💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*NA TSANI MAZA*
💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*💫Na💫*
*💐Aysha Isa (Mummy's Friend)💐*
*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*
*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile's family.*
_*O Allah! Open Your various ways of blessings and favour for us as we set our feet this morning into an uncertain society. Protect us from all the evil tricks that emanate from shattan and his forces among men and jinn. Overlook our shortcomings and forgive our sins, both apparent and hidden; major and minor. For You are the Most-Forgiving, the Most-Merciful. Ameen. Jumma'at Mubarak!*_
_*Nagode da addu'arku gareni, Alhamdulillah jikin nawa da sauki sosai*_
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
5⃣6⃣➡6⃣0⃣
Murmushi *RAYHAN* yayi sannan yace “ da Allah na dogara, kuma zai taimakeni mutukan ita alkhairi ce gareni.”
“ Allah ya taimaka ” inji Zubair, sannan ya cigaba da hira da abar kaunarshi. Daidai kofar gidansu Hameeda yayi parking, ya dan tsaya for some seconds amma basu sani ba saboda sunyi nisa a duniyar love, tsaki *RAYHAN* yaja yace “ toh lover boy sai kabari ta tafi ko .”
Zubair yace “Subhanallah har mukai ko?”
"Mtsw " ya zaka sani tunda kayi nisa, sai zuba zance kake, pls kabar yarinya taje gida ta hutu dix past 10 already, kuma kasan gobe ma da wuri zata tafi can .‘’
Dariya Zubair ya fashe dashi yace "na gane logonka kace dai kana son aje gun buduwarka da wuri, to ba inda zata gobe sai jibi ehee."
Murmushi Hameeda tayi sannan ta bud'e kofa zata fita kenan, *RAYHAN* yace “ Matar aboki please a taimakamin da numbar sahibata.”
“La ba damuwa ai ba sai ka rok'eni ba amma please kar kace ni na baka” kira masa numbar ta tayi bata jira amsa ba tafi.
Daga murya yayi ta yarda zata jishi yace “In Shaa Allah baxan fada mata ba kuma please gobe idan zaki tafi a taimaka koda flashing ayi min inzo na kaiki. ”
Fita Zubair shima yayi domin ya taka mata had'i da fad'in "Ai baka isa ba, babu inda matata zata tafi kuma gwamnati ai ta hana aikin banza,in kana son aiki ka biya kawai.”
“Ba damuwa zan iya biyan ko nawa ne in har zan samu soyayyar *RAYHANA*”
Hameeda tace “don't worry ai yiwa kaine nima ina sonku tare , sai kazo din gobe.”
Juyowa tayi ta fuskanci Zubair tace “Dear wallahi barci nake ji, yau duk a gajiye nake tun safe muke asibiti.”
Zubair yace “eh sorry gashi baki zama tawa ko ba da na maki tausa, wai me aka ce yana damunta ne?.”
Zub'uro baki tayi sannan tace “oho! amma dai ance in tayi aure ciwon zai daina saboda kowani wata hakan yake mata.”
“Oh kice min bakon ku ne na wata shine wai ke kunyar, amma da fatan ke baya maki haka dai ko?”
Rufe fuska tayi da tafin hannunta alamun kunya.
Murmushi yayi sannan yace “ wallahi dadi dake kenan magana daya biyu kice kunya amma kwana nawa ya rage , na kusa cire wannan kunyar…………” bai idda magana *RAYHAN* ya danna masa horn, da sauri ya tashi yace “sai na kira in mun isa.”
Waving nasa tayi tai masa Allah ya kiyaye sannan ta shige gida.
💐💫💐💫💐💫
YOU ARE READING
*NA TSANI MAZA*
DiversosLabari ne akan wata budurwa da ke ikiranin ta tsani maza, wannan dalilin ne yasa bata kula ko wani saurayin. Ko meye dalilinta na tsanar maza?. Ku biyoni cikin wannan labarin don sanin wannan dalilin.