💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*NA TSANI MAZA*
💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*💫Na💫*
*💐Aysha Isa (Mummy's Friend)💐*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
_(Home of peace, honour and super writer's)__*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile's family & Exclusive Writer's Forum*_
*Mumcyna kuma k'awata wallah bani da kamarki, da ke nake tinkaho, thanks for the support momma na. Allah yabaki lafiya mahaifiyata, may you live long to witness bikin kawarki 🙈. Words alone can't express my love for you, ina sonki sosai da sosai😘😘😘*
_*Na sadaukar da wannan shafin ga duk mai sunar momma watau HAUWA ina sonku*_
_*BIMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
3⃣1⃣➡3⃣5⃣
Zub'uro baki Hameeda tayi tace "Umma ina je fa sai tayi ta d'ura min wani abu ina sha, kuma wallahi Umma amai yake sani nidai ba zani ba sai ki mata magana ta daina bani su" ta k'arasa magana kamar zata yi kuka.
Umma tace " kaji min ja'iran d'iya, yoh ba ke akewa gata ba, toh in kin isa kiyi zamarki karda kije kin ji?, maza b'acen min da gani."
Tashi tayi tana guna-guni ta cika fam kamar zata fashe ta bar d'akin Umma.
💐💫💐💫💐💫
*Tuesday morning*
*RAYHANA* kwance a d'akin tana bacci da alamar baccin ta kwasheta ne ba tsamani domin rik'e take da takarda ga wasu kuma watse a gefenta. Mami ce ta shigo d'akin ta ganta kwance, matsowa kusa da ita tayi ta tasheta . Mik'a *RAYHANA* had'e da salati tana murza ido.
Umma tace "ba morning paper kuke da ita ba?."
Gyad'a mata kai *RAYHANA* tayi tace "eh Mami."
"Shine kika kwanta barci this already 9 o'clock ."
"Subhanallah" da sauri ta sauko daga kan gadon tace " tnx Mami har na kusan makara 11 muke da papern amma nayi dasu hameeda 10 zan shigo don akwai abinda zan koya masu." sannan ta nufi hanyar toilet.
Murmushi Mami tace " Allah yabada sa'a babyna kiyi sauri ki fito ina jiranki da akwai maganar da nake son muyi in kin fito."
"Ok Mami just give me 10mins."
*15 mins later*
*RAYHANA* ta fito daga toilet rik'e da towel tana tsane jiki, kusa da Mami ta zauna ta aza kanta kan kafadar Mami sannan tace "Mami na fito, aina cika alkawali ko!."
Mami tace " eh babyna, dama tambayarki zanyi ko mai ke damunki kwana biyun nane?"
*RAYHANA* tace " mami bakomai."
Mami tace "kamar ya bakomai alhalin daxun da nazo tashin ki naji jikinki da zafi kuma yanxu ma haka jikin naki da zafi, ina hankalce dake tun ranar friday kin canza daga yanda nasanki, kinsan dai baki da wacce tafini,ki fad'a min matsalarki may be ina da shawaran da zan baki , kuma kinsa damuwar ki nima yana sanyani damuwa, common my dear tell me wat ur problem is."
K'walla ne yaciko idanuwan *RAYHANA* tana tsoron ta fad'awa Mami taje tunkuran Abba cibi ya zama k'ari, don Abba zai iya bugunta ka n wannan dalilin koda a gabar kowa ne, ita kuma *RAYHANA* idan da abinda ta tsana bai wuci ta gan abbanta yana muxantawa Maminta ba. Ajiyar zuciya tayi sannan tace "Mami bakomai bane fa illa cikina dake ciwo amma tunda nasha magani yanxu naji sauk'i ko."
Murmushi Mami tayi don bata yarda da abinda *RAYHANA* tace ba sabida a duk lokacin da ta ganta a wannan yanayin ta san baya rasa nasaba da irin halin mahaifinta, tace "are you sure?. "
Gyad'a mata kai *RAYHANA* tayi tace " yes Mami."
Mami tace " toh maza ki k'arasa shiri k'arfe 9:30 ta riga tayi kuma nasan su Hameeda na jiranki, am off to work, Allah yabaku sa'a a jarabawarku."
"Ameen Mami, nima sai nadawo, bye."
Mami tace " ok my baby Allah ya bada sa'a, ni na tafi."
A gurguje *RAYHANA* ta k'arasa shiri ko breakfast batayi ba ta wuce saboda damunta da kira da su Hameeda ke tayi.
💐💫💐💫💐💫
Mami ce a office zauna tayi tagumi da dukkan alamu ta lula duniyar tunani, tunani take akan irin rayuwar auranta tun tana buduwar har zuwa yanzu da take matsayin matar mazinaci, azzalamin bawa, hawaye ne ya ke malala akan kumatun ta, " kaicona wallahi gaggawa a lamarin aure ba abu bane mai kyau".
*ASALIN MAMI**Muje zuwa*
ku kasance tare dani don sanin ko wacece Mami.
*Taku ce*
_*💐Mummy's friend💐*_
YOU ARE READING
*NA TSANI MAZA*
RandomLabari ne akan wata budurwa da ke ikiranin ta tsani maza, wannan dalilin ne yasa bata kula ko wani saurayin. Ko meye dalilinta na tsanar maza?. Ku biyoni cikin wannan labarin don sanin wannan dalilin.