💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*NA TSANI MAZA*
💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*💫Na💫**💐Aysha Isa (Mummy's friend)💐*
*♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM*
_(Home of peace,honour & super writers)__*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile's family*_
_*Haba mutane muji tsoron Allah mana mutuwa yanxu ya zame abun wasa abinda ya kamata yazama darasi da aya ga masu tsoron Allah, kusani duk mai rai manacine meye na gaggawan kashe mutum alhalin da ransa?. Allah ya datar damu a hanyar kwarai yasa mu cika da imani.*_
_*بِسْــــــــــــــــمِ اللَّهِ الرَّحْمَ الرَّحِيْم.......*_
1⃣0⃣3⃣
Da misalin k'arfe biyar na asuba RAYHAN ya tashi zama yayi ya k'urawa RAYHANA ido wacce take take barci amma dagani barcin wahala take don sai ajiyar zuciya take sauka alamun ta sha kuka, gefen fuskarta ya shafa had'a da fad'in “ tawan kin faranta min rai, ubangiji ne kawai zai saka maki da mafificin alkhairin” hannuwansa ya daga sama “ Allah nagode maka da karemin mutuncin matata, baka bawa wa'inan azzalumai bayin samun nasarar keta mata hadi ba, Allah ka dad'e karemin ita da dukkan musulmai baki daya” peck ya mata a goshi sannan fad'a toilet ya tsarkake jikinsa. D'auro towel yayi ya fito wani kuma akan kafad'arsa yana tsane jiki dashi. Kura masa ido tayi tana kallonsa don tunda yayi mata peck a goshi ta farka. Jallabiya ya zura sannan yamatso kusa da ita, runtse ido tayi kamar mai barci kafin ya iso gun, sha gefen fuskanta yati cike da wani salo had'i da hura mata iska a kunnenta. Bud'e idanuwar tayi ta zuba wa kyakyawan fuskar sa yace “ afuwan tawan na katse maki jindadi ko?, sallah nake son ki tashi kiyi koda a zaune pls tawan, ni na tafi masallaci”, bai jira cewanta ba yayi tafiyarsa domin wasu masallacin har sun tada sallan ko. A daddafe ta tashi ta fad'a bayi kasa kanta ta fara yi, tayani tana zubda hawayen da ke dauke da abubuwa masu tarin yawa, tana gamawa ta tsarkake jikinta had'i da d'auro allola sannan ta fito gabatar da sallan bata tashi ba har RAYHAN ya dawo daga masallaci tana addu'a tare da mik'a godiyarta ga ubangijinta wanda yasa hasashenta ya zama sab'anin abinda take tunani, zama yayi kusa da ita yna jiranta ta iddar. Tana iddarwa ta gaidashi cikin sanyi murya bata jira amsarsa ba tace “ pls kasa a sake wa'inan mutanen da aka kama.” “ Why?”
“ Bcos I wasn't raped” ta bashi amma a takaice.“ Toh ai niban tabbatar” , dago kai tayi da sauri ta k'urawa bedsheet nasu ido, juyowa yayi don ganin abinda take kallon, murmushi yayi ganin wurin da yayi stain take kallo sannan ya juyo ya sake fuskantan ta yace “ kodai zamu na.........” ya k'arasa xancen had'i da kashe mata ido, sukunyar da kai tayi cike da takaici da kunya ace ynx duk wahalar da tasha jiya bai isa ya tabbatar masa da cewan ita budurwa bace, kuka ta fashe dashi sannan ta juya ta niyyar tashi wani irin zafi taji a kasanta dukawa tayi tana zance zuci " amma a gsky bayi wauta da nace Abba ya min fyad'e tunda dai a lkcn banji irin wannan rad'ad'in ba, da wani irin ido zan kalli abbana, ashe Mami tayi gsky dace abbana bai min fyad'e amma na da'uki karan tsana na d'aurawa maza wanda inda ba Allah daya kareni ba da hakan ta faru dani a zahiri, kaicona kuka ta k'ara fashewa dashi tare da fad'in " innalillahi wa ina ilaihi raji'u" ganin haka RAYHAN ya zaunar da ita sannan ya rungumeta yana rarrashi “ am sorry honey wlh nafi kowa sanin ke buduwar ce, I was jst kiding amma maganar sakesu gsky bai taso da dukkan alamu sun saba suna yin haka.” Ajiyar zuciya tayi tace “ don Allah idan har sbd ni suke ajiye pls a sake su na yafe.”
