27.
Gaskiya bazan ce komai akai ba mai yawa saboda duk abinda ya faru dani bana cikin hayyacina.
Abu guda nasani miji na na sona yana ban farin ciki. Koda na koma cikin dangin sa bai canja ba ko d'aya saima tattali da yake nunan. Banjin ta uwar sa ko 'yan uwan sa saboda basu nake aure ba amma dai banjin dad'in su ko d'aya.
Kodana haihu babu wanda yazo cikin su. Kwana na uku Alhaji yazo min da wata magana ta cewa Baba ba uwar sa bace....komai da yaji ya gayan bai b'oye min komai ba....daga ni harshi munyi murna saboda ganin mu d'in 'yan uwan juna ne...nan nagayamasa yawan dangin mu da kuma matsayin su sosai yai farinciki har yace idan 'yan uwa suka zo zaiyi magana ko kuma ina samun sauk'i zai kaini gida can Adamawa sai yai bayani.
Gaskiya wannan abun kawai nasani...saboda yana fita mikewar da zanyi naga wasu karnuka da magu na k'arshe harda k'adangare addu'a naso yi amma kafin tak sunyo kaina....daga nan bank'ara sanin abinda yake wakana ba. Idanun na dai sin hango min Baba da wata likita sunyi maganar mutuwa akaina....a haukan da nake ina fuskan tar wani abu....har tashin hankalin da kuka shiga iyakacin magana ta kenan sai ranar da nawa yi gari kuma a nan gidan.
Inalillahi wa Inna ilaihir raji'un wacce masifa ce wannan..Allah kamana maganin komai. Ameen Maleek ya fad'a amma hawaye baibari fuskar sa ba. Yana tausayin Momyn sa lallai duniya ba tsoron Allah.
Abban Momy ne yaiwa su Seema bayanin yadda aka kawo Safeena har ila yau da taimakon da NEENA tayi akan ta sosai. Godiya Seema kewa NEENA akan itace sanadi na lafiyar Momy.
Yakamata kowa ya tashi aje a kwanta kuma sai gobe. Sallama Mama dasu Ummi sukaiwa mazan kafin kowacce tabi bayan mijin ta.
Yammatan ma tashi sukai d'akin su da aka ware suka wuce. Seema ma wani d'aki aka bata wanda yake kusa dana su NEENA.
Maleek kam Momyn sa yabi baya. Tana shiga ta ganshi batama san ya biyo ta ba. Murmushi tayi masa tace a'a Maleek ina baccin?, Momy taya zanyi bacci bayan idaniyata suna d'okin ganin fuskar Mama na.
Hannun ta ya kama yace Momy kinsha wuya a duniya amma yanzu saidai labari kinma manta koh?, dariya tayi tace namanta kam amma ciwon mutuwar miji na yanzu nake jin sa saboda bansan ya rasu ba sai yanzu....Sai kuka sosai.
Daga shi har ita rungume juna sukai saida sukai main isar su sannan Maleek ya Kwantar da kansa a kafad'ar ta yace Momy Ina son ki wallahi kullum sainayi mafarkin ki yau gashi Allah ya bayyanan mafarki na ya zama gaske me yafi uwa dad'i a duniya? babu yaji ance yana juyawa yaga NEENA.
Hannu Momy ta mik'a mata gefen ta ta zauna suka saka ta a tsakiya. Momy shima fa Maleek yai rayuwa mara dad'i. Nan ta gayamata komai...sosai Momy tayi kukan halin da d'an ta ya shiga a baya..amma.nabu komai akwai lokaci.
Yanda suke kowa kansa ya kafad'ar a Momy haka bacci ya kwashe su har ita.
Aslam ne yace Yaya Taufeeq bara naga Maleek shiru naga sun shiga d'akin can. Ok duba shi yazo mu kwanta mana.
Baby wai ina NEENA ne tazo a kwanta fa. Halex kema banda abinki ai tana gun Momy jeki ki kirata idan acan zata kwana kuma.
Tana fitowa sukai kacibus da Aslam...harara ya watsa mata itama haka....kaga Malam mene na harara na?, ke da wani idanun kika san ana hararen ki? Kai ka sani kauce ni...wuce shi tayi shima bayan ta yabi.
Lailah tantabaru na wajen Momyn su...lallai bacci tare ma...ke keep quite kada ki tasamin Kani da wata muryar ki.....nima kai shiru 'yar uwata na bacci.....sannu mai 'yar uwa...hmm shi mutum sai magana.
