💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*NA TSANI MAZA*
💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*💫Na💫**💐Aysha Isa (Mummy's friend)💐*
_*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile's family*_
_*Pls readers kuyi hkr da errors dake littafin bana samun time din editing ne pls bear with me dudes🙏🏻.*_
_*BISMILLAHIR-RAHIM-RAHEEM*_
8⃣6⃣➡9⃣0⃣
Mami tace “yauwa ko kefa d'iyata maza tashi kije kiyi wanka ko zaki ji dadi jikin ki.”
Tashi tayi Mami ta tamaika mata ta shiga bayi ta gyara jikinta. Kan ta fito Mami ta had'a mata shayi, tana fitowa ta mik'a mata shayin tace “maza ki shanye sbd nasan halinki ina fita haka zaki kwanta baki ci komai ba.”
Turo baki tayi, goge hawaye dake zuba daga idonta *RAYHANA* tayi tace “Mami nifa a koshe nake bana jin zan iya cin abincin wlh.”
Mami tace “hmmm d'aurewa zakiyi ki ci abincin koda kad'an ne, kuma ina son wannan ya zame maki darasi a rayuwa komai k'ank'anta dan adam ya wuce wulakanci, kuma ki zama mai tauna magana kafin ki fad'eshi musamma a cikin jama'a zai iya kasancewa wanda kika yiwa maganar bai ji zafin ta ba amma wani a gun yaji zafin maganar, abu na k'arshe kuma da zan fad'a maki shine kisan irin shigar da zaki ringa yi in zaki fita anguwa sbd yanayin jikin ko mace taganki zata yi sha'awarki ballanta namiji don haka kiyi kiyaye gaba, Allah kuma zai saka maki wannan cikin mutunci da suka maki.” Matsowa kusa da ita Mami tayi ta kwanta da kan *RAYHANA* bisa k'afarta sannan tace kamar mai rad'e “yanxu dai sai a rage jan aji don ina buk'atan suriki, Allah ya maki albarka.”
Kare fuskarta *RAYHANA* tayi da hannun cike da kunya tace “Mami na, amma ynx wa zai aure mace irina?”
“Shhhh! kar na kara jin kin fad'i haka akwai wanda rayuwar shi tafi taki muni kuma sun samu mijin aure ballanta ma ke, kedai ki dage da addu'a nima zan tayaki.”
“Nagode Mami.”
Murmushi Mami tayi sannan ta dagata daga cinyarta tace “maza kin shanye shayin ki kwanta dare yayi, saida safe.”
💐💫💐💫💐💫
*BAYAN KWANA BIYU*
Zubair da *RAYHAN* ne zaune a haraban gidan Zubair suna hira, Zubair yace “kai nifa na kusan zama baba fa.”
*RAYHAN* yace “ bangane ba kana nufin Hameeda na d'auke da juna biyu kenan?”
“Eh mana da zan tsaya jiran kane, wai kai har ynx baka samu mata ba ne?”
“Hmmm, wlh kai dai bari kawai k'awar Hameedan ce har ynx na k'asa cireta a zuciyata gashi tamun kashedi wai na daina zuwa gunta amma kasan me?”
“A'a sai ka fada.”
*RAYHAN* yace “kullum fa sai na mata text amma na boye numbata.”
“Mtsw” Zubair yaja tsaki yace “amma anyi wahalalle, meye anfani boye numbarka to ynx taya za'ayi ta gane kaike aika mata da sakon har ya kaita ga maida martani?”
*RAYHAN* yace “wlh Zubair na rasa mafita ne kuma bana son ta sake min wulakancin da tamin a baya, pls ko zaka yima Hameeda magana mayb she can be of help.”
Zubair yace “bbu abinda matata zata iya yi kan wannan magnar, ai nima bakai ka tayani niman ta ba.”
*RAYHAN* yace “Zubair kasan bani da kamar ka, don Allah ka taimakamin wlh is affecting me.”
Zubair yace “ok I will tink abt it.”
wannan kenan
YOU ARE READING
*NA TSANI MAZA*
De TodoLabari ne akan wata budurwa da ke ikiranin ta tsani maza, wannan dalilin ne yasa bata kula ko wani saurayin. Ko meye dalilinta na tsanar maza?. Ku biyoni cikin wannan labarin don sanin wannan dalilin.