💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*NA TSANI MAZA*
💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
_*💫Na💫*_
_*💐Aysha Isa ( Mummy's friend)💐*_
_*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile's famil y*_
_*Ina mika ta'axiyata ga mummyna Hauwa Smasher,Allah ya jikan baba yasa mutuwa ta zama masa hutu, Allah yasa aljanna makoma.*_
_*My mentor 🅱K thanks for the love, Alhamdulillah naji sauki ko,you are really a sis from another mother. Thanks for the love dear💋💋💋.*_
_*Dedicate this page to my mummy real smasher*_
*BISMILLAHIR-RAHIR-RAHIM*
7⃣6⃣➡8⃣0⃣
Wani gidan abokinsu suka tafi da ita.
Misalin k'arfe 6 na yamma TJ sukayi parking gabar gidansu *RAYHANA*, su biyu suka fito da ita daga motar a galabaice duk rigar ya bace da jini, shi kuma TJ ya k'arasa gun gate d'in yayi knocking. Baba Iro ne ya lak'a had'i da tambayar ko waye.
TJ yace “mall. don Allah ka bud'e yarinyar gidan muka tsinta a hanyar wani hotel nan kusa da ku.”
Da sauri Baba iro ya bud'e gate d'in yana ganin *RAYHANA* yace “subhannallahi, bayin Allah na gode amma yana gani duk riganta ya b'ace da jini ne?”
AB yace “muma bamu sani amma kamar fyad'e aka mata.”
“Subhannallahi fyad'e kuma, don Allah ku jira ni na kira Hajiya” juyawa yayi da nufi kiranta Mami, Tboy yace “mall. don Allah dakata tafiya zamuyi.”
"Toh mun gode bayin Allah,Allah ya saka da alkhairi" rik'eta Baba Iro yayi sannan ya kwala Mami kira daga inda yake tsaye, ya kuwa yi sa'a Mami tana parlourn k'asa tana kallon, da sauri ts tashi ta lek'a window ta gan baba iro rik'e da *RAYHANA*, da gudu ta fito daga parlourn tun kan ta iso gunsu take tambayar baba iro ko meya sami *RAYHANA*.
Baba Iro yace “wlh hajiya wasu samari ne suka kawota wai sun tsince tane wai a hanyar wani hotel dake kusa damu.”
“Subhanallahi hotel kuma?,toh meya had'a *RAYHANA* da hotel kuma ita da tace min zata makaranta. Baba Iro don Allah taimakamun na shiga da ita ciki. ”
D'aukarta sukayi zuwa d'akin Mami, baba iro ya nufa hanyar fita har yakai bakin kofar kenan yace “yauwa hjy samarin sunce wai suna ganin kamar an mata fyad'e ne , don Allah a duba ta da kyau.”
“Innalillahi wa ina ilaihi raji'un fyad'e, wai meya kai *RAYHANA* hotel ne?. ”
Baba Iro yace “Hjy hak'uri zakiyi d'a ne ynx ka haifeshi amma baka haifa halinsa ba, amma hjy nasan d'iya ta bazata yi abin kike tunani ba, don Allah hjy kibi ta a hankali nasan da yarda Allah gskya zatayi halinta.”
“Toh baba In Shaa Allah zan bita a hankali, nagode.”
Sai da misalin k'arfe bakwai da rabi *RAYHANA* ta farka daga barci mik'a tayi had'i da hamma sannan ta juya gefen ta Mami zaune tayi tagumi, mik'ewa tayi da sauri ta koma a kwanciya sakamakon wani zafin da taji a kasanta “Innalillahi wa ina ilaihi raji'un,mami pls help me.……‘’
Manage this pls🙏🏼
YOU ARE READING
*NA TSANI MAZA*
RandomLabari ne akan wata budurwa da ke ikiranin ta tsani maza, wannan dalilin ne yasa bata kula ko wani saurayin. Ko meye dalilinta na tsanar maza?. Ku biyoni cikin wannan labarin don sanin wannan dalilin.