai shike tada mata da hankali.
Amma kam tayi jarabar wa Amrah akan tadena kula Maleek amma tace mata sam itafa yanxu ma tana fa son k'anin ta babu mai takura masa bare ita.....Afrah ma Umma tayi jaraba tace Maleek maye ne kaf ya lashe mata kurwar yaran ta.
Maleek sunyi jarabawar shiga jami'a inda ubangiji yabashi sa'a shida Aslam suka ci...komai nasu daidai farin ciki ba kama hannun yaro matsala d'aya ya za'ayi yafara zuwa....tabbas akwai matsala dan a yanzu Baba tasawa kowa ido akan sabgar sa..
Hatta kud'in da suke kashewa taso hanawa. ...saida Seema taimata tsaye akai tace mata Baba kud'in ki ko namu?, nan gidan ma fa bana ki bane...gaskiya bamu son takura indai har kinason abiki to kuwa kibar kowa yai rayuwar sa tana gama fad'a mata tayi gaba.
Cak Baba ta tsaya saboda jin maganar Seema. ...gashi babu wanda yaimata maganar batayi daidai ba...eh lallai akwai magana.
Nasan abinda zanmiki...waya taiwa bokan ta na China nan tagayamasa komai cewa yai taje bandaki idan taje tayi fitsari idan tai ta juya shi sau bakwai sannan tayi zagaye akan sa sannan tasha indai tasha to kuwa cikin matan sa da yaran sa babu wanda zai k'ara mata wata magana ta k'ask'anci akan komai.
Ai kam bata tsaya bata lokaci ba ta aiwatar da komai yanda yace mata....a daren ta tara yaran kaf suna zaune ta kalli kowa yanda taga dama sannan tace ina son magana daku.
Kowa cikin rawar jiki yace muna jin ki....wata dariya tayi tace daga yau babu ku babu Maleek d'aya kenan...Kuma gobe zuwa jibi zan kaishi Yobe almajiranci....badan yai karatu ba saidan yaje yai duk abunda yaga dama.
Zuciyar Seema ce tace fat....daga ita har Aslam...gara su Afrah basuji komai ba amma kasan zuciyar su akwai ciwo na rashin son ayiwa Maleek haka suma saboda aikin da tai ne yaci akan su...dan basu wani shak'u ba dama sosai..duk da haka they feel some how.
Kuna Jina?. Ke Seema kinada abin cewa? ,  a'a banda ta cewa.... Aslam ne yaja doguwar ajiyar zuciya yace Baba na raina wayon ki duk shekarun ki baki fuskantar komai...kina zaton wai son Maleek muke?, tab aini duk duniya gara kare da Maleek a guna.
  Kwarai kuwa Baba dan tun farko da banso Maleek ba da tuni yabi uwa duniya amma nuna masa son da muke ne yasa muka shiga jikin sa kunga ba yadda zaiyi yaso wani bayan mu.
Hakan da mukai kunga komai zamuce yayi yi zaiyi....Kuma komai zamu bashi ci zaiyi...ai baku fimu tsanar sa ba...dan da babu shi da tuni bamu san wani tashin hankali ba.
Baba ai idan har aka barshi yatafi wani waje to kuwa yana gaba da ganin dangin uwar sa...abu guda na yanke kawai yazama driver na yacigaba da aikin da yake mun tun da.
Duk inda zani yaci gaba da bina...na saki jiki dashi ne saboda kada yayi aboki ko yasamu wanda zai gayawa damuwar sa.
Tab amma kuna ja ashe ni kuka bari a wofi....ke Umma kinsan da haka amma kike bari na nake babatu akan son da suke wa Maleek?.
Duk maganar da suke yi a kunnen Maleek suke wanda gaba d'aya kuka ne ya kwace masa saboda bai zaci haka daga Aunty Seema ba ashe itama ta  suce?, sai kuka.
Tsawa yaji an daka masa ba kowa bace face Seema....dan uban ka dama  lab'e kake mana to shigo k'eyar sa ta tasa suka shiga parlor'n.
Masifa Baba dasu Amma da sauran k'annen Abban sa sukai tai masa shege wanda ba'asan da dangin sa ba....kaidai ka shiga uku kuka sosai yake a haka ya zauna.
Kai daga yau kaine zaka zama driver na....duk inda zani kai zaka kaini na koyamaka mota ne saboda nasamu mai kaini club da school....na koyamaka waya saboda ina daga zaune na ringa saka ka aiki.....na nuna maka gurare saboda kazama d'an aike na....tashi ka tafi kaje d'aki na ka wanken  toilet ka kwashen duk wani dirty kayan ka....Mai kama da aljanu.
Kuka ya fashe dashi sosai....Seema ma tsawa tayi masa.....haka ya mik'e yana rangaji yai d'akin Aslam.
Yana shiga ya kifa kansa a kan gado yanata kuka sosai... mene amfanin rayuwa ta...mene amfanin zamana a duniya sai kuka....wanda nake so duniya da lahira ashe sunfi kowa k'ina waxai soni waxai cigaba da ban kulawa sai kuka.
Nayi kaicon zuwa na duniya...nayi kaicon kasancewa ta a duniya...nayi kukan me yasa aka haife ni dama ban zo duniya ba..
Rigar sa ya cire ya yaga ta ya nad'a ta a fanka stool ya d'auko ya hau kai ya sak'alo wuyan sa na gwammace na mutu da naga wanda nake so fiye da komai zasu azabtar dani sai kuka.
Hawa yai ya rufe idanun sa..kalmar shahada yai nan ya ture stool d'in rigar sa kuwa nan ta shak'o wuyan sa....

Chaiii please Votes. ...comments and shares....#ina k'aunar ❤

   Poor Maleek.....yaban tausayi dama haka rayuwa take....👌

NEENA MALEEK     {COMPLETED}Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora