44 NEENA MALEEK.

923 44 0
                                    

Da gudu yai kanta yana Fatee na menene kafar ki ke ciwo kuma baki gayamin ba, dagowa tai cikin gajiya tace Dada kamani na zauna, da sauri ya tallafeta a jikin sa yasata, cikin tausayi ya dago fuskar ta yace Fatee na meke damun ki gayamin ko raina zai saki, bazan yafewa kaina ba idan wani abu ya sameki kinsan ina sonki,  murmushi tamasa na kwantar da rai tace Habeeby duk rikicewar ta mece kafata ce kawai fah, cikin sauri ya kalli kafar ta hasbunallah kinga fah ta kumbura, ai kafin tace wani abu ya sabata a kafada ya fita, Neena da tausayin Maman ta ya cikamata ciki harda hawaye amma ganin yadda Dadan ta ya nuna kulawar sa sosai hakan ne yasata mumushi tabi bayan su, acan yana fita kowa tashi yai yana lafiya?< hmm wallahi Yaya batajin dadi tai shuru kiramin doctor plx banoson rasa Fatee sai hawaye shi kansa president hankalin sane yatashi da sauri yaran har suna rige rigen fita kiran ta, Maleek ne yai karfin halin kiran dr d'in a wayar sa, aikam tanajin yadda president yabata umarni na gaggawa ai bata jira sungama gayamata ba ta kwaso a guje daidai anan ta hadu da mazan gidan, gaba daya zagaye dakin datake akai, itakam kallon su kawai take wani hawaye ne ya zubomata na jin dadi ko a yau ta mutu tasan tabar baya da kyau, ganin yadda kowa hankalin sa ya tashi, Neena kam ciki ta shige ayi komi gaban ta. Dr cikin ta tafaraa dubawa tunda already she's know Mama nada ciki, lafiya lou cikin ta jininta ne kawai ya hau kadan sai kuma dan matsala na ciki amma ba komi, drip tasamata sai allurai bacci ne yai bada da ita. Dr jikin mata na fah? tana lafiya fah, ke meke damun ta uncle yafada a tsawace, in ina tafra takasa fada domin ta gargad'eta, ganin takasa fada ne, yasa Neena cewa Uncle Mama ce tahana  a fada fah, wai idan aka sani baraka bata daman kula dasu Momy Safeena ba, zaka hanata sakewa ne shiyasa tahana afada. kamar yaya? Mama nada ciki tsawon wata shida. jiri ne yakusan kwasar su duka, me kikace?< abinda nafada shine gaskiya, kuka Dada yasaka na murna ya rungume Neen a. Amma Fatee bata kyautan ba meyasa zata boyen baiwar da Allah yamin? Allah nagode maka, Aallah kaine abin goodiya. kowa gun murna yafara harda rawa, uncle kam ba karamar murna yai ba ko a lokacin dayaji samun cikin Ummi bai murna haka ba. Mama kamar yaya ya dauketa ba matar kanin saba, saboda kirkin ta da kuma hakurin ta.
Momy Safeena harda rawa saida Dada yace kicigaba kinsan idan Fatee tagan ki fada zakuyi dan ni ba ruwa na, dariya akai. aranar ma su Aslam kusan rabin kwana sukai a gidan ana murna, Mama kam taga gta Mimi ana gayamata tazo, kowa cewa yake Mama me kike so?< mezakici, Ummi kam takasa ta tsare itada neena Dada ma haka tana motsi zasuce Mama lafiya tun tana dariya har sukazo suna bata haushi, fada tafara sannan aka barta, Neena ladan ya isa  kema ba lafiya kika cikaba tashi maza kutafi gida, kowa ya dau matar sa su kara gaba, haba kunsani gaba kamar wata sabuwar amarya?< saidatai haka ne sannan kowa ya kauce aka barta itada Daada. wanda daukan ta yai yana juyi yana murna, ayau takara yadda itace rayuwar Ibrahim ganin yadda ba kunya yake nan nan da ita.
