💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*NA TSANI MAZA*
💐💐💫💫💐💐💫💫💐💐💫💫
*💫Na💫**💐Aysha Isa (Mummy's friend)💐*
_*Dedicated to Alhaji Isa Ndalile's family*_
_*💃🏼💃🏼💃🏼Welcome back my mentor Pretty Zahrah, really miss you.*_
_*Gidan karamci, gidan hadin kai, gidan albarka, gidan…………, am short of word to describe you guys. Allah ya kareku daga sharrin shaidan, ku dole kuyi karko duk runtsi duk wuya anan tare. Exclusive Writers Forum gida daya tamkar da dubu. Ina yinku irin totally😘😘😘.*_
_*I dedicate page to you my mentor @ Pretty Zahrah.*_
_*Kuyi hakuri da typing errors hakan na faruwa sbd rashin editing da bana samu yi bear wit me pls🙏🏻🙏🏻.*_
_*بِسْــــــــــــــــمِ اللَّهِ الرَّحْمَ الرَّحِيْم.......*_
9⃣9⃣
Daidai wani katafefen gida motocin sukayi horn mai gadi ya bud'e masu gate suka shigo ciki, parking sukayi mutanan ciki suka fara fitowa, ko wannen su sai raraba ido yake suna kallo. Gidan ya ha
d'u iya had'uwa domin daga wajensa ma abin kallon ne. Gida ne maidaidaici wanda ya kunsa selfcontain guda biyu sai parlour babban guda daya, san dinning area, kitchen sai store. Gaskiya Abban RAYHANA yayi kokari sbd yayi mata furnitures nagani na fad'a. Duk wannan santin gidan da mutane ke yi RAYHANA na zaune bakin gabo tayi nisa cikin tunanin wai itace zata zauna k'ark'ashin wani, wanin wanda tafi tsana, ko ya zaman tasu xata kasance?, tana tsaka dq tunani Hameeda tayi taping d'inta “ wai tunanin mai kike ne bazaki tashi kiyi sallah ba, kinsan dai k'arfe takwas za'a tafi dinner dai.”Da sauri ta mik'e tace “ Subhanallah har an kira sallah?, wlh banji sanda aka kira ba.”
“ Ina kuwa zakiji bacin kinyi zurfi cikin tunani. Idan tunaninshi kike ai duka bai wuce wasu d'an hours ba zaku kasance tare abinku” ta k'arashe zancen da sigar tsokana.
“ Mtsw zakiji dashi” cewan RAYHANA sannan tayi shigewanta toilet. Wanka tayi sannan ta daura alwala. Tana fitowa gabatar da sallar magrib bata tashi ba har saida tayi isha d'ayani.
Wani had'ad'en peach colour gown Hameeda ta mik'a mata ta saka. Kayan yayi mugun karb'anta, zama tayi aka mata makeup wanda ya k'ara fito da kyawun fuskanta sannan aka mata d'auri da silver head. Takalmi silver colour ta saka ta d'auki purse shima silver colour ne. Mik'ewa tayi ta d")'auki wayarta. Tana tashi Hameeda, Maryam da Zee suka had'a baki wurin fad'in “ wow ”.
Zee tace “ wannan kyan haka kamar a sace a gudu.”
Maryam tace “ kedai bari. Nasan RAYHAN bazai ganeki ba inya ganki.‘’
Hameeda tace “ nidai kar a zauta min abokin miji a sashi aikata abin kunya ” ta fad'i cike da tsokana.
Fur RAYHANA ta wucewarta sbd tagan abin nasu bana k'arewa bane. Da gudu Zee da Maryam suka karasa gunta “ haba mana RAYHANA ba'a san amare da fushi ba.”
Hameeda tace “ haba mana bestyna daga wasa sai fushi.” Shafa cikinta tayi “ babynki yace kiyi hak'uri.”
Murmushi RAYHANA tayi amma bata ce komai ba.
Dariya Zee da Maryam suka yi suka ce “ su baby manya.”
Motar Zubair suka nufa Hameeda ta zauna a gaba. RAYHANA tasa kafa zata shiga motar kenan Zubair yace “ ai ba motana zaki shiga ba” nuni yayi mata wata mota tinted yace “ wance zaki shiga.”
YOU ARE READING
*NA TSANI MAZA*
RandomLabari ne akan wata budurwa da ke ikiranin ta tsani maza, wannan dalilin ne yasa bata kula ko wani saurayin. Ko meye dalilinta na tsanar maza?. Ku biyoni cikin wannan labarin don sanin wannan dalilin.