66-70

436 23 0
                                    

💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫

*NA TSANI MAZA*

💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫

        *💫Na💫*

*💐Aysha Isa (Mummy's Friend)💐*

*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile's family.*

_*🎻🎻🎻💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 cuta ba mutuwa bace da maganinta da maganinsa,sannan ba mai warka da cuta saidai Rabbi Allah,cuta ba mutuwa ba samun ta daga Allah ne watarana sai labari. Alhamdulillah gashi yazama labari Rabbi ya bama my mentor lafiya, ubangiji ya dad'a lafiya yasa anyi dace da maganin kenan. Allah yabama dukkan musulmai lafiya. Welcome Bilkisu Ya'u 🅱K.*_

_*Readers please in kunga mutum yana son kauce hanya a rubutun sa please kubishi private chart ku masa gyara ba wai kuje groups kuna cecekuce akansa ba, kusani we writers just like you guys and we a prone to mistake. Ni Aysha am always free zaki iya biyoni private chart ki min correction, ko kuma shawara (08186212985).*_

_*Momma Ubangijj ya baki lafiya ya ja da nisan kwana, my everlasting lover, my best friend, my …………, gosh words alone can't express how much u mean to me. May you live long to see your grand children from your dearest friend🙈.򒀊I love you whole heartedly.*_

_*Ban manta kuba 'yan uwa rabin jiki*_
_*Hajjo*_
_*Hafsi*_
_*Aunty Aysha*_
_*Aunty Hauwa*_
_*Zeeyan*_

_*Tnx for the encouragement, ina sonku irin totally❤*_

_*Ina son ku masoyana, kuma kusani duk wuya ana mugun tare🤝.*_

_*I dedicate this page to you 🅱K, kiyi yanda kike so dashi*_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM*_

6⃣6⃣➡7⃣0⃣

Bilkis ce ta k'araso gun a guje tana waige-waige ko zata gan motar *RAYHANA* amma har ta k'araci dubanta bata gan motar a gun ba.

“Mtsw! dana fad'a mata tare zamu koma gida, ynx dole a gida xan kwana,nida naso kwana gidan Aunty Hameeda.” Cino baki tayi tana tafiya sai magana take da kanta, daidai zata shiga hall TJ yace “enmata don Allah tambaya muke.”

“Allah yasa na sani.”

“In Shaa Allahu kin ma sani,please number sistet ki muke son kibamu.”

“Kana nufin Anti *RAYHANA*?.”

“Eh ita.”

“Toh!da ftn ba wani tayi ba.”

“A'a ba laifi tayi, daman last week ne da taje shagon mu shopping ta manta da ATM card d'inta.”

“Allah sarki toh ina katin yake nakai mata.”

Susa kai yafara alamu rashin gsky don rasa abun fad'i yayi, Tboy ya amshe maganar  da sauri yace “wlh mun manta da katin ne, don ko zaki d'an taimaka mana da number ta in yaso sai mu kira mu kai mata har gidan.”

Jim tayi tana nazarin maganar tasu, daga bisa ta basu number tayi tafiyarta. Sai da suka bari ta shiga hall sai suka fashe da dariya tare da shan hannu.

AB yace “kai baba ka sofa ka kwaftsa, in ba don Tboy da ynx ka jaza mana asara.”

“Kai dai bari ai shiyasa nayo sauri karb'e zance,ynx dai bari nayi saving number d'inta sai a bata hutun kwana 2,kunga lkcn ta riga da ware daga gajiyan biki ko.”

AB yace “ban k'i taka ba amma gsky na k'agu in lasa wannan zuman.”

Tboy yace “kwantar da hankanlinka zaka sha zuma har kaji ta isheka domin da dukkan alamu 'yar hannunce,yanayin shigarta ya isa ya tabbatar ma da haka.”

Murmushi TJ yayi wacce tafi kama da yake sannan yace “gwamma dai mun bi a hankali don na haga alamu rashin nasara.”

“Wai wani irin magana kenan nifa na kula kamar kana mana bak'in ciki da wannan yarinyar, dad'in abin ba kai d'aya bane Tboy ma ba wasa a wannan fannin na tsara mace.”

“Dallah rabu dashi mudai sai mun d'ana.”

Murmushi TJ had'i da jirjixa kai ya tashi ya koma hall.

Wannan kenan.

💐💫💐💫💐💫

*Bayan Wata uku*

Abubuwa daman sun faru a wa'innan watannin ciki har  kuluwar soyayya mai tsanani tsakanin *RAYHANA* da Tijjani wato TJ. Domin tun bayan bikin Hameeda da sati guda yake kasheta da salon sakon syyr 2ru sms tun bata damuwa har yakai ga in bai mata sending sakon ba sai ta tsince kanta cikin matsanancin damuwa.

A gefe guda kuma *RAYHAN* shima yana ta zuba nashi salon amma kullum numbar a b'oye. Ita kuma Gimbiyar tana zaton duk mutun d'aya ke mata wannan zafafen kalaman amma a zahirin tafi fuskanta tashi hankali in bata gan sakon unknown sender ba.

Zauna suke, su uku suna hira amma banda Hameeda, suna tsaka da hira sai ga Hameeda ta iso rike da ledan awara a hannu tana ciki,Dariya *RAYHANA* ta fashe dashi tace “Sannu besty yau kuma da kwad'ayin awara aka zo, Allah dai ya raba lfy ko zamu samu sararin wannan kwad:ayin.”

Hameeda taja tsaki sannan “Gwamma ni ai, in fitsari banxa ne kaxa ma tayi……”

Kan ta idda magana wayar *RAYHANA* tayi kara alamu msg ya shigo wayar ta fidda daga bag d'inta fuskarta cike da murmushi domin kuwa ta sannan sako ne daga annurinta wanda idanuwarta suke muradin tozali dashi, sakon ta fara karanta kamar haka:

_*Assalam alaikum ya ma'abociyar kyau da kamala, bazan iya rayuwa daidai da minti guda ba tare da ke ba, saboda kedai ce a cikin zuciyata, bana son na rasa ki, ki soni kamar yanda nake sonki don in na rasa ki rayuwata tana cikin garari. Ina sonki *RAYHANA*._

  _*Daga mai sonki har abada.*_

Lumshe ido tayi tare da ajiyar zuciya.

Kallonta suke cike da mamaki sbd basu taba ganinta a wannan yanayin ba, Hameeda ce tace “ke lfyarki kuwa?”

Shiru *RAYHANA* tayi bata amsata ba, fisge wayar Hameeda tayi ta tashi da gudu sai a sannan *RAYHANA* ta bud'e ido ta bita a guje tana  fad'in “pls ki bani wayata, kin dai san ba ke d'aya bace ko, karda ki jaza wa bawan Allah hasara.”






pls manage dix.

*Taku ce*

_*💐Aysha Isa (Mummy's friend)💐*_

*NA TSANI MAZA*Where stories live. Discover now