💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*NA TSANI MAZA*
💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*💫Na💫**💐Aysha Isa (Mummy's friend)💐*
_*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile's family*_
_*My daughter like order, hope is you is doing fine, is this page is for ke kadai. Ki dade kiyi karko ana mugun. Love you dotalle Khadijah Salihu.*_
_*بِسْــــــــــــــــمِ اللَّهِ الرَّحْمَ الرَّحِيْم.......*_
9⃣8⃣
Bayan Mami sun gama tattaunawa da Abban RAYHANA d'akin RAYHAN Mami ta shigo ta zo ta sameta a kwance har lkcn bata daina kuka ba.
“Meye dalilinki na kuka yanxu, auren ne bakya so ko menene?”
Girgiza kai tayi tana hawaye “ mami banfa san wanda Abba zai aurar dani mawa ba.”
Zama Mami tayi kusa da ita sannan ta dafa kafad'arta “ Haba mana RAYHANA yanxu kina ganin Abbanki zai cutar dake ne , ko kina ganin ni zan iya cutar dake ne? ”
Girgixa kai ta sake yi. Mami tace “ toh ki share hawayenki ni nasan mijin da abbanki zai aura maki kuma na yarda da nagartarsa.”
Cike da da zumud'i sanin ko waye wanda ke shirin zama mijin ta RAYHANA ta goge hawayenta sannan tace “ Mami na bar kukan, don Allah ki fad'amin ko wanene shi?”
Murmushi Mami tayi “ kai amma ki fiya zumud'i wlh amma karki damu kin san ko waye anjima daddare in yazo zance zaki ganan wa idonki.”
“ Toh Mami.”
Da misalin k'arfe tara na dare RAYHAN yayi parking a haraban gidan su RAYHANA.Gaisawa da baba Iro yayi yasa ya masa iso gun RAYHANA. Jim kad'an sai gata ta fito ta isa gurinsa cike da mamaki tace “ oh sarkin naci daman kaine, tanan ka b'ullo?”
Murmushi yayi sannan yace “ barka da dare, da ftn kin yini lfy, ya Mamin da Abba?”
Shareshi tayi kamar bada ita yake magana ba.
Girgiza kai yayi had'i da murmushi sannan yace “ daman zuwa nayi wnt to knw ur shoe size and dat of undies?”
“ Bana buk'ata” sannan ta juya tayi shigewan ta cikin gida.
*BAYAN WATA DAYA*
Daidai yake da saura sati uku bikin RAYHANA shirye-shirye ake a duka b'angare biyu. Mami kuwa bata bar RAYHANA haka kawai ba sbd tunda a kasa ranar bikin take wa d'iyarta gyara don gudun samin wata matsala. Haka ma ya b'angare Hameeda, ga gyaran da Ummanta da Anti Hanan suke mata abin har ya ishe RAYHANA. Kowa na ganinta yasan amarya ce domin yanda tayi kyau sai shek'i take sai dai dan ramar da tayi.
Zauna suke suna hira su hudu Hameeda, Zee,Maryam da RAYHANA.
Zee tace “ yanxu RAYHANA kina nufin ko walima bazaki ba bare a kai ga sauran events.”
Murmushi RAYHANA tayi “ Zee bana buk'atan hakan.”
“Ai wlh baki isa ba duk events d'in da akayi a bikina sai anyi a naki” cewar Hameeda.
Maryam tace “ mayb angon nata ya hanata ne kinsan maza da iko.”
Tsaki RAYHANA tayi sannan tace “ toh ina ruwansa dani ai har yanxu k'arkashin ikon mahaifina nake.”
Murmushi Hameeda tayi “ nan da wasu d'an lkc ne zaki zama mallakinsa ai, nidai ba wannan ba wai yaushe zamu gun anti Hanan ne? ”
Had'a rai RAYHANA tayi tace “ gsky Hameeda wlh nagaji da wa'innan abinda anti Hanan take bani, ga Umma ga kuma na Mami duk ni kadai. Kashe ni ake son ayi ne?"
Dariya suka fashe dashi Hameeda tace “ ai lokacin aurana dariya kike ta min, so common lets get going.” Hameeda ta tashi da cikinta wanda ynx watansa shida.
Maryam tace “ ai is for ur own gud mudai mun riga mun san anfaninsa, watarana da kudin zaki siya.”
Tsaki RAYHANA taja sannan ta mik'e tace “ Allah ya raba ni da siyan jabara da kud'ina.”
