91-95

445 25 1
                                    

💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫

*NA TSANI MAZA*

💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫

      
       *💫Na💫*

*💐Aysha Isa (Mummy's friend)💐*

_*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile's family*_

_*Ina gaida members din times writers. Allah ya bar zumunci.*_

_*Life is too short to start your day with broken pieces from yesterday. It will definitely destroy your good today & ruin your great tomorrow. Move forward with a fresh start and say Alhamdulillah ❤️.*_
   

_*بِسْــــــــــــــــمِ اللَّهِ الرَّحْمَ الرَّحِيْم.......*_

9⃣1⃣➡9⃣5⃣

RAYHANA ce kwance kan three 3 seater idonta na kallon ceiling da alamu tayi zurfi cikin tunani.

Hameeda ce bakin kofar falon sai kwad'a sallama take yi amma shiru bbu amsa, k'arasowa cikin falon tayi ta iske RAYHANA kwance, tafi Hameeda ta zub'a mata, Firgit ta mik'e daga kwance tana sosa gun da Hameeda ta doketa had'i da fad'in “auchh wlh hannunki da zafi”.

Tsaki Hameeda ta ja tace “ 'yar rainin sense ashe kina nan kwance  nake ta sallama baki amsa ba.”

“Sorry bestyna wlh banji bane shiyasa.”

“Ya zaki ji kuwa bacin kinyi nisa cikin tunani, wlh in har baki rage wannan tunanin ba zaki ja ma kanki ciwo, haka kawai mutum yayi ta tunani sai kace shi d'aya ne mai matsala. In aka tambayaki kuma kice bbu komai.”

“Hmmm bestyna In Shaa Allah zan daina wlh ban sani lkcn da hakan ke faruwa ba ne.”

“Ke kika sani, Mami na ciki?.”

“Eh muje na rakaki ku gaisa.”

D'akin Mami suka shiga Hameeda ta gaida ita sannan suka nufi d'akin RAYHANA. Kwanciya Hameeda tayi RAYHANA ta d'auko mata lemo daga fridge ta zuba mata a kofi “bismillah bestyna.”

Mik'ewa Hameeda tayi daga kwance sannan ta d'auki kofin lemo ta d'an sha sannan ta ajiye “ yauwa habibaty baki bani lbr yanda kuka yi da ur love.”

Ajiyar zuciya RAYHANA tayi ta kwashe kaf abinda ta faru ta gayyawa Hameeda tana fad'i hawaye na zuba daha idanuwan ta.

“Subhanallah ai shiyasa nace kivbari yaxo gida amma kika ce kin fi son ku had'u a waje tukun, Allah zai saka maki tawan kib'ar kuka haka pls.”

RAYHANA tace “bestyna ynx haka akwai wani unknown numba dake damuna shine kuma silan fad'awata tarkon wa'inan azzaluman domin a tunanina unknown numba da ke kirana duk mutan daya ne.‘’

“Subhanallah, kiyi trying true caller mana zaki gane ko waye.”

“Af na sha'afa wlh mantawa nayi bari nayi trying ynx.” Wayarta ta d'auko sai ta kunna data ta shiga apps din true caller ta saka numbar tana sakawa sai ga duk info. din caller din ya bayyana, zaro ido tayi tace “wat!RAYHAN SHEHU.”

Fisge wayar Hameeda tayi itama tana ganin tace “Wat!how comes.”

Kuka RAYHANA ta fashe dashi “RAYHAN ka tarwatsa min rayuwa, ynx wa xai auran a haka,na shiga uku.”

“Haba mana RAYHANA ki bar fad'in haka akwai wa'inda rayuwan su tafi taki muni kuma sun zamu mijin, aure balantama keda kaddata ta afka maki, kuma wlh na san RAYHAN baiyi hakan don tarwatsa rayuwarki ba asalima sonki ne ya sanya hakan ta faru.”

“So fa kika ce Hameeda, wani irin sone haka?”

“Hmmm RAYHANA kenan kowa da kalar tasa soyayyar, kuma ai ke kika masa gargad'i da ya tafita hanyarki shiyasa ya b'ullo ta wannan hanyar amma kiyi hkr In Shaa Allah komai ya kusan zuwa k'arshe.”

“Nagode tawan amma wlh sai naji nakara tsanar maza.”

“Subhanallah tawan ya kike son maida mu bayane kuma, don Allah ki tsoke wannan zance.”

Murmushi RAYHANA tayi “Allah ya bani ikon yin hakan.”

“Ameen tawan don wlh na k'agu na ganki a d'akinki, kodai da RAYHAN za'ayi ne ” Hameeda ta fad'i da sigar tsokana.

“Hameeda bana son irin wannan wasa don Allah amn't in d mood ehee.”

“Sorry na daina.”

Wannan kenan.

Pls manage dix wlh bana samun time ne.

*NA TSANI MAZA*Where stories live. Discover now