26-30

632 36 0
                                    


💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
     

*NA TSANI MAZA*

💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
     

         *💫Na💫*

*💐Aysha Isa (Mummy's Friend)💐*

*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
_(Home of peace, honour and super writer's)_

_*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile's family & Exclusive Writer's Forum*_

_*My mentor, 🅱K (autan exclusive)  Allah yabaki lafiya ya yaye maki dukkan lalurarki, yasa yazama kaffara. Zamuyi kewarki 😔. Ni har nafara missing dinki. GWS 🅱K*_

_*Masoyana nasan kuna hakuri amma don Allah dad'e yin hakuri abubuwa sun shamin kai banxan samu maku typing kullum kamar yarda kuke bukata ba pls a min afuwa🙏. Ina sonku domin  da bazarku nake taka rawa😘, ana tare irin totally dinnan*_

_*I dedicate dix page to 🅱K & to you my masoyas😘*_

_*BIMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

2⃣6⃣➡3⃣0⃣

Shirun da Ummi taji yayi ne yasa tace " *RAYHAN* kaifa nake sauraro in kuma baka shirya fad'amin ba inyi wuce wata ehee. Ai ba kai kadai na haifa ba ka maida ni kamar sa'arka ina magana sai wahalar da ni kake."

Tashi tayi ta nufi hanyar fita. Da sauri *RAYHAN* ya tashi ya sha gabanta sannan ya risina yana bata hak'uri, yace "Ummi don Allah kiyi hak"uri zan fad'a maki. "

"Toh fad'a ina sauraronka."

Zunb'uro baki yayi cike da shagwab'a  "toh Ummi ki shigo ciki ki zauna mana. "

Murmushi Ummi tayi sai ta k'araso daga ciki ta zauna edge d'in gadon tace " Shagwab'ab'e kawai ka girma amma sai abin yara kake."

*RAYHAN* yace "toh Ummi ai ni yaro har yanxu gun ki."

"Ni dai ka fad'a min abinda ka tsaida ni ma, bani da lokacin wannan shashacin naka."

"Ummi wata yarinya na gani ina so amma da gani na ta tashi ta bar gun.. " kwashe labarin yanda sukayi da kawayen *RAYHANA* yayi sannan ya k'ara da fad'in "Ummi tun daga ranar ban k'ara sakata a idanuwa na ba."

Tunda yafara magana Ummi ke kallonsa cike da mamaki tace " yanxu *RAYHAN* sabida mace ka canza haka?, yanxu duk yawan 'yan mata da suke sonka ba wacce ta maka daga cikinsu, anya ba gamo kayiba kuwa?."

" Ummu ina kyautata zaton mutun ce kamar ni, pls ummi ki tayani da addu'a ."

"Toh *RAYHAN* in itace mafi alkhairi gareka Allah ya tabbatar."

*RAYHAN* yace " Ameen my everlasting angel, nagode Ummi na ina sonki."

Murmushi tayi ta fice daga dakin.

💐💫💐💫💐💫

_*ASALINSU*_

         _*RAYHAN*_

*RAYHAN* d'a ne ga Alh. Shareef Aminu da Haj. Hauwa wacce suke kiravda Ummi, shine d'a na farko yana da kannai uku Kamal, Shuaib sannan auta Fatima wacce suke kira da Inteesar. *RAYHAN* sun tashi cikin maraici sakamakon rasuwar da mahaifinsa yayi a hatsarin mota a hanyar zuwar sa kaduna. Yanxu kimanin shekaru goma kenan domin a lokacin yana matakin k'arshe a makarantar secondary, ita kuma Inteesar sherakanta daya a lokacin.

   
     _*RAYHANA*_

Alh. Saleh Maikudi shine cikakken sunanar mahaifin *RAYHANA* shaharren d'an kasuwa ne, ya kasance mutun ne mai  yawan aure-aure domin ya cika burinsa na samun d'a namiji amma duk cikin matar sa babu wacce ta samu haihuwa sai mahaifiyar *RAYHANA* mai sunana laurat, itama daga *RAYHANA*  bata sake haihuwa ba . *RAYHANA* tashi cikin tsangwama da kiyayya iri-iri gun mahaifinta sbd kasancewar ta 'ya mace.  Sakamakon haka ta tashi da *TSANAR MAZA* tun tana k'arama.

    _*ZUBAIR*_

Alh. Sambo mai yadi  shine uba ga  Zubair yanada mata biyu Hafsat wacce suke kira da Anti yaranta biyu Zubair da Saudat sai uwar gida Hauwa wacce suke kira Mama ita kuma yaranta uku Haleema, Asiya sai d'an autan ta Nasir wanda yake sa'ar Zubair.

     _*HAMEEDA*_

Mall. Ahmad Bako da mal. Shafa'atu sune iyaye ga Hameeda. 'Ya'yan su hudu Hameeda, Bilkisu  (Billy), Jidda sai auta Ibrahim (khaleel). Mahaifinsu ma aikacin gwamnati ne.

wannan kenan.




💐💫💐💫💐💫

_*2 days later*_

"Hameeda,  Hameeda …" Umma ce ta kwalawa Hameeda kira.

Da gudu hameeda ta iso inda take ta risina tace " na'am Umma gani."

"Yaushe zaki gun anti ki ne? nagan lokaci sai gabatowa yake kuma kin k'i zuwa wurin nata."

Duk'ar da kai tayi cike da kunya saboda ta san me Umma ke nufi watau taje anti mata gyaran  amarya ita ba ta gyaran ke damuta ba, a'a wasu abubuwan da  anti ke bata ta sha ne bata so sbd har amai take inta sha su.

Umma tace " ke dake nake magana kinyi shiru"





_*Taku ce*_

_*💐Mummy's Friend💐*_

*NA TSANI MAZA*Where stories live. Discover now