Dake ma dai bani na kula ki ba...kece tun a airport kinga farin bafulatani kin wani nane masa....shewa tayi a hankali tace amma ka yanken....dani da kai wa yafi kyau?, zo a gwada to....nak'i ni sai gobe.
Ok bye sleep tight my heart....Sarai ta jishi amma bata juyo ba...itama fa tana jin wani abu akan sa. ..so yanzu idan yace kule da gudu zata ce Cas.
D'akin su ya koma yace yayi bacci saida safe....ok Asubah tagari all Sarki Family.
*******
Tun safe kowa yai shirin sa saboda 'yan Adamawa fa sunce suna hanya. Ummi kanta tagayawa wani yayan su governor ne a Sokoton kuma da shi da Kakan su Seema uwa d'aya uba d'aya.
Lokacin da yaji zancen Adam yayan sa...nan shima komai yafara dawo masa na mutuwar yayan sa da matar sa da ta gudu ai a daren shima yaiwa dangi waya kowa yace zashi dan babu zama.
11 daidai gidan Mr president yacika kaikace biki akeyi su Afrah sunzo matan su Taufeeq har su da mijin Aya Seema.
K'aton hole aka bude....addu'a aka fara kafin kowa ya bayyana abinda yasani game da ta'addacin Baba....dangi sunga jikokin d'an uwan su. Murna dariya kuka...dangin shi suke wannan yana wane wanann a murna..Sai rungume juna ake yi.
Yammata da yara duk cousins nasu Seema zagaye suke da su ana introducing kai. Alolo itace 'yar governor d'in tayi aure amma a kano..so itama Tazo taga dangin ta da suka b'ace.
Bayan kace nace da akai...su Afrah kuka suke ganin yawan dangin su da tuni saidai su mutu ba dangi. Amrah dai da Taufeeq Kukan su yafi na kowa yawa saboda harda uwar su a ciki. Tsargar kansu ma suke a gun saida wani uncle nasu ya nuna musu ba komai ai basu sukai ba.
Alhamdulillah masha Allah Allah shine abin yaban da godiya. Munsamu k'aruwa a cikin dangin mu ta yara har bakwai saboda haka mu k'ara godiya ga sarki mai kowa da komai.
Inason kuma mu cigaba da addu'a domin kariyar jikin mu. Duk da sihiri gaskiya ne kuma yaci annabin Allah guda bare mu Wanda muka shagala da duniya da ababaen cikin ta.
Muka fifita duniya akan komai...Mukeson kud'i mulki da kuma sarauta...bamu tunanin lokacin mutuwa ta yaya asiri bazai kamu ba....fatana da rok'ona mu dage da addu'a akan Allah yabamu rinjiyae akan mak'iyan mu...Allah kada yabasu ikon komai akan mu.
Abu naga ba inaso kowa yaiwa 'yar uwar mu Amina da mijin ta addu'a Allah yakai kabarin su. Saboda basu sami kyakyawar addu'a daga garemu ba tunda mun manta su daga yau kowa ya d'aukar min alkawari koda K'ulhuwallahu k'afa d'aya ce zakuyi wa Adam da Amina har ma da d'an su.
K'arshen magana ta anan shine naji wasu suna cewa zasuje kano sai anyi wa Baba kisan wulak'anci ko ai mata duka itada sauran yaran ta.
To ina warning d'in ku da kakkausar murya kada wanda yaje ko'ina. Indai alkhairi suka shuka zasu girba idan kuma sharri ne sannu zai koma musu, alhaki kwikwiyo ne.
Abu d'aya muka sani yaran mu basuda alak'a da ita bazasu koma gunta ba. Kuma gidan da take zaune na yara ne za'a sallame ta ta tafi ko'ina ne.
Dukiya zamu kwace saboda batada gadon sa. Matan sa zasu zauna a gidan...ita 'yar uwar ta idan ta gane kuren ta sai a hak'ura kowanne d'an Adam ajizi ne. Watak'il tun kafin haihuwar ita Amman Baba take tsula tsiyar ta.
Ita k'arashe tazo ta gani.....idan kuma bata saduda ba zamu raba yaran da ita. Wannan hukuncin na wane nida Mr president da kuma Sarki.
Wanda baiwa ba yana iya gyaramana tunda muma bada iyawa aka haife mu ba.Auta ce
VOCÊ ESTÁ LENDO
NEENA MALEEK {COMPLETED}
Ficção HistóricaHere are some little part of NEENA MALEEK Book...the story of an orphan Boy called Maleek....and his father's Family....get inside the story .