Aunty to ya akai Ya Jameel ya auri wannan matar?, oho NEENA shiya ganta yace yana so, hmm batada kirki halan waye uban ta?, yar minister of depence ce. Mts batada tarbiyya banga amfanin zaman ta a gidan nan.
Ina gani fa uncle ma a wani yankwane ta gaidashi ko baici darajan surukin taba yaci darajan shugaban k'asar su, wallahi NEENA haka ne sauran ma sun gane kinsan wasu tarbiyya ce basu samu ba tundaga gida shiyasa. Eh ko ta samu ko bata samu ba wallahi ba ta isa ta raina mun ku ba ita din wa useless kawai.
K'ofar aka kwakwasa.....saida suka nutsu kana suka bada umarnin shigowa...Uncle da kanka ashe kadawo?, murmushi yai yace naje nakasa aikin nabar amanar da aka ban tanata fushi banje da ita ba ba dole nadawo ba.
Jikin sa ta fad'a tace banyi fushi ba dan yau Aunty taban labarin ku....naji dad'in kasancewar Aunty da kai.
Dariya yai yace hooo wannan Auntyn naki tafiya surutu.....naga pics sunyi kyau..tawo muyi kaima.
Ya ya iya NEENA ce dolen sa ya tsaya sukai pics dashi. Zama yai cikin su sunata hira wani abin yai dariya wani abin kuma ya kad'a kai har akai kiran Sallah.
Fita yai dan yin sallah mu kuma mukai a d'akin Aunty wadda take ta riritani kamar kwai.
K'asa muka sauka saboda wayar da akai mana nacewa mu fito za'ayi lunch. Gayu nace a zuciyata sabida ganin matan Yayu na nai sunyi Cas kowacce tasha kyau.
Suma ana su b'angaren matar Ya Abdul ce tace da matar Ya Farhan sis yarinyar can na burgeni wallahi batada raini da yanda suke sonta hakan wallahi raina mu zatayi kuma babu nai cewa komai.
Wallahi Hakane shiyasa nima nake respecting nata...K'arasowa tayi kusa dasu taje tace hy Aunties ya kuke? shine kuka gudu gun mazajen ku kuka barni ni d'aya?, ayya ai gani mukai kema kin gudu gun Ummi shiyasa.....haka ne. Ina yaran ku?, sunje school amma anjima kad'an zaki gansu...yaufa weekend tun safe ke zuwa ne?, tun 7 ma sai 5 wallahi...
Baki ta dan tabe kafin tace ina Uncle shi ba zaizo ba? ynz kuwa zaki gansa yar gidan Dadan ta....dariya tai tace Ya Abdul zan had'a ka fa da Dada dan naga kanason tsokana ta da yawa.
Baice uffan ba sai kunnen sa daya kama kawai....kujeran uncle taje ta zauna ta kame kafin tace wai wa zaiyi Serving d'in mu?.
Kafin wani yace komai saiga Mr president ya shigo "Enye yar gidan Dada yau a kujera na aka zauna?, d'azu ma a ita na zauna.
Uncle yaushe zamuje Adamawa?, kedai yaushe zaki nidai banda lokaci saidai Ummin ki?, juyawa tai tace Ummi yaushe zakije?, a'a aini ko yau ya barni zani kodan na duba jikin Safeena.
Ummi wai bataji sauk'i ha har yanzu?, taji amma bawai sosai ba....ayya Allah yabata lafiya..Ameen.
Abincin suka fara ci....wajen kala ashirin a jere sai wanda kake so zakaci haka abin sha ma.
Ba taci da yawa ba ta mike tai wajen kayan kallo..MBC bollywood takai....dan dakuna fuska tai kafin tace Uncle zanbi Aunty Mimi gobe?, haba NEENA yaushe ki kazo gaskiya bamu gaji da ganin ki ba ki zauna next week saina kaiki?, Oo Ya Abdul nidai zani gaskiya.....naji amma...kiyi hak'uri wani week d'in.
Abba yace zamuje dake ne gidan abokan sa fa...chaii naje su basu zo ba haba dai wannan ma yarfi ne. Dariya Mr president yasaki kana yace Ummi kinji yar ki ai ba yaran zaki gaisar ba abokaina da matayen su....hmmm Allah ya kaimu.
Zaku ma kuje gidan su matan yayun ki sai a gaisa koh?, Uncle banson yawo fa kasani nidai babu inda zani ko zani ma bazani gidan minister ba....saboda me kuma itama ai yayar kice....aa ni bansan taba kuma bazani ba.....Ya Abdul ne yamata tsawa ke Abba yana cewa kiyi kina cewa a'a saboda bakida kunya?, hawaye ne ya zubo mata ganin yadda matar Ya Jamil ta sakarmata wani murmushi na mugunta...kallon sa tayi ta kalli Uncle kana tace naji zani amma jibi zan je Japan gun su Dada.
Tana fad'a tai sama abinta. Wayar ta ta d'auka hello Dada kana ina yau an mun tsawa bayan itace bata sona....cikin tashin hankali Dada yace waye ne yai miki wace kuma bata son ki?, itace Yaya ita wa?, matar Ya Jameel.
Oh God stop crying baby zanji dalilin da yasaka zai miki tsawa ko mu bamuyi maki ba sai shi...fad'a sosai yafara..Mama karb'a tai tace NEENA meya had'a ku da ita nasan halin ki bakida rashin kunya?.
