💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*NA TSANI MAZA*
💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*💫Na💫**💐Aysha Isa (Mummy's friend)💐*
_*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile's family*_
_*Masoyana abin alfaharina,nagode kwarai da kulawanku,pls ku kara hakuri dani ina sonku sosai da sosai*_
_*بِسْــــــــــــــــمِ اللَّهِ الرَّحْمَ الرَّحِيْم....... *_
_*The Heart that believes and fears ALLAH Shall always have Peace & Contentment. May you and ur Family remain peaceful & contented forever. May Allah fulfil all our needs, may HE accept all our duas, remove our difficulties and Protect us from Shaytaan and all Evil..... Alhamdulillah it's Friday, remember the Sunnah's of the day, especially reciting Surat Al-Kahf……*_
_*Juma'at Mubaraq*__*BISMILLAHIR-RAHIM-RAHEEM*_
8⃣1⃣➡8⃣5⃣
Da sauri Mami ta iso gunta ta dafa kafad'arta sannan tace “ *RAYHANA* ina ke maki ciwo ynx?”
Mararta tai mata nuni da tana hawaye.
Pain reliever Mami ta d'auko daga first aid box ta mik'a mata “amshi wannan ki sha In Shaa Allah zakiji jikin da d'an dama.”
Ba musu ta karb'a maganin ta sha sannan ta kuma kwantawa ta runtse ido kama mai barci.
“Ina kika tafi tunda safe baki dawo ba sai dazu da wasu maza suka dawo da ke? ”
Gabanta yayi mugun fad'iwa tuni ta bud'e ido tafara i'ina “ummm mami daman…ummm.”
Wani irin tsawa Mami ta daka mata saida 'yan hanjin cikinta suka kad'a
“don't be stupid zaki fad'a min ko sai na b'ata maki rai.”
Jiki na b'ari ta kwashe lbrn kaf ta fad'awa Mami hatta irin shawaran da Hameeda ta bata, yanda suka yi da TJ yau.
Salati Mami tayi “ynx *RAYHANA* har kinyi girman fita da saurayi resturant ba tare da izini ba, ina laifin ki kawo shi gida kamar ynda Hameeda ta baki shawara, ynx meye riban naki na yin hakan?”
Hannu tasa ta goge hawayen dake kan fuskan ta, ta bud'e baki da niyyar magana kenan wayarta ya soma ruri alama msg ya shigo wayar ta, da sauri ta dau wayan ta ko numbar bata duba ba ta fara karanta msg kamar haka;
_*Ya masoyiya ta, hasken ruhina ina fatan kina lfy,ina mai baki hk'uri kan rashin jina kwana biyu wlh ina matukar kewarki.*_
_*Daga masoyinki har har abada.*_"Mtsw" taja tsaki nan take tafara hawaye tace cikin rawar murya “ubangijina baya barci nasan zai saka min.”
"Wai keda wa kike magana?."
"Mami shine wanda na baki lbrn dazu."
"Toh mai yace maki kike kuka kuma bacin abinda ya faru ya riga da ya faru ko sai ki dage da addu'a kuma ki tanadi bayanin da zakiwa mijinki in ya sameki ba budurwa ba."
Kuka *RAYHANA* ke sosai kamar ranta sai fita, mamakin Mami take wai maimakon ta rarrasheta amma ta fureta da fad'a. Wayarta ne ya soma ruri kuma, yi tayi kamar bata ji ba har yayi ringing sau uku, a na hudun Mami ta daka ma tsawa “zaki d'auka wayar ko sai na bata maki rai, meyasa kika bada numbar in baki buk'atar kiran?”
Cikin kuka tace “Mami don Allah kiyi hkr,wlh bansan haka yake ba kuma ynx bazan iya d'auka bane.”
Take tausayinta ya kara lulub'e Mami ta d'an sassauta murya tace “ok bani wayar”. Mik'a mata wayar *RAYHANA* tayi, tana mik'a mata wayar Mami tayi d'auka kiran tasa shi a handfree TJ ne yayi mgn daga dayan side din yace “hlo sexy.” Shiru bata amsa ba, dariya yayi yace "ya jikin ki?, wlh u got a good body structure don kin tara abinda mutun zai huta dashi, sai dai kash ban samu moren wannan garab'asan ba cx bana iya harka da mace cikin najasa. Kuma na soki ne sbd ko bakomai zan samu gun hutu, amma kash ynx bana iya aurenki sbd kin zama saura domin abokai na sun riga sun d'ana zumarki ko,sorry cutie sai a nima wani don dama ba don Allah nake sonki ba. In zaki iya tunawa some month back wurin baki kinma wani guy rashin mutunci, harda ikirarin cewa kin *TSANI MAZA*, sannan kuma yanayin shigarki a ranar shine yafara jan hankalin mu zuwa gareki. Kuma daga karshe karma kiyi wahalar kai k'ara sbd ko kin kai aikin banza kikayi domin wannan harkan ya zama kamar business ne gunmu koma kunyi nasara an kamu dole a sake mu, bye" dif ya kashe wayarsa nan take ya cire SIM ya karaya shi.
AB yace “kai amma guy ka burgeni fa.”
TJ yace “toh daman ance maka ni na yau ne.” Dariya sukayi sannan suka sha hannu.
*RAYHANA* kuwa tunda yafara magana tayi sumar zaune bata iya koda kwakwaran motsi ba sanda ya kashe wayar ta saki wani kara nan take ta zube summiya.
Da gudu Mami ta d'auko ruwan sanyi daga fridge ta shafa mata a fuska, firgit ta mik'e ta fashe da kuka “Mami abba ya cuceni ai tunda shi da ya mahaifeni ya iya min fyad'e kowa ma zai iya ya kwana lfy, Mami na shiga uku laifin Abba ya koma kaina, daman ance abinda kayi sai an maka, kaicona na……”
Rugumota Mami tayi tana shafa bayanta alamar rarrashi sannan tace “haba mana 'yarta ai komai yayi zafi maganinsa Allah kuma a duk lkcn da kike cikin damuwa ki ta fad'in innalillahi wa ina ilaihi raji'un, kuma nasha fad'a maki wlh Abban ki bai maki fyad'e ba, wannan kuma da ya faru ki daukeshi a matsayin kaddararki, kin ji my love.”
Gyad'a mata kai *RAYHANA* tayi had'i da murmushin da bai wuce kan labe ba amma a cikin zuciyata tana kwankonto haka, ita a nata ganin Mami na fad'an haka ne sbd karda ta tsani mahaifinta.
_*Babban magana*_
_Shinvda gsky ne Abba bai yiwa *RAYHANA* fyad'e ba kodai Mami na fad'a ne don ta kwantarwa da *RAYHANA* hankali?_
YOU ARE READING
*NA TSANI MAZA*
De TodoLabari ne akan wata budurwa da ke ikiranin ta tsani maza, wannan dalilin ne yasa bata kula ko wani saurayin. Ko meye dalilinta na tsanar maza?. Ku biyoni cikin wannan labarin don sanin wannan dalilin.