💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*NA TSANI MAZA*
💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*💫Na💫*
*💐Aysha Isa (Mummy's Friend)💐*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
_(Home of peace, honour and super writer's)__*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile & Exclusive Writer's Forum*
*Yaushe ne,yaushe zaki dawo Bilkisu, yaushe zaki dawo,😭😭😭😭 🅱K wlh ina kewarki, Allah yabaki lfy*
*Masoyan kwarai a gaskiya naji dad'in yanda kuke comment kan novel d'innan,nagode kwarai da soyayyarku, musamman ma NATSANI MAZA FANS GROUP, nima ina sonku, I love wujiga-wujiga, duk rintsi duk wuya ana mugun tare 🤝, Allah yabar zumunci😍😍*
*Ina kuke masoyan RAYHANA, RAYHANA na gaishe ku, musamma Hanan da Maman Sadiq, wai ince maku duk dad'i duk wuya ana masifan tare🤝*
*I dedicate this page to NA TSANI MAZA FANS GROUP*
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
4⃣1⃣➡4⃣5⃣
Anti Hanan tace " kwarai kuwa, wannan irin ramar da tayi gashi sai amai."
Hameeda tace "anti batayi aure ko ba fa, asalima ko sarauyi bata dashi sabida bata kulawa su, in kuma kika matsa mata son jin dalilin da yasa bata kula su sai tace maki wai *TA TSANI MAZA*.''
Ajiyar zuciya anti Hanan tayi sannan tace " toh baki ganin wani ne ya yaudareta yayi mata ciki shiyasa *TA TSANI MAZAN*?"
"Bana tunanin haka don da sabida hakan ne da tuni ta haife cikin ko sbd tun muna matakin farko a makaranta take da wannan akida ta tsanar maza."
Anti Hanan tace "Allah yasa hasashenki yazama..."
Kasa k'arasa maganar sakamakon jin fad'uwan abu juyawar da zasuyi suka gan *RAYHANA* kwance tana numfashi sama-sama, da gudu suka yo kanta amma karfin su isa ta suma.
Girgizata Hameeda ta shiga yi amma shiru ko gezau batayi ba, nan take Hameeda tafara kuka 😭 kamar ranta zai fita tace '"Anti na shiga uku ta mutu."
Matsowa kusa da ita anti Hanan tayi ta aza kanta kan kirjinta don jin ko da sauran numfashinta, tana aza kai taji tana numfashi, juya tayi gun da Hameeda ke zaune sannan tace " d'auko min ruwan sanyi a freezer."
Da sauri Hameeda ta d'auko ruwan ta bama Anti Hanan, wanke mata fuska anti Hanan tayi da ruwa sannan ta d'an watsa mata a fuska.
Wani irin ajiyar zuciyar tayi alamar ta dawo daga sumar da tayi kenan. Hamdala Hameeda da Anti Hanan sukayi, rik'e hannu *RAYHANA* Hameeda tayi sannan ta kira sunanta.
Bude ido *RAYHANA* tayi tq maida duban ta gun Hameeda da kyar take magana tace " na'am bestyna."Hameeda tace "da fatan jikin da sauki ko?"
Gyada mata kai *RAYHANA* tayi sannan ta maida ido ta rufe daga haka duk maganar da sukayi bata sake amsa masu ba sbd tsanin azabar da mararta ke mata.
Anti Hanan tace"Hameeda ina ganin zai fi mu tafi da ita asibiti don magance matsalar."
Kuyi managing wannan bana jin dad'in jikina.
_*Taku ce*_
_*💐Mummmy's friend💐*_
YOU ARE READING
*NA TSANI MAZA*
RandomLabari ne akan wata budurwa da ke ikiranin ta tsani maza, wannan dalilin ne yasa bata kula ko wani saurayin. Ko meye dalilinta na tsanar maza?. Ku biyoni cikin wannan labarin don sanin wannan dalilin.