*3 WEEKS LATER*
Ranar laraba aka gabatar da k'unshi da kamu a gidansu RAYHAN. Amarya tasha kyau sai shek'i take. Washegari da misalin k'arfe biyu aka gabatar da walima.
Ranar juma'a da misalin k'arfe uku aka d'aura auran RAYHAN SHAREEF da RAYHANA SALEH kan sadaki dubu 50 wanda ya samu halattar d'inbin jama'a. RAYHAN sai kargab'an gaisuwa yake kana ganinsa kansan yana cike da farinciki.
Ana iddar da d'aurin aure k'awayenta suka fara mata sharri Hameeda tace “ toh yanxu andai zama matar U. RAYHAN, dole ai masa biyayye, yau Allah yakawo mana k'arshen wannan akidar taki *NA TSANI MAZA*.”
Maryam tace “ yanxu muna buk'atar nan da wata tara muji kukan baby.” Suna tsaka da tsokabarta Mami ta aiko billy k'anwar Hameeda ta kira ta. Mik'ewa tayi jiki a sanyaye ta isa gun Mami, tana isa ta risina ta gaida wa'inda suke gun ta zauna. Wani abu Mami ta bata tace “ maza anshi ki shanye shi tas ynx ki bani kofi.”
Amsar kofin RAYHANA tayi tana hawaye ta karb'a kofi tana amshi kofin ta shanye had'in. Nasiha suka mata mai ratsa jiki, daga bisani Mami tace ta tayi tafiyata.
RAYHANA na isa d'aki kan gado ta kwanta, jim kad'an taji mararta yafara murd'ewa, ciza lebe tayi had'i da dafa mararta duk abinda take Hameeda na lura da ita. Mik'ewa Hameeda tayi daga inda take zauna tazo inda RAYHANA take kwance tace “ bestyna meya same ki.”
“ Marana ke ciwo.”
“ Period ne?”
Girgixa kai RAYHANA tayi tace “ bana jin shine bcox last mnth ma banyi.”
Murmushi Hameeda tayi tace “ In Shaa Allah matsalarki ya kusa zuwa k'arshe, mayb maganin da kike sha ne yake saki ciwon maran.”
Zaro ido RAYHANA tayi tace “ daman haka yake yi?”
“ Hmmmm aiki yake yi ciwon zai bari amma maganin na gun mijin ki.”
“ Amma Hameeda kinsan haka abin yake shine baki gaya min ba, kema dai kinsan ba son auren nake ba, yanxu ya kuke son nayi da rayuwata” ta fashe da kuka.
Hameeda tace “ haba mana RAYHANA toh yanxu meye na kuk, am sorry dear zai bari In Shaa Allah.”
Da misalin k'arfe shida na yamma 'yan d'aukan amarya suka parking k'ofar gidansu RAYHANA.
RAYHANA ce zaune gaban Abba sai kuka take yi kamar ranta sai fita, Abba yace “ bbu abinda zance maki da ta wuce ki rike gsky da amana, ki zama mace mai rik'e sirrin mijinta nasan halinki kina da hkr da rik'e sirri, toh ina son ki dad'e hkr akan waccen da nasan ki da ita. Ni Abbanki na yafe maki dukkan laifin da kika min, nima kuma ki yafe……” k'asa idda zance yayi sakamakon jikin sa da yayi tsananin sanyi “ ki tashi ku tafi Allah ya maki albarka.”
Gun Mami aka kaita itama Mamin kusan abu d'aya ta fad'a mata da wanda Abba ya fad'i ta d'a dacewa “ in har ni Laurat na isa dake inason kiyiwa mijin ki biyayye kuma ki sauke dukkan hakkinsa dake kanki, karda ki bari ya kawo min karanki.”
Kuka ne ya ci k'arfin RAYHANA ta tashi ta rugume mami tana kuka “ Mami ni na fasa auren, don Allah a barni nan.” Lallashinta Mami tayi itama tana goge hawayen da ke zuba mata itama a kan kuncinta tace “ d'iyata hkr zakiyi haka ko wacce macen ke fuskanta, nidai fatana Allah yabaku zaman lfy da zuri'a tagari, Allah kuma ya maki albarka.” Dak'yar aka yi RAYHANA ta bar jikin Mami.
*Da fatan yau bbu k'orafin daga gareku readers sbd na cika alkawarin da nayi maku*
YOU ARE READING
*NA TSANI MAZA*
RandomLabari ne akan wata budurwa da ke ikiranin ta tsani maza, wannan dalilin ne yasa bata kula ko wani saurayin. Ko meye dalilinta na tsanar maza?. Ku biyoni cikin wannan labarin don sanin wannan dalilin.