💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*NA TSANI MAZA*
💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*💫Na💫**💐Aysha Isa (Mummy's friend)💐*
_*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile's family*_
_*I dedicate this page to you bestyna Halissa.*_
_*بِسْــــــــــــــــمِ اللَّهِ الرَّحْمَ الرَّحِيْم.......*_
9⃣7⃣
RAYHAN na isa lokacin tara da rabi d'akin Ummee ya nufa kai tsaye ya iske tana nad'a sallayar da tayi sallah dashi da alamu tayi shirin kwanciya ko, sallayar ya amsa ya ajiye a maxauninsa had'i da gaida Ummee da gida. Gefen gado ya zauna har Ummee ta k'arashe shirinta “ Lfy yayan Yara, kamar da magana a bakin ka.”
Sosa kai RAYHAN yayi sannan yace “ Ummee daman yarinyar da nake nima ne a gidansu akace na turo da magabata na.”
“Toh madallah, daman abinda nake jira kenan. Bari na kira kawunka na gaya masa in yaso nan da kwana biyu sai aje ko.”
“Uhmm nagode Ummi Allah yaja da nisan kwana‘’. Kud'i ya ciro daga aljihunsa yace “ Ummee ga wannan aba wa kawu ko da abinda za'a buk'ata. Sai nadawo.”
“ Allah ya tsare ya bada sa'a.”
“Ameen Ummina.” A bakin k'ofan d'akin Ummi ya ci karo da Intee har ta d'an bigeshi sbd bata san da fitowarsa ba.
Murmushi tayi ta gaida shi sannan tace “ sorry ya RAYHAN, wlh bansan da fitowar ka ba.”
Karan hancinta yaja yace “ok lil. sis ykk?”
Turo baki tayi tace “ ya RAYHAN ai ka daina sona.”
Zaro ido yayi “ Subhanallah Inteena kin taba ganin yanda aka raba hanta da jini?.”
Girgiza masa kai Inteesar tayi, “ toh haka zamu kasance ni dake da Kamal har da Shuaib, mutuwa ce kadai zata raba mu da ku In Shaa Allah.”
Inteesar tace “ Ameen yaya amma ai ya kamal da ya Shuaib sun fi sona tunda kullum sai muyi waya da su, kai kuma yanxu na daina ganin ka kuma inna tambayi Ummi sai tace kana gidan ya Zubair amma ni ka k'i kaini.”
“ Toh sarkin k'orafi yi hkr.”
Murmushi tayi tace “sai dai in zaka kaini sch.”
“Ok, amma fa ni nariga na shirya ko.”
“Ai nima na gama ko‘’ daga inda take tsaya ta kwalawa Ummi kira tace ” Ummi na tafi sch ta RAYHAN zai saukeni a sch.‘’ Ko jiran amsa Ummi batayi tabi RAYHAN a baya.
A mota ta sameshi zaune ya jiranta, tana shiga yafara tuki suka bar gidan. Shiru suka yi for sometime tana ganin shirun yayi yawa tace “ yauwa ya RAYHAN wai don Allah yaushe zaka kawo mana anti mu ne, wlh na k'agu kayi aure nima na samu 'yar uwa ka………… ”
“Shhhh sarkin surutu wai ke baki gajiya da surutu ne?”
Turo baki tayi tace “ toh shi kenan ” ta had'a rai bata sake masa magana ba kuma.
Yana ganin haka yace “ haba autar Ummi ynx fushi kike dani?, dont worry very soon zanyi aure jst keep praying for me.”
Murmushi tayi tace “ ai ina tayaka yayana, Allah yasa ta soni.”
“Ameen lil. sis” daidai lokacin da ya kai haraban makaranta .
Sauka tayi daga motar tana waving nasa shima waving d'in ta yayi “ take care lil. sis love you.”
*BAYAN KWANA BIYU*
Hameeda ce zaune tana korowa Mami bayanin yadda sukayi da RAYHAN har da shawaran da ta bashi na turo magabatar sa.
Ajiyar zuciya Mami tayi tace “ Hameeda hak'ik'a kin cika masoyiyar kwarai, kin fi k'arfin k'awa a gun RAYHANA, ubangiji ya barku tare, ya kare ku daga sharrin shaid'an.”
“Ameen Mami.”
“Yanxu yaushe zuwan nasu zai kasance don na sanar da Abbanku.”
“Bai fad'a min ba amma bari na kira na tambayesa.” Numbar RAYHAN tayi kira ya shiga har ya katse bai d'auka ba.
Mami tace “ ko kiran bai shiga bane?”
“Ya shiga sai dai ba'a daga ba,inajin bai……” kafin ta idda magana sai ga kirasa ya shigo, d'auka tayi suka gaisa sannan ta tambayeshi ranar da za'a kawo gaisuwa. Suna kamala wayar ta fad'a wa mami yanda sukayi.
“Mami wai ranar lahadi In Shaa Allah.”
“Nan da kwana uku kenan, zan sanar da Abbanku anjima idan ta dawo.”
Ranar Lahadi da misalin k'arfe tara na safe kawu Shehu ya ga Abban RAYHAN da Mall. Lamiru k'anin mahaifinsa sai Zubair wanda shine ya masu jagora zuwa gidan su RAYHANA. A falon bak'i aka sauke su sannan aka gabatar masu da cinma na musamman, bayan sun gama. Mall. Shehu ya koro bayanin abinda ke tafe dasu ya had'a da fad'in zamu yi farinciki in ka duba buk'atar mu ka baiwa d'anmu 'yar ka.
Murmushi Abban RAYHANA yayi sannan yace “ da fatan a shirye kuke kuma kun tabbatar da d'an ku yana sonta?”
Mall. Lamiru yace “ eh alh. ”
Abba yace “ mai xai hana a d'aura auren a yanxu tunda ga waliyansa, ni zan yiwa d'iyata waliyi.”
Mall. Shehu yace “ alh. don Allah idan bbu damuwa muna son kama alfarma a bari nan da wata biyu, zuwa lkcn mun gama shirye komai ko In Shaa Allah.”
Abba yace “ ba damuwa Allah yasa muna cikin masu rai”
Had'a baki suka yi suka ce “ameen.” Hira suka d'an tab'a daga bisani suka tafi.
Bayan tafiyan nasu Abba ya kira Mamu ya fad'a mata yanda sukayi sannan yasa Mami ta kira masa RAYHANA tana zuwa ta risina ta gaidashi. Amsa mata yayi sannan yace “ nasa mahaifiyarki ta kira ki ne sbd anzo niman aurenki kuma na amince kuma har ansa rana nan da wata biyu.”
Abban na fara mgn ta d'ago kai da sauri had'i da zaro ido a zuciyarta kuma fad'i take “ aure kuma? ” bata sani ashe a fili take maganar ba, ba a zuci ba.
Abba yace “ kwarai kuwa sbd banga anfanin ajiye buduwar kamarki a gida har ynx ba, tashi ki bani guri.”
Mik'ewa tayi ido cike da kwalla tana tunani ko da wa Abban ke son had'ata , kan gado ta kwanta ra fashe da kuka tana mai rokon Allah yasa hakan ne mafi alkhairi gareta.
YOU ARE READING
*NA TSANI MAZA*
AcakLabari ne akan wata budurwa da ke ikiranin ta tsani maza, wannan dalilin ne yasa bata kula ko wani saurayin. Ko meye dalilinta na tsanar maza?. Ku biyoni cikin wannan labarin don sanin wannan dalilin.