Gaskiya am so happy for seeing ur comments my sisters...much love my wattpad ppl #Anatare sosai sosai ❤❤
24
Kalmar babu wanda bata doka ba...tashin hankali nan jikina yafara rawa nace Mai nasara aure kai amma ba sanin mu mun shiga uku wace ita?.
Yar gidan wazirin Adamawa ce. Cak numfashi na ya d'auke bank'ara sanin inda kaina yake ba sai a gadon asibiti inda nai kwana biyar kafin na farfado.
Safeena tana zuwa dubani amma ko kallo bata ishe ni ba. Yara na suma bata samu kallon arzik'i ba..bare Amma dake tasan waye Mai nasara da familyn Maman sa yanda kika san Amina ce ba Safina ba sabida kamanin su da juna.
Tunda muka dawo nake cikin tashin hankali banda aikin yi sai tunanin mafita..shikuma k'ara k'aunar ta yake yi..Umma ma tana son ta uwa uba kuma Seema da ta koma sashin ta da zama.
Bance musu komai ba haka sukaci gaba da zama har wani lokaci da cikin ta ya kusan fitowa duniya...a watannin baya taje gidan su itama sunzo yar gata ce gaba da baya.BAKAR RANA
Ina zaune abin duniya ya ishe ni saboda Mai Nasara yafara hangen kamar sa da amaryar sa gashi Umma itama tana damun sa na kamanin su da ita.
Wata k'awata ce tace tazo inda take ce min mene taga na rame...dake mun yarda da juna nan na kwashe labarina kaf nabata ashe kaf a kunnen Mainasara.
Banji shigowar sa ba saijin duka nayi ta ko'ina yana kuka yana mun Allah ya isa...ball sosai yake dani inda ya tsirani da wuk'a sai nagayamasa ina dangin sa suke..kai naga ta kaina ranar.
Bayani nai masa...kafin nagama Seema taimasa waya akan Safeena na labour....mantawa yai dani yatafi inda take.
Nikam ina tashi waya naiwa Rahee nagayamasa....shima cikin fushi yace kwana na biyar banyi aikin nisan ta tunanin mutane akaina ba..Kuma sati yayi ban aske gashi na ba..Dole na fuskanci haka..amma akwai aikin gaggawa wanda zaimun inda zaiyi k'ok'ari akashe Safeena kota hauka ce..amincewa nai da maganar sa..
A can asibiti Safeena tasha wahala kafin ta haifi yaron ta wato Maleek....murna gun yaran gidan ba magana nan Mai Nasara ya manta wata magana da yaji yafara hidimar Safeena.
Kwana su uku a asibiti nikam tsoro yasaka ni kasa zuwa nida Amma amma sauran yaran suna can. Seema dai har makaranta tadena zuwa lokacin tana ss1 zuwa sss2 inajin.
A cikin kwana kin na samu rayuwa ta tadawo daidai...inda aka mun abunda yafi na dama.....Safeena na zaune itada Seema sukaga ta tashi tana zabura kafin wani lokaci sai hauka tuburan...tanata buga kanta...waya Umma tayi mun na gashi abinda ya samu yar Fulani...gaskiya so nayi ta mutu dan haka ina zuwa nasamu wata likita nace zan bata ko nawa ne ya za'ayi ta mutu...taso min gardama amma daga baya ta amince a daren Safeena ta mutu.
Wayyo hauka Seema Suman ta uku...Mai Nasara kuwa tunda ya yanke jiki ya fad'i baikara sanin kansa ba sai a aranar sadakar ukun ta.
Yayi kuka yai kuka sosai...yaran sa ba mutuwar ce tasasu a gaba ba cutar Mahaifin su. Nikam dai duk da Rahee yace yamun abinda ita kanta Safeena za'a manta da ita amma duk da haka tsoro nakeji na tunkari Mai Nasara....acikin kwana biyar da mutuwar ta ne nai Shahada naje gida
Wayyo aikin Matsafi yafi aikin Boka....wallahi Saratu nagayamiki baice mun komai ba saima k'ok'arin magana da yake amma yakasa...Dangin Safeena babu wanda yazo neman ta kamar yadda har yau babu wanda yazo neman Amina da ita kanta Safeena sabida na nisan ta kaina da rahmar Allah...bana wasa da k'a'idar Malami komai akace nayi zanyi indai dan nasamu duniya ce.
ABDUL MALEEK shine sunan da aka rad'a wa yaron...Seema itace uwar sa...komai itace take masa...gaba d'aya rayuwar ta ta koma gunsa. Cikin kwanakin kuma Mai Nasara naga yanason gayawa Umma wata magana dan idan suna tare nashiga sainaga ya nuna rashin jin dad'i..tsoro haka yasa na tare a gidan sabida shi.
Yanason Maleek dan Seema ta naimasa wanka zasu tafi gunsa. Madara katan biyar haka uban yabada kud'i aka siyo. Kowa yanason Maleek a yaran gidan.
