61-65

585 29 0
                                    

💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫

*NA TSANI MAZA*

💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫

        *💫Na💫*

*💐Aysha Isa (Mummy's Friend)💐*

*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

_*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile's family.*_

_*Ina mai baku hakuri akan jina da kukayi kwana biyu.*_

_*Time writers wallah nayi kewanku sosai,musamman chief editor na brilliant writers @ Meelat Musa a  gaskiya kina kokari, heart you dearie.*_

_*Ina mika ta'aziyata ga Aunty Faiza (marubuciyar DAN FASHI) Allah ya jikansa, yasa aljannace makimarsa.*_

_*Ban mantaku ba Aunty Samira Umar (SS),*_
_*Munary*_
_*Haleema*_
_*Ummu Humaira da duk members din group din NA TSANI MAZA , na nagode da soyayyarki, nima ina matukar sonku.*_

_*Eloquence Writer Association, a gaskiya kunada hadin kai da karamci, nagode da soyayyar ku, Allah yakara hada kawunan mu kuma ya barmu tare.*_

_*Muhievert 'yar india, wish happy birthday day in arriars,age with grace dearie.*_

_*Na sadaukar da wannan fejin ga duk masoyar wannan littafin.*_


_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM*_

6⃣1⃣➡6⃣5⃣

“Mtsw! nifa bana son shashanci, kin sani gaba sai kuka kike bbu gaira ba dalili, ko kanki aka fara auren ne?,wlh in baki yi maza kin shanye shi bq sai na sab'a maki kuma ki goge wannan hawayen munafuncin da kike, abinda wataran da kanki zaki bada kud'i a sai maki.”

Zunb'uro baki tayi ta share hawaye sannan ta kafa kofin baki a tana sha tana yatsina fuska har ta shanye.

“Yauwa ko kefa maza tashi kuje kuyi kunshin tun daxun take jiranki.”

Tashi tayi ta nufa d'akin nasu tana isa da tarda har suyi kunshi ko ita d'aya ta rage, zama tayi aka zana mata kunshi mai masifar kyau, wanda kana ganinta kasan amarya ce.

Zee tace “wow kin ga yanda kikayi kyau kuwa, anya Zubair zai ganeki kuwa?”

Murmushi Hameeda tayi tace “mai zai hana ai ko cikin niqab nake zai nageni balla fuskata a bude.”

Tab'a baki Rayhana tayi sannan tace “Allah ya kaimu ranar ayi aure nan kowa ya hutu wannan zumud'in haka!.”

Murmushi Maryam tayi tace a sigar zolaya “Haba Rayhana ai bata mayi zumud'i wlh dani ce ko barci bana iya wa.”

Rayhana tace ”Kwaji dashi yara sai shegen son maza.”

Murmushi sukayi, Zee tace “ai gwara mun so su domin zama haka ba miji wlh batayi, haka kawai mutum yace ya *TSANI MAZA*, ni kam wlh bana iyawa. ”

Murmushi Rayhana tayi don inda sabo ta saba da irin wannan maganar da Zee take yab'a mata.

Maryam tace “Zee zaki yafara ko?, pls let change topic. Yauwa Rayhana wai baki da lfy ne ko kina taya bestyn ki zullumin?. ”

“Haba wani zullumi kuma ba ita tace tana son sa ba, halan mai kika ganin ne kike tambaya?.”

Maryam tace “Gani nayi kin rame ne.”

Hameeda tace “Wlh mantawa nayi ban fad'a maku ba, bai fi sati  d'aya da aka sallameta daga asibiti ba ai.”

Atare Zee da Maryam suka ce “eyyah Allah yak'ara sauki, halan fever ne?”

*NA TSANI MAZA*Where stories live. Discover now