💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*NA TSANI MAZA*
💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*💫Na💫**💐Aysha Isa (Mummy's friend)💐*
_*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile's family*_
_*بِسْــــــــــــــــمِ اللَّهِ الرَّحْمَ الرَّحِيْم.......*_
1⃣0⃣1⃣
D'aukar wayar yayi ya kara a kunni. Suka gaisa daga nan sai kuma suka ji yace “ gani nan zuwa ynx In Shaa Allah.”
“ Yaya ina zaka?, baka ko karya ba fa” cewan Intee.
Yana sauri yace “ Yanxu zan dawo intee ba dad'ewa zanyi ba.”
“ Sai ka dawo yaya pls kar ka dade.”
Tuni * RAYHANA* ta shiga falo har ta zauna ko, lumshe ido tayi wani irin mugun kewar Mami taji yana ratsata nan take hawaye ya fara zuba daga idanuwanta. Tab'ata Inteesar tayi tace “ anti lfy kike kuka, ko jikin ne har ynx?.”
Girgiza mata kai *RAYHANA* tayi tace “ bakomai inajin kamar wani abu ya shigar min ido ne” k'arya tayi mata donmin idan ba haka ta fad'a wa Inteesar inba haka ba zata bar tambayarta ba, tashi tayi tace ntee bari naje nayi wanka kafin yayan naku ya dawo, “ok ” intee ta fada a takaice.Wanka tayi ta saka riga da skirt na atamfa yayi mugun karb'enta bata yi kwalliya ba tana gamawa ta d'auki wayarta ta kira Mami, cikin sanyi jiki ta gaida Mami suna idda gaisuwan, Mami tace “ lfy naji ki haka kamar wacce bata da lfy?”, kamar wacce zatayi kuka tace “ banida lfy, baima dad'e da aka sallamo ni daga asibiti ba.”
“ Subhanallah daga zuwa sai kwanciyar asibiti, meke damunki?.”
"Marana ne ke ciwo."
“ Allah ya k'ara sauki, In Shaa Allah ciwon naki ya kusan zuwa k'arshe tunda kinyi aure, karda ki sa damuwa a zuciyarki kinji ko?”.
Gyada kai tayi tace “ eh, Mami yaushe zaki zo?”
" Mai zan zo na maki?, Ai rashin lfy taki ba sabon abu bane guna, ftna dai Allah ya baki lfy, kuma don Allah kiwa mijinki biyayya" nasiha Mami tayi mata wanda yasa jikin ta k'ara sanyi.
Hannun tasa ta goge hawayen da ke kan fuska ta tace a sanyaye “ nagode Mami ki gaida Abba” sannan sukayi sallama. Kwanciya tayi tana tunani yadda zaman nasu zai kasance da *RAYHAN*.“ Gashi tun ba'ayi nisa ba wani abu yafara bijiro mata wai shi sha'awa.
*RAYHAN* na barin gida police station ya nufa kai tsaye, yana isa suka gaisa da officers d'in da suke gun zauna sannan ya masu bayanin abinda ya kawo shi. Tashi d'aya daga cikinsu yayi wanda shine yayi kiran *RAYHAN* dazu ya nufa cell d'in ya fito da TJ.
TJ sai murna yake yana zaton bailing d'insu aka zo yi,murna sa ya makoma ciki sakamokon arba da idanuwansa suka yi da *RAYHAN* yace “ yauwa officer ka gan mutumin da yarinyar tayiwa rashin mutunci nan amma wlh nidai bbu abinda nayi mata ku yarda dani don Allah.”
Kallonsa RAYHAN keyi cike da mamaki sbd shi a iya tsawon rayuwarsa bai taba ganin TJ ba. RAYHAN yace “ mall. ni bangane mai kake nufi ba don asali ma ba sanika nayi ba. ”
Labarin abinda ya faru TJ ya bayar har ya kaiga zuwan su cell. Salati RAYHAN yayi sannan yace “ gsky abinda kukayi baku kyauta ba domin ni ban d'au abin da zafi har haka ba , yanxu haka yarinyar da kuka yiwa haka tana matsayin matane a guna.”
“ Don Allah Alh. kasa su sake mu wlh nidai bbu abinda nayi mata” Inji TJ.
Haka aka fito dasu dayan bayan dayan amma duk magana d'aya suke fad'i watau basu yimata fyade ba. Tagumi RAYHAN yayi yamasa rasa abin fad'i.
YOU ARE READING
*NA TSANI MAZA*
DiversosLabari ne akan wata budurwa da ke ikiranin ta tsani maza, wannan dalilin ne yasa bata kula ko wani saurayin. Ko meye dalilinta na tsanar maza?. Ku biyoni cikin wannan labarin don sanin wannan dalilin.