Sassauta rungumar yayi mata yayi “ ni kam ban yarda sai sun biyani hakkin kallan min jikinki da sukayi, amma in kin dage sai dai idan zan sake irin ta jiya.” “ Na yarda ” ta fada kai tsaye,“ sure?” ya tambayeta. Rufe idanuwarta tayi da tafin hannun sannan ta gyada masa. Cakulkuli ya mata da sauri ta cire hannuta daga fuska sai dariya take har ta kai ga kwanciya ganin yanason wuce gona da iri ta rik'e hannunsa tayi narai-narai da ido tace “ pls ka bari bana so.” Dariya ya bushe dashi yace "amma ynx kika gama fad'in kin amince", turo baki tayi tace “ ai ba ynx nake nufi ba.” Murmushi yayi yaje hancinta yace daman bbu abinda zan maki my hrt."
Daga wannan ranar haka RAYHANA da RAYHAN suka ci gaba da zamansu cike da nishadi tare nunawa juna tsantsar so. RAYHANA ta tsoke wannan akidar tata *NA TSANAR MAZA* bazaka taba sanin ba auran syy sykayi da RAYHAN ba.
*BAYAN WATA DAYA*
RAYHANA ce kwance akan three seater rik'e da handout tana karantun last papern da zasu rubuta jibi Monday. RAYHAN yace “ tawan pls kibar wannan karatun haka kixo ki ci abin mana”.
“ Na koshi bai dad'e da na gama shan shayi ba.” Daga haka bai k'ara ce mata komai ba har ya gama cin abincinsa, tashi yayi ya zo falo ya fisge handout d'in hannunta, da sauri itama ta mik'e, zagaye falon ya farayi tana biye dashi tana fad'in “ don Allah ka bani na kusan gamawa ” ganin baida niyyar ba ta tayi zamanta, kusa da ita yazo ya zauna shima, sannan yace “ my dear wai meyasa kika fi bama karatu muhimmanci ne bisa ga lafiyarki, duba fa yanda kika rame sai haske kike k'arawa kamar wacce bata da jini a jiki duk sbd rashin kula da abinci saidai ki girka min ni inci.”
Turo baki tayi tace “ toh ni bana jin dad'in abinci ne shiyasa, don Allah ni ka bani littafin na na k'arasa karantawa.”
" Bbu abinda zaki karanta don ynx ma fita nake son muyi."
“ ni bbu inda zani” tace tana nai turo baki.
“ Dole kuwa tare zamu tafi, kije ki shirya ina jiranki a mota .”
Tashi tayi tana buga-buga kafafuwanta a k'asa had'i da turo baki harda 'yan guntun hawayenta taje ta shirya, a mota ta same shi ta bud'e gidan gaba ta zauna sai kunbure-kunbure take. Shima shareta yayi baice mata komai ba sai gintse dariyarsa yake. Hanyar anguwarsu tagan ya nufa a zuciyarta sai addu'a take Allah yasa nan zasu, tana gani yasha corner gidansu ta washe baki tace “ nagode honey kamar kuwa kasan nayi kewar Mami sosai.”
Murmushi yayi sannan yayi horn, mai gadi ya bud'e masu gate. Tsayawa yayi suka gaisa da baba Iro ta fita a guje ko parking motar bata bari yayi ba. Murmushi yayi tare da girgiza kai yace “mata komai girmansu akwai yarinta tattare dasu ”.
Tun daga waje fara kwalawa Mami kira har ta iso ciki direct d'akin m)Mami ta nufa amma bata ciki, part d'in abba ta nufa tare da sallama turus ta tsaya ganin Mami na daga abba daga kwance, da sauri ta k'araso ciki ko gaida Mami bata yiba ta k'arasa gun abbanta tace “ abbana mai ya sameka kuma hka? ” gun Mami ta juyo tace “ Mami ashe abbana baida lafiya har haka shine baki fad'a min ba kuma kusan kullum sai munyi waya dake, Mami wani irin laifi na maki da bakin son na gana da abbana?” kuka ta fashe dashi. RAYHAN da ke tsaye bakin k'ofa tun shigowar RAYHANA ya k'araso daga ciki “ toh yanxu ai kin ganshi sai kibar kuka ki masa addu'ar samu sauk'in ciwonsa.” Hannu tasa ta share hawayenta tace “ Mami tun yaushe Abba ke fama da wannan ciwon, kuma wani irin ciwo ne?”. Mami tayi shiru bata ce komai ba, sake maimata tambayar RAYHANA tayi a karo na biyu ,sai an sannan mami tace........
YOU ARE READING
*NA TSANI MAZA*
RandomLabari ne akan wata budurwa da ke ikiranin ta tsani maza, wannan dalilin ne yasa bata kula ko wani saurayin. Ko meye dalilinta na tsanar maza?. Ku biyoni cikin wannan labarin don sanin wannan dalilin.