32 NEENA MALEEK

1.3K 77 5
                                    

Mutane suka gani amma yanayin hallitar su wata ira a tsaye baza a iya cewa ga tsayin su ba.
A girma ba za'a iya kamanta su ba...layi uku ne aljanun kuma babu wanda yake hango k'arshen su haka suka fara bin jikin su suna shiga Layin tsakiya kuwa d'akin da Baba take shi suke shiga.
Baki yaa saba da fadin mugun abu bare ayi salati....aljanun nashiga jikin su sukuma suna sauya kama zuwa wata Hallita kamar monkey dan gashi har yafara fitowa a jikin su..nidai ganin inason tsora ta yasaka na fice da gudu....ai juyawar da zan basaiga su su ukun ba suna tsalle kamar Monkey ai daga ni har mai gadin gidan k'afa mai naci ban baki ba sai ihu da gudu.
K'ofa a bude take haka suka fice nidai nayi gabas sukuma kudu sukai...Ina haki natafi gidan su Maleek.
A shirye kowa yake Maleek yana tsaye kusa da NEENA hira suke d'an tab'awa..Aslam ma haka.
Idan kun gama fa kuyo sauri dan jirgi ya sauka mu ake jira Sokoto zamu fara zuwa daga nan sai Adamawa.
Munga ma fa....ok kowa yashiga motor. Cikin mintuna kad'an suka k'arasa filin jirgi inda basu d'auki lokacin ba jirgi ya d'aga sai Sokoto.
Dake akwai yan uwa sosai wanda suka taho tare dasu na Sokoto d'in sune sukai jagora wajen raka su duk inda yakamata sunyi yawo sun zaga dangi sosai....Su Umma sunga ainihin dangin mijin su...Momy Safeena ma haka ita kowa ya ganta yace Allahu Akhbar inda kasan Amina ce....sunyi ziyara gidan Sultan da kuma gidan waliyyai wanda suka gaba ta.
Daga nan sai Adamawa inda sunga kara sosai dangi kamar sun cinye su....jikokin Yafendo Amina da kuma yaron Safeena..haka dai akaita buduri naganin dangi har wani lokacin da komai ya lafa.

