36-40

669 36 0
                                    

💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫

*NA TSANI MAZA*

💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫

        *💫Na💫*

*💐Aysha Isa (Mummy's Friend)💐*

*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
_(Home of peace, honour and super writer's)_

_*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile & Exclusive Writer's Forum*_

*Godiya gareku masoyana, masu kirana da masu biyoni ta private chart don jin lafiyata ina matukar godiya, Allah barmu tare. Mummy's friend na yinku sosai da sosai, thanks for the love dearies😍😍😍*

*I dedicate this page to you my masoyas*

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

3⃣6⃣➡4⃣0⃣

*ASALIN MAMI*

Asalin sunanta Laurat Ibrahim dan yabo, mahaifinta a wancen lokacin yana d'aya daga cikin iyaye wainda suka tsani  'ya'yansu da ilimi bako domin shi a ganinsa ilimi bako bashi da wani fa'ida ga d'a namiji bare macen da duk karantun ta a karshin wani zata k'are, shi dai nashi a nima kud'i. A haka Mami da mahaifiyarta suke sanar amma yawanci kud'in akan lalurar makaranta suke k'arewa. Da kyar da sud'in goshi Mami ta gama secendary school. Bayan ta kammala makarantan ne mahaifinta yace ta fidda mijin aure, hak'uri ta bashi akan don Allah yabari ta cigaba da makaranta tunda bata da wani tsayayye a wannan lokacin, k'in yarda yayi da farko amma daya ganin ta dage akan haka yace ya barta ta cigaba amma ba da kud'inshi ba kuma da sharad'in in ta fara dole ta fidda mijin aure ko kuma ya aurata ga duk wanda yaga dama. Mami ta samu gurbin karatu a ABU inda zata karanta Home management, a gurin ne ta hadu Abban *RAYHANA* inda ya nace mata amma tak'i sauraronshi sbd da lalata yaso ta da farko, da yagan dai ba yarda zatayi ba shine ya biyo ta sigar aure, koda haka m all Mami k'in yarda tayi.Gidan su Mami ya tafi ba tare da saninta ba yaje yayiwa Abba ruwan kud'i sannan ya fad'a masa buk'atansa na son auren Mami nan take mahaifinta ya amince ba tare da dogon tunani ko niman shawara ba.

Kwatsam wani hutu taje gida Ummata ke tace mata ‘’ watoh Laurat kin iya turo da saurayi gida ba tare da kin nima shawarata ba ko, ke kina ganin kin ma kanki adalci kenan?‘’

Gabanta yayi mugun fad'i cike da mamaki  Mami tace " anya ba lamunde ko Hafsat aka ce ba?, don ni wlh bbu wanda na aiko."

‘’Hmmm kyaji dashi domin an ma sa rana ko nan da sati biyu sbd shi wanda kika aiko yace yana son ayi da wuri, kuma ba sai baban naku yamaki komai ba shi ya d'auki nauyin haka.‘’

‘’Innalillahi wa ina ilahi rajiun yanxu Umma sbd yanada arziki shine ba za'a yi bincike kanshi ba, Umma gaggawa fa a lamarin aure bashi da kyau, baku sanya halayensa suke ba umma amma sbd burinku na aurar dani ya cika shiyasa za'a aura mashi ni, nidai gsky…‘’

Dakatar da ita Umma tayi tace ‘’ sbda nice baki tsoro shiyasa kike fad'in haka,ai da sai ki sami baban naku ki mashi bayani, ni dallah tashi ki bani wuri.‘’

Kuka Mami ta fashe dashi kanta hada da guiwa. Nan take jikin Ummata yayi sanyi amma bbu abinda zata iya kai, illa hak'uri  da lalashin da tayi mata.

A haka akayi aure batare da tana so ba, a gidan nasa ta k'arasa karatunta. A halin yanxu tana aikine ministry of education.

Nisawa tayi bayan wannan dogon tunanin tace ‘’ kwadayi da rashi bincike ya jazamin auren mashayi, mazinaci ba don haka ba 'yar ta baxata tsinci kanta a wannan kazantaccen rayuwa ba.

*Annabi S.A.W yayi gaskiya yace ku zab'anma 'ya'yanku uba nagari da uwa tagari.‘’*

_*Iyaye kuji tsoron Allah kusani gaggawa aiki shaidan ne kuma ba mai wuce lokacin auransa, bincike a lamarin aure abu ne kyau karku bari kud'i ko wani abun duniya  ya rud'a ku,  ku kiyin bincike domin kuwa watarana zaku kuyi da na sani.*_

*NA TSANI MAZA*Where stories live. Discover now