💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*NA TSANI MAZA*
💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*💫Na💫*
*💐Aysha Isa (Mummy's friend)💐*
*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile's*
_*Gσ∂ιуα тα мυѕαммα gα єχ¢ℓυѕινє ωяιтєяѕ ƒσяυм ιηα уιηкι ιяιη ѕσѕαι, Aℓℓαн уαѕα нυкυη¢ιη ∂α кυкα ∂αυкα уαzαмα αℓкнαιяι, Aℓℓαн кυмα уα ∂αтαя ∂αмυ нαηуαя кωαяαι.*_
_*NA TSANI MAZA GROUP FANS wallah ina yinku irin totally, you guys are killing me with ur words, karda ku damu RAYHANA bazata mutu yanxu ba 😜*_
_*Ban mantaki ba bestyna nagode da kaunar ki gareni, Halissa I love yhu wujiga-wujiga❤❤❤❤*_
_*I dedicate this page to you only Halissa my besty like no other*_
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_
4⃣6⃣➡5⃣0⃣
Hameeda tace "ok anti."
D'aukar ta sukayi suka sanya ta cikin motar Anti Hanan ta jasu zuwa asibitin da suke ganin likita,suna isa anty Hanan ta fita da sauri ta kira masu d'aukar emergency, jim kadan sai gasu da keken tuka marasa lafiya suka cicib'eta suka aza kan keken, tuka ta sukayi straight zuwa emergency sbd har ynx idonunta a rufe suke. Luckily for them bbu layi nan take Dr. din ya fara duba ta yayi mata su allurai, ya danyi rubuce-rubucen sannan ya fito yace "ina 'yan uwan patient dinnan?"
Da sauri Anti Hanan tashi sbd a lokacin Hameeda taje kiran Mami ta sanar da ita abinda ke faruwa tace “gani ni.”
Dr. yace "ya sunan mara lafiyan?"
“RAYHANA Saleh Maikudi.”
Dan rubuce-rubuce yayi sannan ya mik'a mata wasu paper yace “wa'inan papers zaki je dasu lab. sai kice d'aya daga cikin staffs din su biyoki d'iban jini domin yiwa mara lafiyan tests d'in nan.”
“Nagode sir amma don Allah wani irin test zance masu?”
Dr. yace “jeki kawai in kin basu papers suma zasu duba su gani ko wacce iri ce.”
Godiya tayi masa sannan ta nufi hanyar lab. din da sauri, tana isa taba d'aya daga staff din wurin takardar da doc. yabata, karantawa tayi sannan ta mik'e ta d'auki kayan aiki suka koma inda aka kwantar da *RAHYANA*.
Sallama sukayi a emergency room amma ba amsa masu ba bbu kowa a daki kuma har yanxu *RAYHANA* bata farka ba. K'arasowa matar tayi taja jini cikin allura ta tafi dashi don aiwatar da aikinta.
Mami ce ta k'araso wurin tare da Hameeda hankalin ta a tashe tace “sanda nace kar ta fita sbd yanayin ta ya nuna bata da lfy amma tace min zata iya, ynx ba ga irin taba.”
Anti hanan tace “Maman *RAYHANA* pls kiyi hak'uri itama ai bata tsammanin haka zai kasance ba , In Shaa Allahu komai zai zo da sauki.”
Mami tace “yanxu mai aka ce yana damun ta?”
"Wlh basu ce komai ko ba, Dr. ya bada tests din za ayi mata har ma an d'auki sample ko, result muke jira ynx.”
Mami tace “Allah yasa muji alkhairi, amma wani test yace ai mata?”
Anti Hanan tace “wlh baimun bayani ba amma nagan PT test a d'aya daga cikin test d'in.”
Mami da Hameeda suka kwalo ido 😳 cike da mamaki bbu ma kamar Mami sannan suka fad'i a tare “Pt test kuma mai ya had'a *RAYHANA* da test d'in masu ciki ita ba matar aureba?.”
YOU ARE READING
*NA TSANI MAZA*
SonstigesLabari ne akan wata budurwa da ke ikiranin ta tsani maza, wannan dalilin ne yasa bata kula ko wani saurayin. Ko meye dalilinta na tsanar maza?. Ku biyoni cikin wannan labarin don sanin wannan dalilin.