oshhh My Malek irin wannna mintsini haka? yo Neena yau kinmatani shiyasa na mintsine ki, wace ni da mantaka ina murna ne sosai Mama na takusa mun kani, murmushi yai cikin ta ya shafo yace nima na kusa samun baby, muma zakace ai dana ne banaka ba, hhhhh d'ana ne kam, Neena Allah mai yadda yaso daga ke har iyayen mu babu mai laulayi kamar ba musu ciki ba, sosai wallahi ni kaina yadda nasan ana wahala a ciki banga hakan akaina ba, haka ne bakia su Ummi ba ma?, nagani mana. tashi maza kisha kankanar ki kada ki fara mun ihu cikin dare, jikin sa ta kwanta tace ina sonka, kanamin komaimna rayuwa ina kaunar ka, Allah yakaramanan zaman lafiya, Ameen.
sosai Malek yake gwadawa Neena kauna, duk wani abu datake so yana mata, ga Maman ta ma kullum cikin mata waya take me kike so, bakijin ciwo, komai dai sai sam barka. amaren su ma suna zauna lafiya kusan duk karshen sati sai sun hadu dan a gidan  mr president ake weekend duk sati, idan kagan su sai sun baka sha'awa. Aunty Seema ma mijin ta yadawo Abuja wayyo murna, wannan satin har ita akai zaman hira da kara sanin matsalar juna itada su Aunty Amrah da Aunty Mimi ga kuma Aunnty Saratu yar Baba datazo duk suna zaune anata hira. Aunty Mimi da Aunty Seema sun zama iyaye sune suke kara wayar wa da kannan su kai akan darajar aure da kuma kula da kai da miji.
Maama kunna mana  tv en can yau ana scope with raya ina son gani, dan allah kubarmana Arewa anayin ZAyra film din nada kyau Amrah tafada, hmm nikam ban kallo wallahi, haba Afrah kibari sunma kusa gamawa, naji uwar  naci, naji nima. hmm Allah a shirya ku kudai kullum  cikin fada Umma tafada dake tazo. ido suka ware jin bayanin da akeyi da kuma wanda suka gani. Baba ce da Isma da dayar yartata jikin su duka ya koma irin na biri fuskace kawai tasu, labaran ne yaci gaba, Assalamu alaikum masu kallon mu, wadannan wasu bayin Allah ne wadan da anrasa daga ina suke an tsincesu sama da wata uku a garin Jigawa suna yawo cikin daji gashi dai mutane ne amma Allah ya maidasu wata hallita daga cikin munnan hallitun da Aallah ai, gwamnati tai fakon su inda aka kamusu aka tsare su wajen wata biyu, basa magana amma lokaci bayan lokaci suna kiran sunan Maleek da Seema duk kokarin mutane nasuyi bayani sunkasa domin basa magana, ajiya kuma tsakar dare anje kaimusu abinci aka tarar da gawarwakin su Allah ya dauki ransu, ga wanda  yasansu saiyai kokarin zuwa dan karbar gawar su.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'uun itace kalaman da kowa na cikin parlour din yake ambata, Saratu kam kuka sosai takeyi kowa agun ma kuka yake ganin yadda Allah yaidasu, Seema kam kuka take tana nidai nayafemiki Babab duk da ni baki kaunata duniya ina zaki damu, Allah kaimana kyakyawannkarshe, Maleek dasu Aslam da gudu suka shigo turus sukai ganin ashe suma sun gani, Taufeeq da Tauheed kansu kuka sukeyi, anan kowa yace ya yafemusu, Umma ma da Ummi dai yafiyar sukai.