Mama tun fa a London da sukaje Ya Jameel yake cewa ga matar sa ta gaishe ni...so ban bari ma ta gaishe ni ba nina gaishe ta....shine yace mata ga k'anwar sa nan duk abinda nake so tayi mun bayada kamata akan ta zai iya rabuwa da kowa itace last born d'in su bayan haka ni dashi mun tashi cikin rainon ki kuma munason juna.
Nan yai ta gayamata ta kula dani....shine yana fita ta juyo wai me nake dashi za'a ce akan na za'a iya rabuwa da kowa....Kuma ai mata tafi k'anwa...nikam nace saidai.idan k'anwar batada important wajen yayan ta.
Kinsan me wai saitace duk important d'in ta ba zatayi masa abinda mata zata masa ba...Kuma ita ba bautata tazo ba yanda akeji dani haka a gidan su akeji da ita saboda haka karma nace zan kamata raini...tundaga lokacin take harara ta bantab'a gayawa kowa ba har yau da ta saka aka mun fad'a.
Tab aikam wallahi bara na dawo Jamil saiya zaba....daga magana sai rashin jituwa yashiga tsakani..shi kuma.Abdul barni dashi yi hak'uri kinji kiyi bacci kada kanki yai ciwo....Tom Mama I Miss u.....more than u miss me no kuma dariya suka saka.
Suna gamawa wayar baccin ta tahau yi tama manta da wata Salma matar Ya Jameel.
A k'asa kuwa Ummi ce taketa masifa akan an tab'a NEENA....wallahi Abdul saina barmu ku gidan ku akan NEENA nima zan iya rabuwa da kowa...yarinya daga zuwan ta zaka mata tsawa ko ni danake uwarta banmata ba sai kai?, ai saika tsaya kaji dalilin ta nacewa bazata ba bawai ka hauta da masifa ba ahakan kake cewa ta zauna zaka kaita kasheta ma wataran zakai....tunda kai haka a matar wani bare matar ka.
Farhaan ne ya tashi gunta yaje yace Ummi dan Allah kiyi hak'uri bazai kuma ba kalla Abba magana yake miki fa kiyi shiru...hararen sa tayi tace sannu ubana ko miji na to naki na hak'ura ko na hak'ura kasan Maman ta bazata hak'ura ba...Abdul kaban mamaki wallahi....Ummi kiyi hak'uri kefa Maman muce bayan haka gaki first Lady....uncle ne yace rabu da ita ai zanyi first Lady nan gaba. ...ihu tasa wallahi ko last Lady ce bazakai ba bare first.
Dariya sukai....Abdul ne yace Ummi kiyi hak'uri wallahi ni badan wata nayi ba nayi ne saboda naga Abba yana magana itama tanayi amma kiyi hak'uri...uhmm kawai tace....Ya Jameel ne yace Ummi kiyi hak'uri bamu san meke tsakanin su ba Abdul kuma ba d'an Salma yai haka ba kiyi hak'uri...ya wuce Jameel a dai guji gaba dan kuwa ban fidda ran tagayawa iyayen ta ba su zaka bawa hak'uri..Mimi tana ina?, naje naga tasaka lock na buga naji shiru.....tayi bacci fa. Haka dai Jameel wani irin bacci kuma?, tab Uncle ai indai NEENA tayi kuka to kuwa bacci take a gaban sa....ita kuma haka halin ta yake.
Wayar sace tayi tsuwa Ya Abdul ne yai saurin matsawa kusa da Mr president yace Abba Dada ke kiran ka?, ok danna min.
Hello Yaya kana lafiya?, lafiya lou Dadan NEENA...hmm kaga Maman ta tasani gaba wai lallai yau zamu taho ita hankalin ta bazai kwanta ba NEENA na kuka...ohh kaga haka Ummi wallahi tagama tabara yanzu....kabata hak'uri kaji bacci ma take....insha Allah nama bata kasan mata sha'anin su sai a hankali..kwarai Allah ya kyauta.
Ummi kinji Yayar ki ma na can na cewa yau zasu dawo?, da gaskiyar ta ai NEENA kusan ran mu ce mai tabata sai ya shirya......ohh Ummi itama Salman yar ki ce ai?, yata ce amma kuma wata kusan tafi wata....ko da ace na haifi 'ya to matsayin NEENA yafi na yar dana haifa kaga kuwa ban had'a sonta dana kowa.
Shi dai Abdul shiru yai...haka aka gama cin abincin kowa ya tashi...Salma kam ranta a bace yake ganin yadda duk Ummi ta d'aga hankalin kowa....mts ita tasani gida ne babu mai kirata. ..ehe. haka yafada a zuciyar ta dan kuwa batajin zata raga wa wanda ya nemi ya shiga rayuwar ta....Nikam nace ayi dai mu gani.Auta ce love you all....❤
#AnaTare#AnaMuguntare sosai sosai #Masoyan juna...💜💙💝❤💛💖💚
![](https://img.wattpad.com/cover/123374325-288-k80845.jpg)
ВЫ ЧИТАЕТЕ
NEENA MALEEK {COMPLETED}
Исторические романыHere are some little part of NEENA MALEEK Book...the story of an orphan Boy called Maleek....and his father's Family....get inside the story .