Abuja

A zaman da iyayen sukai sun k'ara sati biyu bikin Neena sabida Maman ta tace bata gyara 'yarta ba..Dole sai da aka k'ara....ita kanta NEENA taso a k'ara sati uku ma...Amma tunda aka k'ara biyun ma is ok.
Chadi takanas aka kaita inda akai mata gyaran jiki na gani na fad'a a kwana Bakwai ..daga nan sukai India acan daga ita har family friend nata saida akayi musu wani gyaran jiki wanda idan baka san mutum ba ba lallai kagane shi ba sabida kyan da sukayi.
Daga can kuma kowacce ta d'anyi tsince tsincen ta na abubuwan da suke so....komai na d'aki dama Ummi itada Aunty Mimi da Aunty Seema sune suka tafi China da England domin siyo musu kaya na gani na fad'a.
Dake kaf yammatan suna India bazasu dawo ba sai ana gobe za'a fara biki ko sauran kwana biyu.
Hatta card daga London Mama da Dada suka saka a bugo...Kuma sune da kansu sai Yayun ta suke mata rabon saboda ita din bata nan.
Zaune suke a wani Hotel dake Mumbai hira ake yi Halex ce tace ku wai ba zakuyi free wedding pics ba?, tab koma zamuyi aiba time bare ma naga baiso tunda baitab'a cemun yanaso ba. A'a gaskiya kuyi mana....ai k'auyenci ne wannan...ba yace zasuje Cairo ba?, kawai ya biyo ta nan sai kuyi anan amma ace NEENA guda bikin ta ba pics gaskiya a'a yakamata yazo kawai ayi.
Ai dole ma yazo tunda matar Babban Yaya tace ayi....dariya sukai. Ai kam waya Halex tayiwa Aslam tagayamasa....shima bayan su yabi yace insha Allah kuwa nan da jibi zasu taho ba zasuyi a 9ja ba gamma a fita abroad yan da komai zai tafi cikin gayu da nuna yaran mulki ne.
Koda Uncle yaji bai hana ba..saima cewa yai ayi mai kyau daga can suyi Saudi ayi a can....Momy Safeena dai dariya tayi tace Mr president wai kai baka hana abu ba saima kace ayi...to Safeena yara naso idan akace a'a anshiga hakkin su ne kawai abar su lokaci ne.
Kwana biyu da yin wannan maganar su Aslam da wani Aminin Aslam d'in sai Yaya Jameel suka tafi can India d'in.
Maleek kusan kasa gane NEENA yai saida tazo daf dashi nan d'in ma hannun sa yaji a nata kana ya farga....My NEENA wai kece dama....wow u look so muah...murmushi tayi masa mai k'ayatawar....kaima kayi kyau kamar na b'oyeka kada wata ta kalle ka....haba dai wane ni ai kinfini kyau sosai....kajika nidai nasan kafini kyau....suna wannan hiran suka k'arasa inda sukai masauki.
Mama tayi murna da zuwan su....saida suka huta kana Mama ta buk'aci sanin wane ne expert a wajen d'aukan photo...gayamata akai nan kuwa aka tafi dasu NEENA bayan an tsara mata kwalliya akaita d'aukan su.
Iya kyau sunyi....Ana gamawa akafara posting inda miliyoyin jama'a suka fara surutun nasu na wow wow wow saikace jiniya.
A washe gari ne sukai Cairo dama angama gyaran jikin. ..harda Mama akaje nan ma sunsha gayun su....daga Cairo visa suka samu ta Chicago....idan ba kayi bani waje free weeding pics ma a k'asar waje ake....sabon Salo. ...duk yanda naso ganin waye yafi wani kyau tsakanin NEENA da MALEEK sainaga nakasa sabida had'uwa ce kan had'uwa.
Maleek iya kyau yayi abu yazo ya hade da mutum d'an gayu kuma....ai ba magana.
Suma su baby sunyi pics nasu wasu tare ma sukai dasu Maleek d'in. Daga Chicago gida 9ja suka yo.
A 9ja gari gaba d'aya ya d'auka bikin 'yar President kowa kagani kallon free weeding pics yake....wasu su yaba wasu suce saboda k'arya dama ai ba'ayi wa d'an Adam gwanin ta....komai kai akwai mai kushewa.
Ta kano suka sauka inda gidan Aunty Mimi su sauka saboda k'ara shirya wasu abubuwan....kowacce abinci taci sannan suka bi lafiyar gado...saida suka huta ne ana wata hiran Neena tace nashiga d'ari..
Inalillahi ku namanta?, me fa?, ina k'awata Autar hajiya dana baku labarin ta yakamata na kaimata komai gaskiya banyi kirki ba....Bara na kirawo ta kuwa naji tana wanne unguwa.
Aikam tana kira aka amsa....nan sukai hira kana NEENA ta buk'aci sanin unguwar su...aikam gayamata tayi....nan da nan suka tashi motoci sunyi 20 aka jera aka tafi gidan su Auta.
Lokacin da suka je unguwar waya NEENA tayi mata tace tafito bakin titi suna gun....cikin abayar ta bak'a tafita titin unguwar su dan gidan su shine farko a coner tasu so daga titi zuwa gidan su ko 3 minutes bazakayi ba zaka fita.
Lokacin da taje motoci ne na alfarma zagaye da gun security ne kamar Hauka saboda taruwar mutane a gun.
Da kanta NEENA tafita saboda taga Auta na ware idanu taga ta ina zata ganta. .. k'ok'arin juyawa take saiji tayi ance Auta yada tafiya bayan gani. Cikin sark'ewar harshe Auta tace sorry Madam badai ni Autar ba...gani tayi mace hamshakiya....cikin gayu gashi taji ana yaran president ne dole ta diririce.. ke mana ta UBA halan baki ganni da Hijab ba?, nan dai ta dage itama ta dage saidaga can dai tagane lallai itace...aikam cikin sakin fuska suka k'ara gaisawa su Baby duk suka fito akai gidan su Auta.
Sosai suka zauna baran da sukaga itama akwai hira gata yar gayu duk da gidan su dai....but she's nice.
Dan kallon NEENA tayi tace sorry banda abinda zan baku. Haba dai bamu ruwa musha saikace wasu bak'in Hallita.
Pure water takamusu sai Cake aikam sunci....bikin ta ta gayamata kana tace mata tun jibi zata zo ashobe acan za'a bata.
Insha Allah zanzo amma Hajiya bata nan kada kuma....aa wallahi saikin zo ita kanta Hajiyar ai bazata hana ba..ko ma dai da safe sai mu k'ara zuwa gaskiya saikin je kodan ki bamu labari....murmushi tayi cikin muryar ta mai taushi tace insha Allah zan gayamata...yauwa ko kefa kutaso mu gudu aikin mu da yawa.
Har bakin mota ta rakasu kana ta juyo....aifa 'yan unguwar su kowa yace to ina Auta tasan NEEN....basuda amsa saidai zancen da gulmar.
Masha Allah akace komai yai farko zaiyi k'arshe duk abinda Allah yaso babu makawa saiya faru...duk son ka ko k'in ka da abu idan Allah yaso ya faru saiya faru.
Kowanne b'angare sun shirya yo dama ai b'angaren d'aya ne...Kuma kowa cikin farin ciki da annashuwa yake babu sauran damuwa ko kad'an.
Salma matar Ya Jameel ganin ba sarki sai Allah tana kuma son ta da kushewa kanta tauraruwa yasaka ta saki makamanta ta bada kai bori ya hau dan tabbas akan NEENA komai yana iya faruwa da auren ta hatta Mr president bayan 'yar sa yake bi.
Su Umma kaf d'insu Abuja sukai har 'yan Sokoto gari fa ya d'auka bikin yar gata ake.
Maleek dai abokan Aslam sune suka zame masa abokanai....Aslam da ya Jameel sune aminan sa....Momyn sa tana bashi kulawa sosai....da taso yin Al kunya amma taga ina son d'an ta ya rinjayi komai.
Saratu ita kanta ta hak'ura ta shiga cikin 'yan uwa ana damawa da ita...Yau itace ranar kamu.....inda akai a Katafaren Hole d'in dake gidan Mr president wato Villa.
Amarya ango....Kat kenan fadin kyan da sukai ba'a magana....dama tundaga India da Turkey aka d'auko masu kwalliya so kyau dai masha Allah anyi shi abin ba magana.
Anyi abubuwan Fulani sosai....an cashe an rak'ashe...Dollars sunyi kuka...dan ba Naira xance ba.
Matan yayun ta abin sai wanda yagani dan kuwa madaran da zallan kyau kowa yake a gun....

Auta ce

.sorry am too busy wallahi.....save the date 22 December my b'day..so tight ur bellet....it's Autares Day❤❤👌

NEENA MALEEK     {COMPLETED}Where stories live. Discover now