Ranar da Safeena tacika kwana bakwai da rasuwa ranar shima Mai Nasara ya amsa kiran Allah..babu kowa a gunsa daga Maleek sai Seema inda yabata amanar Maleek yace yasan bazai rayuwa ba amma ta kula da Maleek wataran sanadiyyar sa gaskiya ta fito.
Mutuwar Mai Nasara ta girgiza kowa ba kad'an ba....gari ya d'auka..nikaina naji mutuwar sabida ko babu komai akwai shak'uwa tsakanin mu. Haka aka zauna aka fara karb'ar gaisuwa.
Ni kam cikin satin naje India inda na buk'aci amun aikin da Maleek zai mutu...anyi amma babu nasara..komai nasa ayi indai akan Maleek ne baya tafiya saima kauna da ake nuna masa....shawara d'aya na yanke na saka tsana tsakanin sa da kowa hakan zaisaka ya mutu dan bakin ciki da kuma yunwa.
Nayi naga nasara amma fa Seema babu abinda ya canja. Komai nata Maleek har yafara wayo....sauran dai babu su babu shi
Ko a rabon gado naso yin yadda raina yake so amma ina..Umma ta tsaya kaida fata saida akayi komai daidai...hatta Maleek saida aka fitar masa...shege wanda daga gani kasan yaron ba d'an halak bane...tsinanen yaro babu irin abinda banyi ba amma wallahi Saratu saima d'auka ka dayake yi....gashi yanzu ya girma asirin da nayi na tsana ya karye k'aunar nan dai ta da ta dawo da suke masa.
Saratu komai nawa yafara lalacewa dan yanzu wajen wata guda kenan inason aske gashin jikina amma ba dama...Bai fito ba gashi wataran sainai ta ganin Safeena tana cemun takusa zuwa gareni. Babban tashin hankali na ance duk ranar da Maleek ko su Seema suka had'u da dangin Kakar su to fa ranar asirina zai fara karyewa...banda tabbas d'in sun gani amma dai sun had'u koma a inane.
K'annen kakan su wato mijina Abban ku ina yawon ganin su a mafarki suna cemun suma suna nan zuwa na kashe musu d'an uwa ya na iya..jiki na yanzu wani hucin zafi yake uwa uba kuma bana iya bacci inason yi amma bana iyawa.
Saratu babu mafita dole zan koma Italy agyara komai.
Hmm gaskiya Baba kinyi kuskure...amma ke uwata ce bazan ce komai ba....Gaki ga Allah nan...cuta kincucemu kin rabamu da dangin mu wallahi kema zaki gani sai kuka.
Seema wadda tagama jin komai tas hawaye tun yana zuba harma yadena fita....da sauri ta fice sai cikin motar ta.
Kuka sosai take tabbas Baba shu'umace ko a labari bata tab'a jin wadda tai nesa da Allah kamar ta ba. Idan haka ne Maleek koda ba k'anin su bane d'an uwan sune?.
Biri yai kama da mutum shiyasa a kullum taga President saitaji tana k'aunar sa..uwa uba kuma Sarkin Adamawa ashe kakanin sune. To ni Seema ta ina zan fara nemo dangin kakan mu na b'angaren uba ko kuwa na nemo na Adamawa?.
Aslam ne yace Aunty Seema Sokoto zamuje dai...na Adamawa bamuda matsala tunda ga kama nan a jikin mu...Kuma munsan komai na sokoto ne Bamu sani ba.
Da sauri ta waiga tace Aslam ya akai?, naji komai ina part d'ina naganki zan miki magana naga kinyo nan..ganin ki tsaye tasaka nima na rakub'e naji komai.
Inalillahi wa Inna ilaihir raji'un Aslam ashe Baba ba kakar mu bace itace ta kashe mana kaka...Aslam wacce irin rayuwa ce wannan?, Aslam mu shiga uku gaskiya duniya ba amana..Sai kuka dukkan su.
Ina school d'in kaikuma?, an tafi strike jiya fa. ..aa nabar Maleek na shiri...to fa aikuwa dai bara na masa waya nima a radio naji.
Waya yaiwa Maleek akan yana ina?, Ya Aslam kaganni yau Hajar zatazo so yau zata nunan face nata shiyasa ma namanta ban gayamaka an tafi strike ba..ok nima shina bugo nagayamaka.
Kace munada manyan baki...munada issue anan amma ya zama dole muzo mu ganta ina zakaje?, No tace mun wai naje airport na d'auke ta...ok to ka biyo ta gida sai mu tai.
No problem....yanzu kuwa zaka ganni.Auta ce

ESTÁS LEYENDO
NEENA MALEEK {COMPLETED}
Ficción históricaHere are some little part of NEENA MALEEK Book...the story of an orphan Boy called Maleek....and his father's Family....get inside the story .