💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*NA TSANI MAZA*
💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*💫Na💫*
*💐Aysha Isa (Mummy's Friend)💐*
*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile's family.*
_*UDKHULUL JANNAT BISSALAM Enter PARADISE in peace... I pray for u and your family to be among those who will be told this statement yaumul qiyama. Jummat mubarak.❤_
_*Ina mika gaisuwata ga mummy na real smasher, ina kuma tayaki murnar farawan sabon littafinki,kamar inda kika fara lafiya Allah yasa ki gama lafiya.*_
_*💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 Ranar farinciki yau gashi ta zo, nima da tamburan na gani nazo, murna nake my sis ta haifi baby……, Allah yara kan sunnah, godiya ga Allah ubangijin mu mabuwayi. Masha Allah, wat a unique birth Aunti Fatima, born in March, Married in March and Masha Allah bless with bouncing baby girl still in same month. Allah ya raya baby ya kuma kara karfin jiki ya sauka dukkanin musulmai masu ciki lafiya. Ameen.*_
_*I dedicate this page to Aunty Fatee*_
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM*
7⃣1⃣➡7⃣5⃣
“Ina ruwanki ki, ai bake zan jazawa hasaran ba.”
“Ok, naji pls ki bani wayata mana.”
“Wlh in kinga na baki wayar toh nasan dalilin lumshe ido da kikayi daxun saida na fisge waya kika farga.”
“Uhmm toh karanta ki bani wayata.”
Sakon Hameeda ta shiga ta karanta sannan ta jiyo da dubarta zuwa gareta tace “ *RAYHANA* you are in love ait?”
Murmushi tayi sannan ta sake lumshe ido had'i da gyad'a mata kai.
“Who is he?”
“Don't knw him yet amma muna dai exchanging words.
Murmushi Hameeda tayi sannan ta koma gun su Xee da sauri *RAYHANA* ta bita sbd bata son Hameeda ta fad'ama su Zee don kuwa zata sha tsokana. Da isar su gun, Hameeda tace “dudes albishirinku?”
“Goro”
Tace “Masha Allah daman kawarku ce ta………………”kafin ta idda magana *RAYHANA* ta rufe mata baki da tafin hannunta sannan ta rad'e mata magana a kunne.
Murmushi Hameeda sannan taja bakin tayi shiru , wayar *RAYHANA* da ke hannunta ne ya ruri alana wani msg ne ya shigo da sauri Hameeda ta bud'e ta karanta sannan ta dago ido ta kalli *RAYHANA* “have ur phn."
Amsar wayar tayi ta karanta sakon kamar haka:
_*Pls dear wai yaushe zamu hadune, wlh ina muradin ganinki matuka. Bana iya barci koda min 1 face sai nayi mafarki. Miss dear really want to see you.*_
_*From Tijjani mai kaunarki.*_
Dago da fuska tayi tana kallon Hameeda da alamun akwai maganar take son tayi.
“Maryam tashi mu tafi tunda yau ba'a son hiran damu amma dai ko menene in tayi tsami maji.”
Suna tafiya *RAYHANA* ta dawo kusa da Hameeda tace “bestyna meye shawaranki?”
Ajiyar zuciya Hameeda tayi “a gaskiya bazan boye maki nafi sonki da *RAYHAN* amma tunda wannan ya kwanta maki ynt invite him home?”
“Kai gsky bana jin zan iya cx Mami na ganin shi mgnr aure zata min.”
“Kuma ke baki shirya aure ko ba ko me kike nufi, da fatan dai ba akidarki ta da kike son dauwama a kai ba?”
“Hmmm a'a na sassauta ra'ayi amma jst don't want to invite him home for now.”
“Just be careful dear, mazan ynx sai a slow.”
“In Shaa Allahu dear I will, tnx alot bestyna, Allah ya sauke ki lfy kuma yabarki tare da Zubair.”
“Ameen Allah kema ya baki miji nagari.”
“Ameen nagode sai gobe idan mun had'u.”
💐💫💐💫💐💫
*BAYAN KWANA BIYU*
“Kai guyz mun kusan kwasan gara fa.”
“Kai TJ da gskyr kake, chick din ta yarda kenan?”
Tboy yace “AB sarkin zumud'i, kabari ya bamu details mana.”