Maleek kam jikin Neena yatafi yai kukan sa maiisar sa, Momy Sasfeena kuwa kukan ma yaki zuwa bare tafadi kalmar yafiyar, amma ganin yadda kowa yace ya yafe itama ganin sakayya da baiwar da Allah yamata yasaka tace Allah yajikan ku nayafemuku duniya da lahira.
aAdaren akaiwa President bayani inda ya bukaci akawosu nan, Ummi kam tsalle tai ta dire tace wallahi baza'akamana annoba ba, asamu masu musu wanka acan a binnesu acan, kowa ma har Saratu bata bada goyan bayan akawosu ba, tunda ance doyi suke, aikam safiya nayi su Maleek sukai Jigawa acan akaimusu komi aka binnesu, rayuwa kenan ga karhen yadda Baba yakoma sunso duniya kuma sunbi duniya amma ga yadda duniya tai dasu. Jama'a kugane shi alkhairi duk inda kake yana binka ne, sharri bayada kyau, cutar dan musulmi ba kyau, duk daren dadewa Allah yana madakata zaisakawa wanda ka cuta, sunki Maleek sunso  su kashe shi Allah baiso  ba, sunso su tagayyara rayuwar sa amma Allah yace masa na'am baibasu ikon hakan ba, Allah kada kabamu zuciya ko kawar dazata kaimu ga hakala, Ameen.
                                        3 months later.
cirko cirko naga mutane abakinnkofar katafaren hospital din dake gidan president, Neena wadda cikin ta yafito sosai itadasu Ummi tsaye take ana addu'a akan Allah ya suki Maman ta lafiya, Maleek ne yazo yajata, Neena be patients mana insha Allah yanzu Mama zata sauka, addua kawai zaki mata. Dada kam yana ciki dashi ake haihuwar kowa na gun adua yake mata domin Mama abar soce ga kowa, budewar kofar itace tasaka kowa juyawa, shawul biyu aka mikawa president dayan kuma Neena, idom kowa ya bude twinc Mama ta  haifa, Neena kam kasa rike yaron tai illa Maleek data bawa shii ita ta Maman ta takeyi, mace ne da namji yara tubarkallah.
a dakin da taimakon Dada Mama ta shirya tsaf abinta. bacci ne a idanun ta amma bata bsh dama ba sai cewa tai ina Neena, aikam bata rufe baki ba saigata, hugging din juna sukai sunawa juna barka, sannu Mama kinsha uya wallahi amma yanzu ciwon kadan ne>?, kadan ne kam, sannu kisamu kiyi bacci ki huta.
Idan bakayi bani waje, kyauta ko ban fada ba kunsan sai anyi, jama'a ba adadi kow murna yakeyi, yara masha Allah kamar su daya da Neena, kullum suna gun Dada ko hannun Neena rowa sosai suke na yaran wataran sai Ummi tace ke zan mareki fah bawa mutane suganai, saidakowa yai dariya. yara sunci sunan Mr president da matar sa, mai sunan   Neena. anyi suna nagani nafada.
life move on, da wata biyu Allah ya sauki Ummi da Momy Safeena rana daya, waih hauka murna tsalle ba wanda baiba a family din sarki, Duk yadda zan kwatanta murnar jama'a masu kaunar wannan family d'in bazai fad'u ba, tabbas sunga masoyan su na asali, Su Amrah, Afrah dasu Seema uwa uwa Aunty Mimi damai gayya Neena sune kan komi. Maza ne duka yaran su masu kama daya kaikace mace daya ce ta kawosu duniya har mai sunan uncle jinjirin Mama duka da iyayen su maza suke kama. Neena ma wannan karon itace mai zabar suna, dan MOMY SAFEENA SUNAN ABBAN SU MR PRESIDENT YACI, SHI KUMA DAN UMMI SUNANN ABBAN SU UMMI DA MAMA, DA MAMAN TA MARIGAYYA, sosai ta burge iyayen ta da wannan sunan. Suma dai suna ne akai na abuga ajaridu da nunawa a gidan tv akai, naira tai kururuwa da tsalle na kuka yadda ake wasa da ita. Maleek yai murnar samun kani, kuma kamar su daya da kanin sa abinka da family masu kama da juna. Momy taga gata komai tare sukeyi, tana kaunar Mama dan Mama bata dauketa a kishiya ba ko daya.

auta ce. loading last page. ayi hakuri agurguje, love u, vote and share.......

NEENA MALEEK     {COMPLETED}Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon