💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*NA TSANI MAZA*
💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*💫Na💫*
*💐Aysha Isa (Mummy's Friend)💐*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
_(Home of peace, honour and super writer's)__*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile's family & Exclusive Writer's Forum*_
_*Nasa rasa irin godiyar da zan maki komai nace zan fada sai nagan ki wuce hakan, ashe mutun yakan hadu da wanda baya k'ashin sanar da kai wani abu domin karda kafi shi watarana?., nikan na hadu da gwanata, 🅱K ki dad'e kiyi karko ina yinki irin sosai dinnan. Nagode, nagode, thank for the love.😘😘😘*_
_*Members dinnan exclusive writers forum masoyan kwarai a kullum soyayyar dad'a k'aruwa take a cikin zuciyata ina sonku irin totally, Allah ya barmu tare ya karemu da sharrin maqiya. Words alone cannot express how happy I am being with yhu guyz. Love yhu wujiga-wujiga❤❤*_
_*I dedicate this page to my dear 🅱K*_
_*BIMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
1⃣6⃣➡2⃣0⃣
*Ranar Juma'a da yamma*
Wasu 'yan mata biyu ne zaune a parlour suna hira, d'ayan cikin su a shakaru ak'alla zatayi sha biyar, d'ayan kuma bata wuce sha uku ba. Babban cikin tace "Jidda wallahi na K'agu ayi bikin nan."
Wacce ta kira da Jidda tace "Aunty Billy ina ganin nama fiki k'aguwa, kinsan fa wannan shine first time da za'ayi bikin aure a gidan mu, I can't wait to see that day. "
"Kedai bari kawai sai nayi inviting duka 'yan class d'in mu harma da 'yan islamiyya. "
"😳 kai anty sun fa yi yawa, nidai best friend d'inta kawai zan gayyata sabida in samu time din kwasar shoki💃🏽. "
Suna cikin hira Hameeda ta shigo parlour da sallamar kafin ta karasa inda suke zaune wani yaro wanda ba zai wuci 5yr ba ya shak'o da gudu ya d'ane jikinta. Rungume shi tayi daga bisani ta sauke shi suka zauna kan cushion d'in dake fuskantar su billy da Jidda.
Yaron yace "antyna oyoyo, I miss you. "
"My Khaleel I miss yhu too. Ya makaranta, da fatan dai kana karatu sosai ko?."
"Eh ina yi, rana nan ma Aunty mu ta siyar min biscuit wai ina da kokari sosai. "
"Yauwa haka nake so, give me five 🤚". Hannu ya bata suka sha.
Billy tace "ina yini anty. "
"Ina gajiya Billy ya kuke?" Hameeda ta amsa mata sannan tace "Jidda ba gaisuwa ne?"
Zunb'uro baki Jidda tayi tace " toh ba tun daxu inata gaida ke baki amsa ni ba. "
Tashi Hameeda tayi ta koma kusa da Jidda sannan tace "eyya kiyi hak'uri Khaleel ya cikani da surutu ko gaisuwar banji ba kiyi hak'uri kinji little sis".
Murmushi Jidda tayi ta sake gaidata ta tashi tace " bari in kawo maki ruwan sanyi".
"Ok sis, am waiting., "
Jim kad'an Jidda ta dawo da ruwa a kofi ta mik'a mata sannan ta samu wuri ta zauna tace "yauwa sis dama hira yanda bikin ki zai kasance muke sai gashi Allah ya kawo ki, so sis wat are your plans?. "
Murmushi Hameeda tayi tace "your plans are also mine duk abinda yayi maku nima yamin. "
Suna tsaka da hira Ummansu ta shigo tana fadin "wai muryan wa nake ji kamar ta Hameeda?. "
Mik'ewa Hameeda tayi daga inda take zaune tace "nice Umma. "
"Shine baki shigo kin gaidani ba ko saboda kisan zan tambayeki dalilin dawowar ki ko?. "
Risinawa tayi tana ba Umma hak'uri tace "wallahi umma ban jima da shigowa ba. "
Umma tace " toh me ya dawo da ke yanxu, inace next week zaki gama exam d'inki?. "
"Eh Umma amma bani da exam sai ranar thursday kuma ina kewar ku shiyasa na dawo. "
Umma tace " yhu better get use to it, ke da ke shirin barin gida gabaki d'aya".
Zunb'uro baki Hameeda tayi sannan tace "ai Umma zan ta kawo maku ziyara koda yaushe. "
Murmushi Umma tayi ta tashi daga zaune sannan tace "a ta ki wautar ba da shike shi mijin naki bashi da nayi kullum yabarki kina ziryan gidanku ba, in kun gama hiran ku kintsa ko ina kafin Abbanku yadawo ni na tafi d'aki."
Hameeda ta amsa mata da "toh umma" komawa tayi zaune suka cigaba da hiran su da k'annenta.
💐💫💐💫💐💫
Horn *RAYHANA* tayi a gaban wani gida mai dank'arin kyau, wani tsoho ne ya wangale gate din ta kunno kan motar ciki gidan tayi parking wurin ajiye motar sannan ta fito, ta k'arasa wurin shi a gajiye tace " Baba Iro ina yini".
"kin yini lafiya d'iyata ya makaranta?".
"lafiya kalau baba".
"Toh madallah Allah ya bada sa'a.
"Ameen baba" kud'i ta mik'a masa tace "baba ga wannan ka rike".
K'in karb'an kud'in yayi yace "rike abinki d'iyata ke da ki ke makaranta. "
*RAYHANA* tace " ai ba yawa baba sai dai in ka rena ne. "
Ansar kud'in yayi yace " 'Diyata ba renawa nayi ba, nagode Allah ya maki albarka. "A zuciyar shi kuma tausayinta yake saboda ita da mahaifiyarta duk mutane kirkine amma saidai kash *RAYHANA* batayi sa'ar uba ba.
"Ameen baba, nagode". Juyawa tayi ta nufi parlour tun kafin ta isa parlour take kwalawa Mami kira "Mami, Mami......"turus ta tsaya sakamakon abinda idanuwarta sukayi tozali dashi nan take hawaye ya fara zubar mata tana mai furta _"Innalillahi wa ina ilaihi raji'un , Allahumma ajirni fi musibati wa khalifni khairi minha._"
*Muje zuwa*
_Ko mai *RAYHANA* tagani ya firgita ta haka?._
Ku kasance tare dani domin samu amsar wannan tambayar.
_Domin shawara; gyara ko k'orafi kofa a bud'e take zaku iya samuna a lamba kamar haka._
*08146960525*
*Taku ce*
YOU ARE READING
*NA TSANI MAZA*
عشوائيLabari ne akan wata budurwa da ke ikiranin ta tsani maza, wannan dalilin ne yasa bata kula ko wani saurayin. Ko meye dalilinta na tsanar maza?. Ku biyoni cikin wannan labarin don sanin wannan dalilin.