Murmushi TJ yayi sannan yace “ta yarda, ynx zuwa karfe uku zamu had'u da ita a lace resturant, don haka kuyi making necessary arrangement kan nazo.”
AB yace “ok ba damuwa zanje ina da abokin gun wanda yake aiki as waiter a zanje a matsayinsa zan taya shi aiki ina so sai muyi duk abinda zamuyi ba tare dawani yasani ba.”
TJ yace:“Yauwa kagan kenan abin zai zo mana da sauki, ni na tafi samu gurin da zamu huta ba tare da wani ya dame muba.”
“Ok all the best sai munji ka kenan.”
A b'angaren *RAYHANA* kuwa yau a daddafe ta tashi sakamokon matsanacin ciwon marar data kwana dashi yau kimanin kwana 3 days kenan tana fama dashi shiyasa ma tasa a haduwar su da Tijjani a yau cx tana expecting yau ciwon zai mata sauki, amma sai lbr tasha banban sbd yau har fad'uwa gabata keyi, ga wani ciwon kai da ya adabe ta. Wanka ta shiga tana fitowa da ta goge jikinta da towel ta shafa mai, light makeup tayi sannan ta sa jallabiya baki,sannan ta yafa veil dinshi, bag dinta ta d'auka banda car keys cx bata buk'atan zuwa da mota kar ta tafi da ita wani yazo ya kawo wa Mami k'aren a gan motar wani gun daban ba skul ba. D'akin Mami ta shiga da sallama, ta risina ta gaida mami.
Amsa gaisuwa Mami tayi kannan tace “lfy naganki haka kamar wacce bata da lafiya?”
“Mami wlh mararta ke ciwo shine ya had'a min da ciwon kai amma da sauki ynx.”
“Tun yaushe kenan?”
“Yau kwana uku kenan.”
“Shine baki fad'a min ba sbd kar na maki fad'a ko?, toh wlh ko ynx ba fasawa zanyi ba inma zaki fidda miji kiyi aure da yafi maki in ba haka ba zakuwa kiyi ta fama dashi, kuma na baki nan zuwa ending of dix year in ba haka da Abbanki zan had'aki ya samu wani wanda ya dace ya had'aku kawai, shashasha dallah tashi kibani gu.”
Tashi tayi jikinta ya mugun sanyi kuma ta kudurci aniyar amincewa da Tijjani koda kuwa bata wani sonsa ko Mami zata koma sake mata fuska kamar da.
Da misalin k'arfe uku dadai TJ ya iso skul yazo ya d'auketa suka nufi Lace resturant murna kamar ta kashi, ita kuwa *RAYHANA* in banda fad'uwa babu abinda gabanta yake, da ganin shi kawai taji bai kwanta mata ba amma ta fison in sun iso gun suna fara cikin abinci ta fad'a masa don su rabu lfy ba tare da jin haushin juna ba.
Suna zama bada jimawa ba sai ga AB ya iso gun su as waiter yace “mai zamu kawo maku?”
TJ yace “gimbiya mai za'a kawo maki ne?”
Murmushi tayi sannan tace “any soft drink is ok by me amma wlh a koshe nake.”
Ido TJ ya kashe ma AB yace “ka kawo lacasera kawai nima bazan ci komai tunda gimbiyata ma bazata ci komai ba.”
Lashe leb'e AB yayi sannan yaje ya taho da gora biyu na lacasera had'e da stroll ya ajiye guda a gaban *RAYHANA* dayan kuma ya ajiye gaban TJ.
Bud'e mata goran TJ yayi sannan shima ya bud'e tasa yafara sha itama tafara sha, suna d'an taba hira daga k'arshe dai ta fad'a masa gskya bai mata ba. Bai nuna damuwarsa ba iyakacin cewa ma yayi ta tashi ya kaita gida ai ba damuwa, suna shiga motar ko mintin goma baiyi ba bacci ya d'auketa. Dariyar mugunta ya fashe dashi yace “ai in kin san wata baki san wata ba, mu za'a raina wa wayoh.” Wayarsa ya d'auka ya kira Tboy da AB, suna isowa yaja motar sai………………

YOU ARE READING
*NA TSANI MAZA*
RandomLabari ne akan wata budurwa da ke ikiranin ta tsani maza, wannan dalilin ne yasa bata kula ko wani saurayin. Ko meye dalilinta na tsanar maza?. Ku biyoni cikin wannan labarin don sanin wannan dalilin.