51-55

875 46 9
                                    

💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫

*NA TSANI MAZA*

💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫

        *💫Na💫*

*💐Aysha Isa (Mummy's Friend)💐*

*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile's family*

*💃🏼💃🏼💃🏼 Ranar farinciki yau gashi tazo,nima da tamburata gani nazo, farin ciki nake 🅱K taji sauki.*

*Alhamdulillah Allah mungode maka akan wannan ni'iman da Kai mana na azurta 'yar uwarta 🅱K da lafiya, Allah ya baiwa duk musulmai da suke gida ko asibiti kwance ba lafiya sauki (Ameen).*

_*I dedicate this to all readers of this novel*_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

5⃣1⃣➡5⃣5⃣

Had'a rai tayi ganin irin kallon da yake mata don in bata manta ba wannan guy d'in ne da suka had'uwa dashi kwanakin baya, sannan tace “Alhamdulillah jiki da sauki.”

“Allah ya kara sauki.”

“Ameen” tace sannan ta koma zuwa ga kwanciyanta.

Tashi Hameeda tayi ta koma kusa da ita sannan ta rad'a mata mgn a kunni tace “kin ganeshi kuwa?”

Halin ko in kuluwa ta nuna tace “in na gane shi sai mai kuma, in fara tsalle ko rawa?”

“Allah ya huci zuciyar ki.”

“Ameen”.

Shi dai *RAYHAN* hankalinsa na kan *RAYHANA* domin tunda yake a rayuwarsa bai taba samun d'iya macen ta tafi da imaninsa ba irin *RAYHANA* komai nata burgeshi yake, ya nisa cikin tunani Zubair yayi taping nasa ya rage murya ta yanda bbu wanda zai ji maganar tasu yace “ man lfy kuwa,wannan kallo haka ai sai kasa wacce akayi mawa tsarguwa.”

Ajiyar zuciyar yayi yace ”kai dai bari kawai wlh bayin kaina bane."

“Kodai kana ciki ne?”

“Eh don Allah a tayani da addu'a da gani ba karamar wahala zata bani ba.”

Murmushi Zubair yayi sbd yasan kadan ne daga aikin *RAYHANA* sbd da ma xata iya yin fiye da haka, yace “Hameeda in kin shirya tafiya bismillah, mu zamu tafi. *RAYHANA* sai mun dawo gobe In Shaa Allahu, Allah ya k'ara sauki.”

“Ameen nagode”

Hannu *RAYHAN* yasaka cikin aljihu ya zaro kudi ya baiwa Hameeda yace “ ga wannan a siya lemu, Allah baki lfy yasa zakkan jikine.”

Shiru *RAYHANA* tayi kamar bata jishi ba.Hameeda ce ta amsa masa da ameen tare da godiya.
Ajiye mata kudin tayi a gefen ta sannan ta rage murya tace “ai in bazaki amsa addu'ar da aka maki ba ai sai ki godiya ko!”

“Mtsw! Idan an k'i fa?"

Hameeda tace “wannan kuma ya rage gareki, ni kinga tafiyata, gwara dai a bada kai bori ya hau ko za'a samu sauki wannan ciwon.”

Bata tsaya taji amsarta tayi ficewarta.

Tsaki *RAYHANA* tayi tace “ ina ruwanki da ni, ina ce jiki na ne bana wani ba.”

Sai a sannan Mami tayi magana don bayan su gama gaisawa ta tada sallah, tace “ana fad'a maki gsky shine kike wannan maganar ko, wai nufin ki ke bazaki yi aure bane ko me, haba mana *RAYHANA* ai ya kamata ki tausayawa kanki ko sbd wannan wahalar da kike sha, ko baki min zance ba nagan alamun sonki tattare da yaron da yazo da Zubair, meye aibunsa nasa, ina laifin mai sonka.”

Zub'uro baki tayi tace “toh ni *NA TSANI M……*”

Bata idda zancen ba Mami ta buge mata baki tace “akul dinki, karda in kara jin wannan zancen daga bakin ki, in ba sbd wannan laluran taki ba ai kamata yayi ina gida ynx ina hutawa, this will the last time da zan zaune dake asibiti kan wannan lalurar, in kin ga dama kiyi auren, in kuma baki ga dama karda kiyi, shashasha kawai kullum  sai ai ta magana d'aya dake sbd kingan ina lallashin ki.”

Jikin *RAYHANA* ya mugun sanyi sbd ta manta rabon da Mami tayi mata fad'a haka, hak'uri taba wa Mami akan hakan bazata sake kasancewa. A zuciyar ta kuwa wani irin tsanar *RAYHAN* taji ya dasu a zuciyar ta domin sbd dashi Mami ke mata fad'a, K'wafa tayi a cikin ranta “wlh sai na baka mamaki, sai kace ana so dole.”

💐💫💐💫💐💫

Tafe suke a mota *RAYHAN* na tuki, Zubair na gefen sa Hameeda kuma na zaune a baya duk sunyi shiru kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa.

*RAYHAN* ne ya katse shirun yace"Dazu nayi tunanin na san ki amma ina ce ko kamace ashe ke d'in ce."

Murmushi Hameeda tayi tace “ni kuma ina ganinka na gane ka.”

Zubair yace “toh ke a ina kika san shi?”

Labari ta bashi inda suka had'u.

Murmushi yayi “ina ruwa *RAYHAN* sarki zumud'i. Meyasa kuma kukayi tafiyar ku daga yace yana sonta, ni a ganina ai baiyi laifi ba.”

*RAYHAN* yace “nima dai haka nagani amma dukkansu ba wacce ta tsaya ta saurari ni ballanta a fad'in ko sunanta ne.”

Zubair yace ‘’gsky basu kyauta maka ba kam, amma ynx tunda ga Hameeda In Shaa Allahu komai zai zo da sauki.‘’

Hameeda tace “Nidai ban maku alkawari ba sbd kaima ka san halin *RAYHANA* idan har ba tada niyyar yin abu bbu wanda ya isa yasa ta dole, hasalima ban taba ganin ta kula kowani d'a namiji ba.”

*RAYHAN* yace “Alhamdulillah haka nake son matata ta kasance, amma don Allah ko zan iya sanin dalilin da yasa bata sauraron su?”

Ajiyar zuciya Hameeda tayi sannan tace “dalilinta shine wai ta *TSANI MAZA*.”

Zare ido *RAYHAN* da Zubair sukeyi suka fad'a a tare “ ta *TSANI MAZA*!”

“Kwarai kuwa.”

*RAYHAN* yace “pls ko zamu iya jin dalilinta na *TSANAR MAXA*?”

Hameeda tace “nima abinda har yau ban sani ba kenan, ranar da sauran frnds d'inmu suka sata gaba kuka ta fashe masu dashi tace is her little secret don haka baxata iya fad'a mana ba, nasan dalilin nata will be something terrible.”

Zubair yace “babban magana, wlh *RAYHAN* kana da babban aiki nidai fatana Allah ya daidaita tsakanin ku don kun dace da juna and a part from that *RAYHANA* is a very nice person jst as you……”



Pls manage this, wlh jikin ne har yanxu, nagode da soyayyarku.

*Taku ce*

_*💐Mummy's Friend💐*_

*NA TSANI MAZA*Where stories live. Discover now